Banyi zato ba.
Mrsjmoon
*13 to 14*
Abdul Hakeem yana da shekaru hud'u da rabi aka haifi Yunus.
Daganan suka zama su biyu yaran gidan.
Gata na duniya an nuna musu sosai sannan an wadatasu da ilimin addini tare da na zamani, amma abin haushi Yunus tun yana k'arami baya da basira ga fitina da rashin kunya wanda uwarsa ita ta jagoranci duk wani tabara daya keyi.
Don haka kowa na gidan yake nuna so da k'aunarsa ga Abdul Hakeem sabida da nutsuwarsa ga tarin basira da hak'uri kamar Ummansa.Bayan sheraru kusan goma sannan Hajiya Na'ima ta haifi hauwa'u wacce suke ce mata Mamie, alokacin itama Hajiya Bara'atu ta haifi Imranat wanda kwanaki uku ke tsakainsu da mamie. shekara na zagayowa ta kuma haihuwar Fatima don kwarne tayi tsakaninsu, shiyasa suka taso su uku kansu d'aya.
Daganan ba a k'ara haihuwaba sai bayan tswon wani lokaci dan su Mamie sun zama 'yan mata har sun shiga jami'a sai kwatsam hajiya Na'ima ta soma laulayi atake aka gano cike take d'auke dashi wanda yabawa al'ummar gidan matuqar mamaki sabida ba ayi zaton samun wani haihuwarba dubi da ganin tsawon shekarunda aka kwashe ba wacce kak'ara haihuwa cikinsu amma cikin ikon Allah sai gashi wani k'aruwan ya kuma samuwa.
Wannan samun cikin da Na'ima tayi shine ya k'untatawa Bara'atu rayuwa har yajefata bin bokaye don ganin Na'ima bata haihuba kuma tak'are rayuwarta a titi cikin hauka. Ka wai dan tsabar hassada.
Allah gafurun rahimun sai gashi hak'anta bai cinma ruwaba, Na'ima ta warke kuma ta haihu lafiya.
Hajiya Na'ima agidan marayu ta tashi.
Uwar goyonta kuma shugaban gidan marayu Hajiya Jidda itace tazamemata sanyin idaniyarta domin tunsanda aka kawota cewar an tsinceta awani had'arin mota da ya afku kuma mutanen cikin) motan duk sun rasu sai ita kad'ai 'yar kimanin watanni bakwai da haihuwa ta rayu kuma bataji ciwon komiba, sai taji tausayin jaririyar tare da k'aunarta ya kamata.
Sakamakon haka ita tayi ta kula da ita har ta soma girma ta iya tafiya tare da magana sai tasoma barinta cikin sa'anninta yaran gidan marayu.Da ta isa shiga makaranta ta sanyata awani makaranta kud'i mai kyau kuma ana hadda da islamiyya cikinta, don haka takasance mai tarin ilimi ta fita daban cikin tsaranta.
Har tagama secondary alokacin ta sami haddar AL-QUR'ANI mai girma tare da sauran littafai.
Tasoma karatun jami'a inda anan ta had'u da Aminiyarta Fiddausi.
Ita d'in d'iyan wani shahararren hamshak'in d'an kasuwa ne wanda baicika zama a k'asarshi ta haihu ba sosai sabida hada hadar kasuwancinsa.Aminci tare da k'auna mara algus suke nunawa junarsu har suka kammala karatunsu, a inda sukayi aure kusan a tare amma Fiddausi tariga Na'ima aure da watanni biyu.
Abu d'aya ke damun gidn auren Na'ima shine matsalar Bara'atu da d'anta Yunus wanda yake neman illata yarinyar kirki Mamie kawai don tsaban son zuciya da biyewa kururuwan iblis, yabari shaid'an yagama yimasa futsari a zuciya baya tuna mutuwarsa tare da ubangijin da ya halicceshi Allah S.W.A balle yayi koyi da bin sunnar ma'aikin Allah SAW. Dan zamowa d'a na kwarai irin Hakeem, sai dai kullum ciki neman magana yake.
Cigaban labari....
Dasauri ta fito daga part d'insu tana duba agogo wanda ke d'aure atsintsiyar hannunta na hagu, wata k'aramar mota arsh colour mai kyau sai kyalli takeyi ta bud'e ta zauna tare da yimata key tayi jim kad'an sannan jata cikin natsuwa tana duban agogo ganin duk saurinta sai ta rasa first lacture, tsaki taja ta furta "Dik umma ce ta jamin ai, datace dole saina had'a breakfast to gashinan na makara ai."
Tak'atasa maganar kamar zatasa kuka.
Tana fitowa gate Yunus ya tari gabanta ta taka burki da sauri tana k'are masa kallo, ya matso kusa da ita tare da zura hannunsa cikin aljuhunsa tanaganin haka cikin hanzari ta d'aga glasses d'in sama ta rufesu ruf taja motarta da gudu tayi gaba yabiyota da sauri ta dawo da baya da uban gudu yayi saurin kaucewa amma ina yakara domin sai da ta tureshi yayi mugun fad'i haryana mulmulawa kansa ya bugu da dutse. Ta fito ta tsaya gabansa ya d'ago kansa awahale yana kallonta har goshinsa ya fashe yana zubda jini.
YOU ARE READING
BANYI ZATO BA
General FictionBayan gamayin dinner d'insu suka balle da hira, sosai suka tattauna da juna a inda Hakeem yayi ta bashi baki akan yazamo mai yarda da qaddara abisa laluran data sameshi. Yunus cike da annashuwa yayi ta godiya game da kulawansa akan laluranshi ganin...