19

1.1K 96 9
                                    

Wata irin muguwar tsawa boka yadaka mata had'i da nunata da hannun sa, yace ke! Rahamu"garki sake kiyi Amannan muddin kikayi to hakan na nuni da Zaid" yafi 'karfinki, tabbas ko da wannan tsafin yayi tasiri to fa yayi rauni da Kashi sittin cikin dari!

          Da idanuwan ta da suka gama firfitowa sukayi ja"ta dubi boka, bata iya tayi magana ba Sai gyad'a kai da tayi alamun taji ta amince, daga haka ya d'auko wata Yar karamar 'kwarya yabata jiki na rawa ta amsa yace... Wannan shine asalin tunanin Zaid" garkiyi wasa dashi matu'kar ruwa yata'ba'kwaryar to fa Zaid'" zai dawo natsuwar sa... Ki kiyaye! ki kiyaye! Ki kiyaye!  yana kaiwa nan yace ku fice la'anannun Allah, saida ta zubewa boka ledar kudade, kafun tace godiya muke la" ananne.

            Suna fita ta turo su shago"suka fito da Zaid".... Mota tashiga ita da salma dan nufar masaukin su, su shago ma maboyar su suka nufa da Zaid,

    Ai Rahamu" tana ganin kanta a gida ta fad'a toilet tasoma she'ka amai,, a wahalce ta fito daga ban d'akin, a tsora ce salma ta dubeta, mommy" Kar dai aman kikayi?

       batace komai ba Sai lumshe idanuwan ta da tayi tana ci gaba da sauke numfashi,

Amma gskiya mommy baki kyauta ba shikenan Kin rage tasirin abun? Saboda Allah? Allah ni dani ce bazan yarda inyi aman ba....

Ke! Rahamu ta daka mata tsawa, dan ubanki sai kije gun bokan ki fad'a masa nayi amai... tunda sani zaiyi,, kuma ma wannan joining idan ban amayar dashi ba Sai ki fad'an yadda zanyi kinsan bala"in da naji a cikin da mako shi na?  Sai kace wacce tasha mugun abu? (ikon Allah Yo'ai mugun abun kika sha 😂lol)

        Salma billahillazi to dake ce na tabbatar da ko baki mutu ba Sai kinyi d'an gawa.. ta'karasa fad'a a wahalce tana fiffida numfashi tamkar wacce tayi wasan tsere.

Fita daga d'akin salma"tayi tana gunguni, dan sosai taji haushin mahaifiyar ta ta dan itakam tsoronta d'aya Kar Zaid ya'ki auren ta.

Tana fita Rahamu" tasaki tsaki, Shegiya tanason taga laifina dan bataji masifar d'auke cikin jinin bane, yo ni naki a had'a mun duka jinin jikin Zaid d'in in kurbe ne?
Saidai maseefar jinin ce ai abun gudu, shegen yaron shi yasa gashinan a tafashe ko tsoron mutane ba yayi... Waiii wayyoooooo,, doles yau insha madara ko gwangwani takwas ne....!

      ********
       Baby" bata tashi ba Sai gurin isha"i, tana farkawa, Adiya ta nufeta, tana mata sannu sai kallon ta baby tayi,, Mami" ce ta shigo d'akin, tana ganin baby, ta farka, ta 'karasa gurinta itama baby tana ganin Mami tayi murmushi dake nuna ta gane ta, sannu Mami tayi mata,, sai daga Kai tayi,,
ban d'aki ta d'an ri'ke ta suka shiga tace kiyi wanka kiyi al'wala kiyi sallah,
Gyad'a mata kai tayi... tayi wankan ta tsaf kamar yadda kwana biyu taga Mamin tana yi mata, haka ma al'wala tayi Shima yadda Mamin ke mata.

Tana fitowa Mami ta gani ta kabbarta sallah, dan haka itama ta tsaya a gefenta na dama, duk yadda Mamin tayi haka itama takeyi.... har suka sallame.
duban ta Mami tayi tace maike miki ciwo?

girgiza kai tayi cikin muryar ta mai sanyi tace babu komai. dad'i sosai  Mami taji ganin yadda yanzun yarinyar take cikin nutsuwar ta, gashi ga dukkan alamu tanada hankali da nutsuwa.
Wata Yar sheikh ce ta shigo d'akin da flaks d'in abinci,, ta koma shigowa da drinks ruwa da fruits.

Mami ce ta zubawa baby abincin, ta kuwa ci sosai musamman had'in kazar da yaji tafarnuwa.

Mami ma abincin taci, bayan sun kammala ne, sheikh ya aiko akira su,, bayan sun zauna a babban setting room d'in sheikh d'in yayi wa Abba umarnin ya tambaye ta ko zata San ita d'in wacece, dake abban yayi masa bayani kan tsintar ta yayi ba yarsa bace,

Duban baby, Abba yayi wacce kanta ke sunkuye,, Rukayya" yace... Saidai bata ko d'ago ba bare tasan da ita yake... dan haka ya sake cewa YARINYA..! da sauri ta d'ago da wani irin bugawar zuciya... Idanuwan ta ne suka Sauka cikin na mus"ab da haushin ta ya isheshi... na ganin yadda ake mata magana amma ta wani 'kyale mutane tamkar bataji ba Sai tsaki yake kasa kasa shi kad'ai.

ga mamakin mutanen gurin... tashi baby tayi tanufa gun mus"ab ta zauna kusa dashi tamkar zata shige jikin sa... Sosai hakan ya baiwa kowa dake gurin mamaki.. Ita kuwa babu abunda ya dameta, Mami dake kusa dasu ce tayi karfun halin taba baby tace... yata, kallon ta baby tayi tana murmushi, Mami tace, yata daga ina kike? Su waye iyayen ki? Kuma ya asalin sunan ki?

Duk da ita Mami da biyu take wannan tambayoyin... shiru baby tayi tamkar mai son tunano wani abu,, daga bisani ta duba mus"ab tace shine iyaye na!

Shiru wurin ya d'auka, tsabar mamakin abunda tace,,  shi kuwa mugun takaicin ta ne yakama shi ji yayi tamkar ya sha'keta,

baby kam daga fad'ar haka tayi shiru tana sake duban sa tana murmushi bata damu da yadda yake zabga mata harara ba...

Abba"kam maida dubansa yayi gun abu haula, yai masa bayani da turanci.... ya Kara da fad'in Kodai har yanzun aljanun suna tare da ita ne, murmushi abu haula yayi yace Bana tunanin haka, face dai akwai wani abu da ubangiji ya boye cikin al'amarin, amma koma Menene zamu ci gaba da addu"a... Yanzun ku tafi gida dare na dad'a yi, godiya sosai Abba yayi masa kafun suka tafi, cike da tunanika,


WANNAN KENAN!

***bayan su Rahamu sun dawo da kwana biyu aka dawo da Zaid" 'kofar gida su shago suka watsar dashi kamar abun banza,, mai baiwa fulawa ruwa ne yazo fita ya ganshi nan aka d'auko shi zuwa cikin gida, dad na dawowa yasa aka sashi mota zuwa hospital,

Gwaje Gwaje aka shiga yi masa inda likitoci suka Gano inyi ta masa amfani ne da sinadarin dake saka mutum bacci yayin da yabi ta numfashin sa,,

Sosai dad yayi ta mamaki to mai ya had'a Zaid da sinadarin bacci?

Kwanan sa hud'u a asibiti kafun yadawo hayyacin sa, yana ganin dad yasoma kuka.. Sosai dad ma hankalin sa yatashi, nan yashiga tambayar sa mai yafaru dashi ne?

Dad tun ranar dana kwanta bacci bansake sanin inda Jaina yake ba....

Inna"lillahi wa'inna ilaihim"raji'un,, mu ai har muna fad'in Kodai bakaji maganar mu bane ka tafi neman UMAIMAH?  Ikon Allah Lallai dole ayi bincike a gidan dan gane ko maike faruwa.

Satin sa biyu a asibiti aka sallame shi,  ummi ma da yan uwansu sunzo duba Zaid"  

Ma'aikatan gidan dad yatara dan jin yadda akayi babu tsaro har aka sace Zaid babu wanda yasani tambayar tasa tafi yawa ga mai gadi Dan shine alhakin kula da kofa ke kansa,

Saidai kuma yayi ta rantsuwa kan baisan komai ba, ko ransa da dad zaiyi dan acewarsa baisan aikin sa ba, Zaid ne ya bashi ha'kuri had'i da neman alfarmar ya kyaleshi yaci gaba da aikin sa....amincewa dad yayi da shara d'in idna hakan ta sake faruwa sai yabar masa gidan sa dan wannan shine Karo na uku da hakan ta faru.

Bayan kwana biyu Zaid ya murmure, yaji sau'ki sosai, nan yakoma makaranta yashiga karatu babu kama hannun yaro duk da iyayen Cary over d'in dake gareshi.... Haka ya matse da iya ko'karin sa, duk ranar da baida lectures kuwa yana company gun dad,

Wani lokacin kuma yaje Niger gun ummi"

tsawon kwanakin basu taba haduwa da Rahamu ko salma ba wannan yana cikin tsarin boka na garsu had'u har Adadin lokacin da ya basu.

Yau ce ranar da boka ya amince Rahamu ta gana da Zaid dan sake fad'a masa burin ta a Karo na biyu.....!

Allah wuya na ke ciwo....... 😢


Xinnee smart 💋💕👌

  

UMAIMAH! Where stories live. Discover now