29

1.2K 109 11
                                    

****
'karfe goma na safe"Mus"ab ya farka daga allurar da akai masa, a hankali ya shiga bude idanuwan sa, sauke su yayi kan Dad dake dannar waya ba images San ya farka ba.

     Sosai ya shiga mamakin mai ya kawo shi asibiti? Sai dai cikin yan mintinan da basu fi biyar ba kwakwal warsa ta shiga fad'a masar komai tun daga saukar sa Airport zuwa abubuwan da suka faru dashi, saidai akwai tarin tambayoyi a zuciyar sa kwarai zai so sanin amsoshin saidai wa zai tambaya?

Ko ina wacce ta d'auko shi? ta fad'a masa akwai abubuwan da take son sanar da shi, to meye su?

   Dad d'agowa yayi dan Kai duban sa gun da Zaid"yake dan akai akai yake duban sa dan ganin ko ya farka,  aikuwa akayi sa'a ya farko, cikin farinciki ya'karasa gun shi.

Zaid" ka farko kenan? Masha'Allah, sannu"sannu Zaid! Y jikin naka?

duban sa mus"ab ya shiga yi shikam dai wannan abun yana bashi mamaki, waye ZAID? da ake kiransa da shi? Kodai na hau kace ne? to Kodai nine nakejin ba daidai ba, to su waye wadannan?

Yana da tarin tambayoyi birjik, saidai kuma waye zai fad'awa? Waye zai bashi amsa?

Dad"ganin yadda Zaid d'in ya zuba masa ido ne yasa, yayi tunanin ko dai bai dawo hayyacin sa bane?

Da sauri ya fita dan kiran likita.

Tare suka shigo da doctor d'in.

Kallon sa doctor fahad yayi, yayi ya ce, ya jikin naka?

Kallon sa mus"ab yayi ba tare da ya"amsa ba.

Doctor ganin irin kallon da mus"ab yake binsu da shi ne yasa, ya shiga yan goje2,

Kallon dad yayi yana mai cewa, Masha'Allah Alhmdllh" komai lafiya yanzun zamu d'ora shi akan magani saboda zama da yunwa har ulcer na ko'karin kama shi amma insha'Allah idan ya kiyaye ka'idoji da shan magani akan lokaci to zai samu lfy.

Masha'Allah" to doctor nagode sosai.

Yanzun dai ayi ko'karin bashi abinci yaci kafun akawo maganin sa.

********
Wayooo Allah na!........ Ni Jamila na tsallake rijiya da baya!

Wannan shine abunda hajiya Jamila take fad'a lokacin da taga kanta a tsakiyar parln ta.wayar ta ta ciro daga jaka sai haki take faman yi, layin hajiya azumi ta shiga kira sai ringing yake ba'a d'auka ba, dan haka ta zauna jugum tana dad'a gwada wa, saidai yayi ringing ya gaji ya Katse babu wani respond.

Cizon lips d'in ta tayi, saida yayi jini saidai Sam bata ma ji zafi ba tsabar tashin hankalin da take ciki, dan sam hankalin ta ya kasa kwanciya.

Sai uban gumi take had'awa tamkar babu na"urar sanyaya d'aki a parln.

****
Sosai Abba"ke kuka ganin halin da tilon d'an nasa yake ciki dan sam bai San waye a kansa ba, a cikin daren akayi masa aiki aka fito da harsashin,

Saida safe Abba" yasamu yayi waya da Mami, kwatanta mata asibitin da yake yayi, had'i da Umar tar ta tazo da kayan break.

Haka kuwa akayi, karfe 8.30am sai ga ta tazo da uban basket. shake da kayan kari.

Tana yin arba da tilon d'an nata taji wani mugun fad'uwar gaba, lokaci d'aya kuka yazo mata, kansa tayi tana kiran mus"ab d'ana, Alhmdllh Allah na gode maka, ashe zan sake saka ka a idanuna?

       Sosai take kuka tana zubawa d'an nata addu'ar samun lafiya.

Abba" ne ya shiga rarrashin ta, had'i da nuna mata a asibiti suke fa, da kyar yasamu tayi shiru.

Sallama yayi mata da zummar zai je gida yayi wanka, zai sa driver ya kawo ummi dan ita yafi dacewa da tayi Jinyar mijin ta.

******
Zaid" mai yake damunka?  tunda ka farka baka magana, ko wani abun yake damunka ne?

UMAIMAH! Where stories live. Discover now