11

1.5K 137 35
                                    

Dare ne sosai yayinda ko wani d'an Adam daren yakasance mahuta a gare shi, sa'banani Zaid" da sai faman juyi yake tunanin sa nazarin sa, duk suna akan UMAIMAH"baby,   hakika reaction d'inta na yau akan sa ya matu'kar bashi mamaki tabbas ko ba'a fad'a masa ba baby haushin kalaman salma"taji shine dalilin da yatun zurata har taiwa salma wannan aika aikar,,

          Wani juyin yakoma yi,, yasa ki tattausa murmushi dake sake nuna tsantsar nutsuwar sa. duvet yaja had'i da yin addu'a dga bisani yyi light off.

            Asuba ta gari zaidu! 😂🕯️

*********kwanaki sunja, abubuwa da yawa sun faru wasu kuma suna kan faruwa, wanda tun ranar da tsautsayi yasa salma taiwa Zaid magana a gaban baby har yau bata koma ba,, saboda a cewar ta aljanun baby mahaukata ne. Gwara tanayin nesa nesa da ita....

a yanzun Zaid"yana matakin aji uku a makaranta,, yayinda baby jiki saidai neman sau'ki ga Allah,,

         Yauma"a zaune suke palon ummi" yayinda Zaid yake d'an duba takardun shi haka kuma lokaci zuwa lokaci 'kirjinsa yake bugawa wanda yarasa dalilin haka baby tana zaune a kusa dashi rike da tap d'in ta da ya mata playing karatun alqur'ani da wata Yar yarinyar larabawa take karantawa, a lokacin ummi"tana kitchen ne tana ko'karin had'a abincin dare Kasancewar lokacin 'karfe biyar na yamma ne.

          Zaid" daina karatun yayi, ya zubawa baby ido, cike da wani irin bugu da kirjin sa yakeyi,, tamkar tasan ana kallon ta tadaina kallon tap d'in tayi ta d'ora idanuwanta, saitin da yake, murmushi tasaki wanda har saida ha'kwaran ta suka bayyana masu d'auke da kyakyawar ushirya.

a lokacin da zaka ganta bazaka ta'ba cewa bata lafiya ba.
Zubawa juna ido sukayi na seconds daga bisani,, ya rike hannun ta cikin sautin sa mara hayaniya yasoma magana, yarinya ta! dubansa tayi wannan karon saidai batayi murmushi ba Sai idanuwa da ta zuba masa, murmushi yayi mai taushi kafun yace ... Mai yasa nakejin wani abu a game dake? Lokaci d'aya kuma da mummunar fad'uwar gaba? hakika inajin wani iri a game dake kema kinajin abunda nake ji ne?

    Sake 'kura masa ido tayi,, a ransa yasake jin wani irin tausayin ta da kaunar ta suna sake huda shi, a lokaci d'aya...har baisan lokacin da hawayen son ta da tausayin ta suka zubar masa ba. bai Ankara ba yaji hannunta akan fuskar sa.. tana aikin share masa hawayen,,  hannun nata yarike akan fuskar sa, kafun yace... INA SONKI.. yarinya ta! ke fa? Wani duban sa takoma yi.. Saidai wannan karon idanuwanta a lumsashe suke. Shiru suka d'auka duk su d'in,,
Kiran sallah, da kuma alamun shigo palon da ake ko'karin yi ne suka saka shi sakin hannun ta had'i da mi'kewa dan tafiya masallaci,, binsa da ido tayi har yafita.

***Boka a gaskiya ina cikin damuwa,, naso zuwa saidai hakan bai samu ba, shi yasa ma na kira ka dan in d'an fad'a maka kafun in samu zuwa,, dan a gaskiya abun yafi karfin tunani na.

daga d'aya bangaren boka yashiga cewa.. Maza fad'i damuwar ki tattaba tsine ya share miki hawayen ki... Cike da damuwa hajiya Rahamu"tashiga cewa.. Waton yata salma"ce ta d'auko mun rigima,, da sauri boka yace.. Nasan wannan fad'i wani inji.. sauke numfashi tayi kafun taci gaba da cewa.. Sai matsalar Alhaji,, koma dakatar da ita yayi yace... Nasan wannan ma.. to boka sune matsalolin da suka sakani a gaba,,

Ya"kike so ayi?

boka ya bu'kata.

Bayani tasoma yi masa... boka abunda nakeso yanzun shi yaron na"amince inason yata ta aure shi dan na hango amfanin da zaiyi, bayan auren zan San yadda zanyi yasamo mun duk wani sirrin arzikin Alhaji!

Angama! fad'i bu'katar ki ta gaba.

Cike da farinciki tace... boka inason Alhaji asake yi masa mugun 'kulli ta yadda sai abunda nace masa...

UMAIMAH! Where stories live. Discover now