21

1.2K 106 12
                                    

Shiri akeyi babu kama hannun yaro,, salma"sai salailai ake tayi,
Rahamu". Wannan duk bai dame ta ba idan da abunda ya dameta to cikar burin ta ne.

Zeema" ce ta dubi salma da sai faman sakin tsaki take hannun ta ri'ke da waya, tace saly yahdai?
Wani tsakin salma tasaki kafun tace wlh zeema"bangis ne yabi ya ishe ni, wai Lallai yau inzo mu had'u,!  Kuma nasan Sarai idan na kuskure na je to wlh bazai barni in dawo kan lokaci ba,  inda ma naji dad'i d'aya ne baisan cewa aure nake shirin yi ba da nasan sai ya mun rashin mutunci.

   Hmmmm" Zeema ta ja kafun tace ni fa kina ban mamaki saly, yanda kike tsoron wannan bangis d'in, yanda yake ta'kamar gidan su akwai arziki ai kema gidan ku akwai shi, idan kuma sonsa kike to kawai ki fad'a masa yafito ayi dashi a fasa da wanna......

Zeema!... Ki rufan asiri dan Allah Kar ma mommy taji wannan zancen, kinsan irin wahalar da aka sha kafun Zaid ya amince zai aure ni?

Anzo gurin! Zeema ta fad'a a ranta, saidai bata nuna komai a fuskarta ba, tace wai bangane mai kike nufi... hmmm Zeema abar maganar nan kawai amma idan na fad'a miki ai mommy sai ta kusa kashe ni yadda take da burin cikar burin ta!..... Salma.....'kundun ubanki.... Nace kaniyar ki.... Shasha wacce batasan ciwon kanta ba.!

Rahamu" ce mai wannan zancen bayan taji zancen da su Salman su keyi. jikin salma ne ya d'auka rawa dan tasan mommyn na iya cewa anfada auren...da sauri ta shiga baiwa Rahamu" ha'kuri,,

Ko kallon ta Rahamu"batayi ba, ta dubi zeema wacce ke duban su cike da tuhuma... tace fita tana nuna mata hanya, jakar ta ta d'auka ta fita, a ranta tana kitsa yadda zata samu jin dukkan abunda suke boye wa tasan salma wawuya ce, ta bugawa a jarida ba zata sha wahala gun jin sirrin ba, kuma ma ga hanya mai sau'ki.... ta fad'a wa kanta kawai kayan maye zata loda mata ta kwaye mata komai suke rufewa ita da azababbiyar uwar ta,
               Dan ta dade da tuhumar ba Kai tsaye Zaid zai auri salma ba saboda yadda salma tasha bata labarin yadda take sonsa yake wula'kanta ta.   hakannan taji tanason taimakon zaid d'in ko dan hassadar da takeyi wa salma, bata shirya salma tabar bariki yanzun ba so take ko barin ne to Sai dai su bari tare. da sa'ke sa'ke tabar gidan.

            *****
Salma ashe ke wawiya ce? wa ya fad'a miki ana amin ta a bariki? Waton da banzo kan lokaci ba da yanzun sirrin mu yakoma hannun wata, wacce kuka had'u wurin yawon club... Ko kin d'auka bansan iskancin da kuke yi ke da azeemar bane?

Wawuya kawai,, to wlh bari kiji in fad'a miki duk ranar da kika sake kika fad'awa wani wannan sirrin ina mai tabbatar miki da babu ke babu zaidun har abada kuma mutuwa zakiyi dan ubanki!
   
        Mommy ni dai dan Allah kiyi ha'kuri, wlh ni dama ba fad'a mata zanyi ba, kawai dama bangis ne yadameni wai sai nazo mun had'u shine nake fad'a mata shine wai in auri bangis d'in, shine fa nace ta daina wannan zancen batasan yadda na sami zaid d'in bane,,... shine fa muke maganar,

Tsaki Rahamu tayi, kaji irin sakarcin naki ba, Sam bakida wayau, ni wani lokacin jinki nake kamar ba jini na ba saboda rashin wayau, haka kika ga ina al'amura na?

Dan haka idan zakiyi hankali kiyi hankali na fad'a miki kenan dan wlh wannan sirrin da kika gani shine rayuwar mu u better be careful.

ficewa tayi daga d'akin tana kaiwa nan a zancen ta,  d'akin ta, ta koma... Zarya ta shiga yi yazama dole ta d'auka mataki akan haduwar salma da azeema, bangare d'aya ga d'an iskan saurayin ta, tasan mai zatayi... Murmushin samun mafita tayi.

*********
Zaid" bawan Allah gaba d'aya ya maida hankalin sa kacokam akan karatun sa, wani 'bangaren na zuciyar sa na cike da tsantsar kewar Yarinyar sa, tunanin sa yazame masa jiki dan har lokaci yakan ware dan yin tunanin ta,

wani abun yayi Murmushi wani yayi dariya, haka yake kullum zuciyar sa cikin azalzalar sa take a kanta, saidai abun haushin Sam ba shida wani kata'bus akan yadda zai nemawa kansa mafita...

UMAIMAH! Where stories live. Discover now