34

1.5K 123 32
                                    


Gaisuwa da fatan alkhairee 🙏Aunty jamila yakasa😘Fateema Radda💋Haleelos💕Maikokona 😍mum Munawwara 💞maman Yara 😍mum Afra💖Mamn Sulaiman 💝mum zaheen💕baby bint oriflame 💞binta Umar 😍ta sidi🙏kankanaty Mrs yusuf mamn sajjad ta Annabi ummu haidar, Summy wakeeli 🙌😘gaskiya Kuna da yawa d sauran wanda ba fad'i ba ina muku ftn alkhairee Allah y raya zuri'a ysa albarka 🙌💕💋

ASALIN ALHAJI FAROUQ... Mutumin kano ne a karamar hukumar gwarzo mahaifin sa Alhaji Zubairu dalha" d'an kasuwa ne wanda Allah yayi masa nasibi a harkar kasuwan cin sa.

Yana da mata d'aya sai d'an su kwara d'aya wanda saida suka shekara goma kafun suka samu haihuwar sa, Alhaji Zubairu yana da yan uwa na dangi saidai yar uwar sa da suka fito ciki d'aya kwaya d'aya ce ita ma uban ta daban bayan mahaifiyar sa ta haifi suwaiba" ta rabu da mahaifin ta shine ta auri mahaifin zubairu,

      Iyayen su kuma du sun rasu, saidai yana matu'kar kaunar Yar uwarsa suwaiba kodan ita kad'ai ce dashi, a lokacin tayi aure itama a cikin garin kano Shima ya Gina gida a garin kano ya tare da matar sa.

Bayan shekaru goma Allah ya bashi haihuwar farouq, sosai yake nuna wa d'an sa gata dan ko makaranta ta yayan masu kud'i yasa shi, Allah yayi Alhaji zubairu, mutum mai tausayi da taimako, wannan yasa ya kasance mutum mai yawan ziyartar gidan marayu gajiyayyu da kuma asibitoci makabarta da gidan kaso.

A duk lokacin da yakai ziyara a irin guraren yana matu'kar jin imanin sa yana sake karfafa, haka kuma duk lokacin da yaje yakan bayar da taimakon kayan abinci kudade da sauran abubuwan bukata, wani lokacin ma ko baije ba idan suna neman taimako sukan same shi da zancen baya ku tsayawa zai bayar da abunda ake nema wannan yasa Yawanci gidan marayu da kungiyoyi na ma bu'katar suka San shi sosai.

Wannan yana daga cikin sirrin habbakar kasuwan cin sa.

Tun farouq yana kankani yake zuwa dashi duk ziyarar da zai Kai a d'aya daga guraren.

Wani lokacin idan yaga abun tausayi, sai ya dinga hawaye yana Godewa ubangiji, a lokacin farouq yakan ce Abba" an Duke ka ne?  Alhaji zubairu baya bashi amsa saidai ya shafi kansa.

Farooq yana shekarar karshe a secondary school. Wata rana mahaifin sa yace ya shirya dan suje gidan marayu kamar yadda suka saba a duk ranar jumma'a.

Hakan kuwa akayi sun shirya suka tafi kafun sallar jumma'a, dan hakan sukan yi ko idan sun gama daga can su tafi masallacin ko kuma bayan sunyi sallah sai su nufa can.

Yau dai kafun sallah suka tafi.

Suna office d'in shugaban gidan marayun, inda Alhaji zubair yake jin korafin abubuwan da suke bu'kata.

Sai ga d'aya daga cikin masu hidima da gidan marayun ya kwankwasa kofa had'i da shigowa, d'auke da kwali wanda kafun a fad'a maka abunda yake ciki zaka fahimta da kanka.

Saboda kukan jinjirin dake fitowa daga kwalin.

gaisawa sukayi da alhajin had'i da maida duban sa ga shugaban gidan.

"barka dai yallabai.

Barka malam Audu,

Yallabai kamar yadda kake ji wannan jinjira ce aka samu a gunwar da nake shine na d'auko ta zuwa nan gidan.

Ya fad'a yana mai sake duban kwalin.

Ajiyar zuciya shugaban ya sauke yace, mallam Audu, baka sanar da hukuma ba kuma ba kuyi bincike ba? ko a cikin unguwar ce wata tayi aika aikar?

Yallabai" kaima kasan yana da wahala a gano wannan al'amari.

Hmmmmm shikenan miko mun shugaban ya fad'a yana Mika hannu.

UMAIMAH! Where stories live. Discover now