13

1.3K 117 14
                                    

Kuyi ha'kuri fa, har yanzun bandawo ba, d'an sawa nasamu nayi muku saboda jin dad'in ku, masu kirana nagode sosai Allah bar qauna 😘

Masha'Allah Maidambu nah, Allah y raya mana baby yasa albarka yasa dad'in musulmi ne Kekuma Allah ybaki lafiyar shayarwa 💕

Sake buga 'kofar akayi, take 'kirjinsa yakoma bugawa, bashida za'bi dan haka kawai yanufa kofar bud'ewa yayi a sanyaye. Ummi"ce yagani tsaye a kofar d'akin, dubansa ta d'anyi, gani tayi kamar baya cikin nutsuwar sa, saidai kuma ba wannan bane a gabanta dan haka tashiga tambayar sa ko baby tazo gunsa?

Muryar sa nason yin rawa rawa,, yace.. a a ai tunda na fito part d'inki na barta,, d'an jimmm! tayi kafun tashe shikenan dama naduba bata d'akin ta ne bari insake dubawa, to yace a sanyaye, dan sam yakasa sanin a wani halin ma yake!

Koda ummi"ta koma sakamakon d'aya ne babu baby babu alamun ta,, take tasoma fita nutsuwar ta,,

Zaid" idan kabar gidannan ina zakaje? alhalin mutane nan masu arziqi ne kasani duk inda kaje zasu iya su nemeka? kawai ka tsaya kagani komai ta fanjama fanjam! Allah ne shaida bakaso ba wannan al'amarin yafaru... Wani irin ruwa ne ya surnano masa Astagfiru"llah y Allah.. Ya fad'a da wata irin muryar kuka,durkushewa yayi a gurin yasoma kuka mai cin zuciya yanayi yana istigfar na abunda ya aikata.

*******
SHAGO"tunda Yasom tafiya da UMAIMAH"a mota yasoma zuba gudu,, a ransa yana fad'in Alhaji"Farouq, yau kaima kashiga tashin hankali dan baxanyi missing wannan targets d'in ba... Halama hajiya tanema takardar ta? Hhhhhhh yasaki wata muguwar dariyar bosawa a sarari,

gudu kawai yake a kan titi yayinda baiwar Allah UMAIMAH batasan ma mai yake faruwa ba.
Bai tsaya a ko ina ba Sai kano a lokacin da ya isa kano 'karfe9 na dare ne saboda mugun gudun da ya zuba,, saidai yanayin cunkoson ababen hawa ne yasa bai'karasa unguwar da zaije da wuri b, kai tsaye nasarawa GRA ya nufa,, a kofar wani tamfatsetsen gida yyi parking.

Yar paper yasamu yashiga rubutu yana gamawa ya fito daga motar saida yayi d'an dube dubensa dan tabbatar da bbu wanda ya ganshi, daukar UMAIMAH yayi yanufa kofar katafaren gate d'in ya ajiye ta,, hannunta ya bude saka mata takardar yayi a ciki kafun ya mayar da hannun ya rufe, da uban speed yabar gurin.




********
Inna"lillahi wa'inna ilaihim"raji'un"kagani ko Alhaji.. Na shiga uku na takoma bata,, babu ita babu alamar ta, shikenan na rasa ya ta akaro na biyu... ta'karasa fad'a da wani irin kuka mai taba zuciyar mai saurare, Alhaji da a lokacin yake yin waya da comsnr,, rungume ta yayi a gefensa yana shafar ka fad'ar ta ta sigar rarrashi. saida sukayi sallama da comsnr kafun ya dubeta,

Cikin halin damuwa yashiga yi mata mgana da tattausan lafazi,, lubabatu"komai tsanani yana tareda sau'ki fad'in Allah SWT ne, haka kuma yana fad'a cewa.. Yana tareda masu ha'kuri, dan Allah inaso ki kwantar da hankalin ki, muyiwa baby addu'a kuka taci gaba dayi... Shikuwa yana sake lallabata, sallamar Zaid ce tasa dukansu suka dubi kofa, cike da tsantsar damuwa... ganin Zaid take ummi"ta soma sabon kuka,
Shi kuwa cikin kaduwa da da damuwa, yace ummi lafiya? a raunane yayi mgana,

Cikin kuka ummi"tace Zaid bansan Yaya zanyi ba Zaid narasa UMAIMAH akaro na biyu Zaid"  ina matu'kar son yata inason, kasancewa da yata saidai na rasa ta, a wannan karon bansani ba ko a wani hali take ba Zaid... Zata had'u da Mutumin kirki kamar ka ko kuwa bnsani ba.... ta'karasa fad'a da wani irin gursheken kuka mai taba zuciya..

Zaid"kam tunda yasoma jin kalaman ummi yaji wani irin duhu duhu yana Sauka a kansa da cikin idanuwan sa, take ya fad'i sharaf! a sume,, da sauri Alhaji"yayi kansa, yayinda ummi tashiga kiran a... A...a Zaid dan Allah ka tashi.......

da sauri Alhaji"yayi gun Bala ya umarce shi da yaffiddo mota,,

Haruna ne ytaimaka masa suka d'auko Zaid"zuwa mota ummi biyosu tayi tna ta faman kuka a hargitse,



*******
Asubar"fari UMAIMAH"  ta farka saidai saboda nauyin da kanta yayi yasa ko d'an yatsan ta takasa motsawa bare akaiga ta tashi haka taci gaba da kwanciya a gurin sai idanuwa take rabo amma ko motsi bata iyayi, tamkar wacce d'an dannau ya taushe.

Alhaji"Farouq ne yafito dan zuwa masallaci gabatar da sallah, har yatafi bai lura da mutum ba, saida yadawo daga masallacin yana tunkarar gidan shi ya hangi mutum a kwance, addu'a yasoma yi,, a hankali ya karasa gurin baby dake kwance tamkar matacciya,, dan ta rufe Ida nuwanta saboda tsananin ciwo da kanta yakeyi.

   Shahadar 'kuda yayi ya tallafe ta zuwa cikin gidan shi,, palon matarsa hajiya Rukayya"yakai ta a lokacin tana bedroom d'inta, shiga yyi yakira ta, tana fitowa tayi arba da mutum a kwance kan tiles, a d'an tsorace ta dubi mai gidan nata tace... Abba"wacece wannan?

Numfashi yasauke, mammy nima bansani ba ganinta nayi a kofar gida da alamu tana bukatar taimako shi yasa ni kuma nakeson taimaka mata,, sauke numfashi tayi a ranta tace... Allah ya taimake mu gar garin taimakon nan naka ka kwaso mana jangwam, a zihiri kuwa murmushi takaitacce tayi kafun tace... to inaga bari inkawo ruwa a yayyafa mata mugani ko zata tashi.


****
Kai tsaye asibiti aka nufa da Zaid da yadad'e a cikin doguwar sumar da yayi,

Direct emergency aka nufa dashi ganin condition d'insa. Bayan doctors sunyi ko'karin farfad'o dashi ne suka shiga masa binciken abunda ke da mun shi.

Angano jininsa da yayi wani irin hawa ga damuwar da take barazana ga ransa,, sosai su dad suka shiga tashin hankali, matu'ka bayan doctors sunyi musu bayanin ciwon Zaid, ummi kam kasa ha'kuri tayi tashiga zuba kuka, cike da damuwa mai tafiya da rai.




Bandawo ba fa.. 😂Tohm wannan d'in ma dai time nasamu 😊ade di u all 😘

UMAIMAH! Where stories live. Discover now