1

6.6K 357 22
                                    

    'kayataccen Palo ne wanda ya amsa sunansa wanda kallo d'aya zakai masa kasan ma'mallakansa sunci suntada kai d dukiya,, wata hakimar, mata ce zaune a d'aya daga cikin royal chairs d'in da suka sake'kawata palon.

Kyakyawar mace ce wacce bazata gaza shekaru 40 ba. danma tanada jikin 'kiba da bazaka ta'ba cewa takai shekarun ba saboda yanayin kyan fuskarta da kyawon Jikinta da Kyakyawar skin d'inta da sai faman glowing yakeyi.. kayan dayake jikinta kuwa... wani tsadadden material ne wanda yagaji da haduwa. tasha earrings da bangles na tsadadden zinari,, gabanta wani had'in chicken pepper soup ne da yaji kayan had'i sai mug d'in dake d'auke da zobonta,, cin pepper soup d'inta takeyi hankali kwance yayinda fuskarta Sam bata nuna kwanciyar hankalin nata ba dan fuskarta cike take da tsantsar damuwa wacce a kullum take tashi d ita haka kuma take kwana da ita,, tasani wannan ya na daga cikin jarabawar ta, saidai,, a duk lokacin d ta tuna takanji wani bakin ciki mara misaltuwa,

Yaya zatayi? Allah yariga da ya jarabce ta da Baby a cikin yayanta wanda daga ita har mijinta sunayi mata wani irin so wanda baki bazai iya furtawa ba,, saidai basu isa su Hana Allah yayi ikonsa a akan Yar tasu ba duk da irin son dasuke mata kuwa!

Tsame hannunta tayi.. zuciyar ta cike da wani 'bacin ran... tana sake yin addu'a wa yarta mace kwaya d'aya. dinning tanufa ranta a jagule, ta wanke hannunta a gun sink, towel ta d'auka ta goge hannayenta d bakinta. Komawa tayi ta zauna bayan takai bowl mug d'in kitchen,, tagumi ta rafka,, abubuwa d yawa na sake Kai kawo a zuciyarta.

Hajiya..... hajiya....uwani mai aikin gidan ce ke kwala mata kira... muryarta na tsananin rawa! da sauri tamike cike da fargaba, dan ko ba a fad'a mata ba tasan abunda ake kiranta domin shi ya shafi baby"

Uwani lfy...? ta tambayi uwani, cike da fargabar mai zata fad'a mata,
haki take tama kasa magana saboda tsorata... da tayi,, sake shiga tashin hankali hajiya tayi ganin halin da uwani take ciki,, kawai sai tabi ta hanyar da uwani tafito yayinda 'kirjinta ke wani irin do Kawa,, da sauri uwani ta bita dan ganin halinda uwar d'akin tata tashiga.... Ita kanta tana tsananin tausayawa uwar d'akinta ta..

Tura d'akin Yar tata tayi cike da tsantsar fargaba, aikuwa da mummunan tashin hankali tayi arba,, dan yarinyar sai faman buga kanta take a jikin gini. da matukar tashin hankali ta isa gareta.... Rungumeta tayi, yayinda itakuwa tashiga fiffiz' gewa da tsananin 'karfin da baza kace yar shekara goma bace....

Cikin tsanin kuka mahaifiyar ta tashiga gurgiza ta tana fad'in... Baby... Baby ki nutsu baby...! cikin tashin hankali d rudewa had'i da tsantsar tausayin yar ta,,
   Ganin yadda gushin nata yafashe yake jini ta sake shiga tashin hankali..... take ta tuno da mijinta abun kaunar ta da yake yawan cewa lubabatu"ki dinga nutsuwa a duk lokacin da kika samu kanki cikin tashin hnkali kiyi ko'karin kawo Allah kafun komai a zuciyarki... Lallai shi maiji ne kuma mai gani,, Inna"lillahi wa'inna ilaihim"raji'un.... Shine abunda tashiga maimaita wa, a hankali tana sake 'kan'kame yarta had'i da yimata addu'a jikin baby ne yasoma sanyi ta zube jikin mahaifiyar ta... tana fitar da wani irin numfarfashi.

Da sauri uwani"taje d'auko first aid box d'inta. towel da ruwan d'umi takawo jikin hajiya lubabatu a sanyaye tashiga dreasing raunin,, saida tagama ta kaita bathroom tayi mata wanka ta fito d ita ta shirya ta tsab!

tabata drugs d'inta... a take tasoma bacci a jikin mahaifiyar ta tana sauke numfarfashi dake nuni d wahalar da tayi tayi,,, a sanyaye ta d'auke ta kwantar da ita tayi kan kyakyawan bed d'inta gashin kanta ta tattare ta mayar mata shi baya kasancewar ya rufe mata ido addu'a tashiga yi mata,, kafun ta tashi dan tayi sallah dan tasan da wuya ta tashi yanzun dan maganin yanada 'karfi, so zata iya Kaiwa kaman 3 hours tana baccin.

UMAIMAH! Where stories live. Discover now