30

1.4K 117 26
                                    

Alhmdllh nsamu sauqi, thank you for du'a, really appreciate 🙏😘💕💋

Isar ta d'akin yayi daidai da farka war Zaid" motsi ya shiga yi da hannun sa, kafun budewar idanun sa, Mami ce ta mike had'i da fad'in bari inkira doctor.

Amsa wa baby tayi da to Mami.

Mami na fita, ta matsa kusa da shi dan hakann taji tausayin sa ya kama ta. saboda yanayin sa da tagani, hannun sa ta kama a hankali, tana jera masa addu'ar samun lafiya, sosai ya 'kan'kame hannun ta, yana wani irin juya kai saboda azabar da ke ziyar tar sa. kan nasa ta ri'ke da d'ayan hannun nata, had'i da fad'in sannu.  Allah yabaka lafiya.

a hankali ya shiga bude idon sa,sake rufe idon sa yayi, a ko'karin sa na kauce wa gizon da take masa kamar Koda yau she, saidai yana sake bude idanuwan sa suka sake bashi kallo d'aya, Yun 'kurawa yake ko'karin yi dan ya tashi, fahimtar abunda yake ko'karin yi tayi, dan haka da sauri ta d'an danne sa.

Sannu kayi a hankali kaga jikin ka da ciwo musamman kafar ka Karka fama.

tana maganar ne har lokacin hannun ta yana cikin nasa, shiru yayi ya zuba mata lumsassun idanuwan sa,  itanma duban sa tayi, a hankali, ya lumshe idanuwan sa.

A ransa yana Fata kar ya farka daga mafarkin da yake yi.  sake bude idon yayi. Yana ci gaba da Kure ta da kallo, tun tana maida masa kallon har ta d'auke kanta, a ranta tana mamakin yau meye yahau kan mus"ab yake mata irin wannan kallon?

        Kodai yayi mamakin dana zo gaishe shi ne? Kuma fa haka ne dole yayi mamakin ganina a yan dubiyar sa bayan ya gama yimun rashin m. ai ni bazan biye shi ba kodan darajar iyayen mu da kuma ladar dubiya da bazan so ta wuce ni ba.

Shigowar Mami da doctor ne ya katse mata tunanin ta. Mami da sauri ta isa kisa dashi tana fad'in, mus"ab!.... Sannu kaji. tana mai shafa kana, sosai yaji wani iri mus"ab?

    Waye mus"ab d'in?

Wannan matar wacece da har take kiran sa da sunan da ba nasa ba?

Shin wai mafarki yake ko sabanin sa? Idan ba mafarki bane to wannan kenan ba yarinyar sa bace? Inaaaaaa! yarinya ko shekaru dubu zamuyi bamu had'u ba idan nagan ta zan gane ta.
bugawar zuciya ta dabn ne a inda yarinya take.

doctor ne ya Katse masa tunanin sa ta hanyar cewa ya jikin naka? Kallon doctor d'in yayi a hankali yace Alhmdllh ya fad'a a takai ce. gwaje2 doctor d'in ya shiga yi, daga bisani yace Alhmdllh jikin da sauqi kafar ce dai za'a dinga kulawa da ita garki ya motsa ta sosai, kuma gar abari ruwa ya shiga ciki, Allah ya qara lafiya.

Amin likita mun gode, cewar Mami.

ficewa likitan yayi daga d'akin. ganin hakan yasa Mami duban baby ta ce, ummi had'a masa abinci ko? bari inkira Abban ku.in sanar dashi ya farka. tana gama fad'in hakan ta fice daga d'akin.

Food flaks d'in ta shiga bubbu dewa, a sanyaye, tuwon semo ta gani da Miyar alayahu tasha Ganda da kifi, ga kuma had'in farfesun kaza mai ruwa ruwa.da yasha kayan yaji sai kamshi yake, tuwon ta zuba masa a plate. 

     Matsawa tayi kusa dashi, had'i da mika masa tuwon. a hankali ya dube ta zuciyar sa na wani irin bugu da sauri da sauri. ganin yadda yake kallon ta ne yasa taji jikin ta na rawa a sanyaye tace ga tuwon! sai lokacin ya ankara da bai karba tuwon ba, a hankali cikin muryar sa mai dad'i da kamala yace inason in wanke bakina, OK, tace komawa tayi ta ajiye abincin ta rufe, ledar dake kan drower ta d'auka had'i da bude wa.

a nan tasamu brush da teeth paste robar wanke hannun da Mami tazo dashi ta d'auko da goran ruwa, zuwa tayi gaban sa had'i da fad'in to ka tashi ka wanke bakin ga brush, tana maganar ne tana matsa masa teethpaste d'in.

UMAIMAH! Where stories live. Discover now