page 65 to 68

94 5 0
                                    

Banyi zato ba
Mrsjmoon

*65~68*

Misalin 8:10am mamie ta farka, Dada ce ta fara lura da motsawan da fatar idanumta keyi, ta matsa kusa da ita tana cewa "Takwarata kin tashi ne? Sannu."

Idanunta da suka kayi mata nauyi ta bud'e ahankali tasoma bin d'akin da kallo.

Dada ta kama hannunta "sannu takwarana, Allah yabaki lafiya."

Ta gyada kai hawaye ya zubo tagefen idanu.

Sannu suke jera mata. d'aya bayan d'aya.

Hakeem yashigo tare da Doctor Bilyamin. Ya dubata yayi mata sannu ta d'aga kai alamar amsawa sabida ji tayi bakinta yayi mata nauyi ga kuma wani zafi da takeji akasan maranta kamar an barbad'a mata barkonu.

Hannunta takai wurin ta shafa taji bandage kato tayi saurin janye hannun, sai lokacin ta turo ashe fa operation akayi mata, ta lumshe idanunta tana jinjinama iyaye. 'Lallai wanda baiji tausayin uwarsa tare da yimata  biyayya ba yayi asara, bashi basamun babban rabo duniya da lahira.'

Ahankali ta furta "Allah ya baki aljanna mad'aukakiya Ummana, kiyafemin  in na saba miki."

"Amin, bakimin komi ba mamie, Allah yaqara miki lafiya, sannu kinji."

  Asannu ta sauke dubanta kan Umman wacce ke tsaye gefenta, murmushi tayi tace "Nagode Ummanmu."

Mummy ta tallabota ta kara mata fillo abaya ta jingina,, hawayen da yaki tsayawa a fuskanta mummy tasa hannunta tana sharewa, tana cewa "Ayya yarinyata kibar kukan haka, zaki sami lafiya."

Gyad'a kai tayi tace "Abani ruwa kishi nakeji."

Hakeem me ya dafata yace "A'a mamiena kibari ruwan da ake samiki ya kare tukunna."

Kuka tasa mara sauti tana cewa "Kishi nakeji sosai, mak'oshi kamar zai kama da wuta."

Batare da sun shirya ba mutanen dakin dariya ta kufce musu jin zancenta na k'arshen.

Dakyar aka lallafab'a ta hakura barci yakuma d'aukanta.

Da yammmaci Dr. Bahijja ta shigo domin duba jikin mamie, lokacin tana jingine ajikin gadon  Hameeda tana bata tea, cikin jin dad'i Dr.Bahijja ta isa ta dafa kafad'ar tace "Sannu Jidda, ya kikejin jikin naki yanzu?"

Kwabe fuska tayi ta amsa "Har yanzu zafi wurin kemin kamar an watsami garin barkonu."

  "Ayya yi hak'uri zai bari, kinsan ciwo ne babba, sai kinyi hakuri nan da 'yan kwanaki zai koma kamar baki tabajin zafinba."

"Allah yasa haka Doctor."

"Amin."

Yau kana biyu da yiwa mamie cs tasami sauqi sosai baki ya bud'e har tana rama tsiyan da Sady takemata na wai ta ishe mutane da shagwaba.

Shigowar Doctor Bilyamin tare da Doctor Bahijja d'auke da babies,  bayansu Hakeem ne tare da mummy, yasa mamie had'e rai ta tura baki tana hararan babies d'in ta gefen ido.

Murmushi Hakeem yayi ya matso kusa da ita yace "Gyara sosai zasu sha nono ne."

Motsa labbanta tayi tace "Anqi."

Bai kula taba yace Doctor matso ki koya mata yarda akeyi don jiya ina kallo yatsa tayi ta tura musu taki bari su kama da kyau yarda zasu koshi."

Harara ta dalla mishi ta dubi mummy wace keyi musu dariya tace "Mummy kirabani da yaron Umma, Allah yafiye sharri."

"Hakeem narabaka da sama yarinyata idanu tam." Momy ta furta cikin murmushi.

Dariyar da yake kunshewa ne ta kufce.

BANYI ZATO BAOnde histórias criam vida. Descubra agora