2

2.5K 168 7
                                    

  'karfe 4na yamma suka iso gidan Alhaji Tahir yuguda"dake unguwar wise2 Abuja Nigeria. wangale musu gate d'in gidan akayi,, parking Bala yayi a parking lot,, bud'ewa Hajiya Rahamu,, kofa yayi jikinsa na wani irin rawa dan sosai yake tsoronta dan duk wanda ya kwana yatashi a gidan to fa yasan hajiya Rahamu gurin shinfid'a mulki,, isa da gadara wanda..... Babu wanda ya isa yake tare umarnin ta Koda kuwa mai gidan ne,, shi yasa Kowwa yake kaffa kaffa da ita.... Idan bata nan kuwa tamkar anyi wa gidan bushara duk ma'aikatan gidan sun samu freedom kenan,, da Zarar ta dawo kuwa... tofa shikenan sunkoma zamn makoki.

        Cike da isa da gadara,, tafito daga cikin motar,, tana cika tana batsewa,, wata matashiyar budurwa ce tafito itama sai wani fizgar kai takeyi,, kallon Bala tayi a wula'kance tace... Ka kwaso mana kayan mu.. Amsawa yyi da to jiki na bari,, su kuwa gaba sukayi zuwa part d'in Rahamu,,

            *****
Hajiya lubabatu nasamun labarin isowarsu tasaka uwani ta Deba abincin su takai musu,, cike da farga ba tashiga palon samu tayi babu kowa dan haka ta sauke ajiyar zuciya Kai kayan tayi kan dining ta ajiye ta fita,, tana ganin kanta a waje lami lafiya ta sauke ajiyar zuciya had'i da fad'in Alhmdllh a sarari!

              Hajiya lubabatu bayan tayi sallar la'asar ta tabbatar da, yanzun sun d'an huta tasaka hijab d'inta tanufi part d'inta dan fita hakkinta Koda dai Annabi (SAW) cewa yayi mai tafiya ya gaida na zaune,, ita ta amince taje Tai mata sannu dan tasan idan ta Rahamu ne Kowwa yayi harkar gabansa ita kuwa baza ta iya Zaman gaba ba,, shi yasa duk inda suka had'u takanyi mata magana Koda bazata amsa ba,,, takance rayuwar duka nawa ce da kishi zaisa kayiwa kanka dakon shiga wuta?

     Sallama tayi a palon ba a amsa ba dan haka tashiga da niyyar ta sake rafka wata idanma suna ciki ne su jiyo ta,,. Saidai ga mamakinta.... Salma tagani Yar Hajiya Rahamun.. dubanta tayi taga sai faman dannar wayarta take ko a jikinta,, danne damuwarta tayi kafun tace.... Salma... Bakiji ina sallama bane? cikin gwatsine da sakarci tace.... Naji mana... Shine kika kasa amsawa? Kinsan ladar sallama da amsata kuwa?

          Mtssss.... Ke fa hajiyar nan kincika takura daga zuwa na zaki wani fara damuna da surutu kuma ma gani nayi ai dai d'akin mahaifiya ta ne.... ko ban amsa ba babu ruwanki..... Saki baki ummi tayi tana kallonta,, a ranta tace tirkashi... A Zahiri kuwa cewa tayi Allah ya kyauta... Ina mommyn ki?

         bata amsa mata ba cikin sa'a kuma sai ga hajiya Rahamun nan tafito,, tana ganin ummi ta wani tabe baki irin kinji dashi d'inan.
                        Hajiya Rahamu sannu da zuwa..... Ummi tafad'a cike da karfin Hali,, a da'kile ta amsa da lafiya Kuna lfy?

     fuska a sake ummi ta amsa da lafiya lau Alhmdllh.

              daga haka gurin tad'auka shiru,, dan haka tasaka Kai zata fita tana cewa Allah ya hutar da gajiya,, ko amsawa basuyi ba suka vita da mugun kallo musamman ma mommy,, dan ji tayi tamkar ta janyo lubabatu ta shake ta har lahira saidai babu yadda ta iya,, dan boka yace mata akwai lokaci kuma dama ita bataso tai mata kisan wuri tafison sai ta d'an ji a jikinta kafun kuma daga dukkanin alamu bata cikin walwalarta dama abunda take bukata kenan..... ta ganta a damuwa wahala ciwon rai kuma ga alamun nasara..... Wani irin shu "umin murmushi tasaki. had'i da jin ita d'in wata ce.

********
Alhaji Tahir yuguda! Shine asalin cikakken sunansa haifaffen garin yuguda ne kuma bafulatani,, inda yawon biggali yakai iyayensa wani kauye kusa da Abuja ana kiran kauyen ruggar mai danmma. Anan ya rayu da iyayensa kasancewar shine kawai d'ansu,, wata rana masu satar shanu suka shigo rugar inda duk wanda yafito ko zai kawo musu gardama saidai su kashe shi cikin rashin sa a mahaifinsa Umar yuguda yayi ja yayya dasu take suka kashe shi babu imani ko tausayi.

                  Da gari ya waye gari tad'auka koke koke,, tsabar bakin ciki da yai wa uwarsa Hari katutu yasa take ta yanke jiki ta fad'i,, itama anan tace ga garinku.

UMAIMAH! Where stories live. Discover now