14

1.5K 117 20
                                    

Abba"kamar fa ta farka, hajiya Rukayya ta fad'a tana matsawa kusa da UMAIMAH"wacce dama tuni take a farke, Masha'Allah shine abunda Abba ya fad'a, tallafo da kanta Hajiya Rukayya, tayi cikin tausayawa tashiga shafa kanta a hankali baby ta bud'e idonta kallon su tashiga yi kamar mai nazarin wani abun, a sanyaye Alhaji farouq yashiga fad'in sannu yarinya, koma dubansa tayi.
Kallon hajiya Rukayya"yayi yace... Shiga da ita ciki ta d'an samu nutsuwa, amsa masa tayi, kama hannun baby tayi zuwa cikin bedroom d'inta, kwantar da ita tayi kan gadon ta,

Fitowa tayi gun mai gidan nata, tace... Abba! a ina kasamu wannan yarinyar wai? Saida yasauke numfashi kafun yace, kamar dai yadda na fad'a miki ne a 'kofar gate nagan ta. muyi addu'a dai Allah yasa tadawo nutsuwar ta, daga baya sai muji komai daga bakinta. Allah ya kyauta amin ya amsa mata yana ficewa daga parlour.
itama kitchen tanufa a ranta tana addu'ar Allah yasa yarinyar tadawo nutsuwar ta.

******
Ummi"ce a gefen gadon da aka kwantar da Zaid" cikin muryar ta da ta disashe saboda kuka ta tace sannu Zaid" Allah yabaka lafiya.

baice mata komai ba Sai ido da yazuba mata, yayinda a zuciyarsa tsantsar damuwa ce fal a ciki ga tarin tunanin baby, ga girman zunubin da ya aikata wanda yake ji shi kansa bazai yafewa kansa ba dan hakan nan yakejin baiyi wa son da yake wa baby adalci ba, yabata gobensa, yabata goben baby, a bangare d'aya ga mutane masu daraja da tsantsar hallaci a gareshi, wanda bai duba duk girman alkhaireen su a gareshi ba, har ya iya keta alfarmar Yar su, shi kuwa ina zai Kai wannan abun kunyar, runtse idanuwansa yayi yayinda zuciyar sa taci gaba da wani irin suya...take kuma 'kwa'kwalwar sa tashiga bashi labarin batan UMAIMAH wanda shine sanadin sunan sa,

     Wani irin zabura yayi daga kan gadon, ya Mike daidai shigowar dad, ummi ma tuni ta mike.

Lafiya Zaid!?

Dad"yarinya ta dad, ina take....a wani hali take? Zanje nemanta dad.

Wani irin kuka ummi"ta fashe dashi had'i da yin waje,  dad kama Zaid yayi, ya zaunar dashi, haba zaidu ka nutsu mana kadawo nutsuwar ka baka ganin Bakada lafiya ne?

baka ga halin da UMMIN ku take ciki ba Uhmmm? Kuma ma insha'Allah Za a ga baby, ka kwantar da hankalin ka.

Kuka Zaid yafashe dashi.. Dad ni..dai.. zan nemota a duk inda take a fad'in duniya dad nayi alkawarin nemota dad.

Rungume shi dad yayi, take yasake kanka me shi yana koma sakin wani irin kuka mai tattare da tsantsar damuwa,

      Ummi"itama gu tasamu a waje taita rera kuka mai tsuma rai, tana mai yin addu'a Allah ya bayyana mata yarta Yakuma baiwa Zaid lafiya.

Dad haka yashiga rarrashin Zaid" da 'kyar aka samu ya d'an kwantar da hankalinsa, kwanan sa hud'u a asibiti, ya matsa kan a sallame shi.

Duk kwanakin da yayi hajiya Rahamu' bata zo ba bata aiko ba,

***
Salma tunda saura yinta yatafi da ita matatar iskanci bai barta ta dawo ba kullum cikin d'in kira mata kayan maye yake wanda a karkashin ranta tana matu'kar son tadawo dan ta aiwatar da mugun nufinta kan Zaid"dan tasan yanzun wancan yayi exper, dole sai tayi sabon zubu.

Dan haka ma tashiga sake neman wata mafitar ta yadda zata kama Zaid a hannunta yadda idan yashigo babu shi babu kubucewa.




Zaid"ka kwantar da hankalin ka dan Allah kadaina zancen fita neman baby da kanka, tunda jami"an tsaro na bakin ko'karin su dan haka kayi ha'kuri mu zubawa sarautar Allah ido. Muyi ta addu'a insha'Allah zata bayyana a garemu a duk inda take,, lumshe idanuwa Zaid"yayi.

UMAIMAH! Where stories live. Discover now