Page 3.

842 41 0
                                    

*3 to 4*

Dada ta sauko ta iso wurin mamie ta sa hannu ta tafa kafad'arta, da hanzari mamie ta ture hannun nata tare da matsawa gefe ta saki kuka.
   Dada ta daka mata wata uwar tsawa wanda sai da mamie ta gigice bata san sanda ta fad'a jikin Dadan ba ta k'ank'ameta tana cigaba da kuka.

  Cikin taushi Dada ta soma magana tare da shafa kanta "Takwarata kiyi hak'uri don Allah, nasan kinji wani abun da su bara'atu da yunus suke fad'a amma nasan baki fahinci komiba, to inaso ki nutsu kiji dalilin ganina tare dasu a daren yau amma  tabbas nibansan komi ba akai sai yau kuma cikin daren nan.

Shiru tayi tabar kuka ta d'ago ta zubawa dada idanu tana alamar tana saurarenta, dada jiki ba kwari tasoma koro mata bayinin...

"Takwarata wallahi bilahil azim ban san komiba akan laluran na'ima wato ummanki,  yau cikin daren nan ina palour na idar da sallar nafila ina jan tasbaha naji ana kwankwa samin qofa ahankali ana kiran su nana namatsa jikin k'ofan sai naji muryan Yunus ne yake kirana don haka sai na bud'e, shi da mmnsa suka shigo, naji tsoron ganinsu don nayi zaton Baffansa ne ba lafiya sai suka tabbatarmin naya cikin k'oshin lafiya sunzo in tai makesu kamar yadda nataba taimakonsu wurin binne layan da sanadinsa Na'ima ta hauka ce, iya gigita ta rud'ewa nayi jin zancensu domin hakik'anin gaske sanda suka kawomin layar da na binne cemin sukayi sun amso maganin natsari ne akan dukiyan Usaman da Umaru wato Abbanki da Baffanku shiyasa na binne batare da wani dogon bincike ba, ashe matar kirki akayi wa surkulle."

   Tayi shiru tana kallon mamie wanda ta zuba tagumi tana sauraren ta, domin ko kadan bataji mamakiba don ta dad'e tana zargin mama cikin lamarin ummanta shi yasa ta kance ma hakeem da Abba anemi na gargajiya zaifi amma sunk'i bama zancen nata muhinmanci.

     Dada tacigaba "Ganin na tsorata shine suka cemin in kwantar da hankalina wannan dazan binne ta warwarewan matsalar ce, jin haka sai na amsa amma ban yarda dasu ba, sosai naji tsoron su alokacin nakasa musa musu.

Haka suka fice fuskokinsu cike da nushad'i, sai da suka jima da fita sai naji wani kuzari yazomin don haka sai nabi bayansu bakina d'auke da ayatul kursiyyu...

       ahankali nake tafiya bako talmi har na cinmasu a bayan d'akin Abdul hakeem sun tsaya suna magana wanda banji misuke tattaunawa akaiba, zuwa can Yunus ya sunkuya ya haqa rami yabinne wani abu sannan suka wuce ina biye dasu abaya har suka isa shashin bara'atu  sai suka tsaya aqofar barandar shiga shashin na labe don jin mizasu fad'a.
bak'aramin mamaki da dimaucewa nayiba sanda naji Yunusa yace mama wancen tsohuwar banzan inaga asirin fa bai kamata ba dubi da yarda take kallonmu a d'age kamar bata yarda damu ba, uwarsa ta amshe magajina kenan ai abinda baka saniba malam yace tana yawan azkar don haka bakomi za amata yakamata da hanzari ba, shinema yabani layan can in bata ta binne da hannunta to inta aikata hakan lallai komi za muyi agidan bazata tsawatarba balle ta ga bamu kyauta ba.
 Wani tsalle yayi yanawa uwartasa kirari na shaid'ana.

  jin hakan danayi atake jikina yasoma rawa najuya zan koma naji shu'umar tana cewa ai haukan da nasa Na'imah ciki so nayi tayi ta bugun cikin jijinta har sai ya zube amma kafaffen cikin yak'i ko gezau to don haka yanzu na sanza shawara inaga asibin zanje nasami wani doctor cikin sirri yayi mata alluran guba kawai ta bar duniya baki daya kawai donmin wallahi bak'aramin haushi take bani ba tun kafin in haifeku.
  Da wannan sharawan yayi kam mama, kinga ta mutu shi kuma Hakeem yabi duniya ita kuma shegiyar can fitsararriya abarta in riqa hutawa da ita inda zansa Baffa ya auramin ita kawai muyi ta azaftar da ita ak'arshe intakamu da ciwon yoyon fitsari sai in saketa mu korata duniya itama, kinga an huta.
  Wani dariya tasaki tana cewa gaskiya magajina kanka naja Allah ya maka albarka. Amin mamana.

Sai duk suka kwashe da dariya kamar wasu mahaukata, Yunus yace mama inje d'akin mahaukaciyan can inyima shegiyar yarinyan can nata fata fata kinga innazo da zancen zan aureta baza amusaba don ya ayi tunanin zan rufa mata asirine. Aha yayi magajina, se da dafe.

BANYI ZATO BAWhere stories live. Discover now