28

1.2K 108 14
                                    

Abba" bai isa gurin ba saida Cp yazo suka tsara duk yadda za"a tunkari gurin kasancewar da dare ne.

         Wayar Abba"ce ta sake yin kara, wancan number dai ce, dan haka jiki na rawa ya daga Cp ne ya karbe wayar had'i da saka ta hands free. ga dukkan alamu Alhaji"baka son d'an ka!

Abba"jiki na rawa ya shiga cewa ina... S... on... sa wlh dan Allah garku cutar mun da yaro shi kad'ai na mallaka a duniya.

Ko nawa kuke so zan baku.

Kayi mana shiru! Kaji ko, an fad'a maka dukiyar ka muke so ne?

to bari kaji, mu ba kud'i ne yasa muka d'auko d'anka ba dan cewa akayi mu kashe shi, shine na tausaya maka na ce kazo kafun mu kaddamar masa, shine ka kwaso zugar kwala"wa.

to matu'kar kana bu'katar d'anka ka gaggauta sallamar su idan kuma ba haka ba.... to ka shirya makoki.

Muryar Abba cike da damuwa yace shikenan, zan sallame su dan Allah nidai garku cutar mun da yaro, d'iff aka katse kiran.

Shiru Abba yayi yana duban Cp"kwantar masa da hankali Cp ya shiga yi.

******
Sautin horn mai karfi da security d'in gidan su kaji ne yasa suka fito da sauri dan ganin maike faruwa, basuga kowa ba Sai mutum da suka gani yashe a kasa, a hankali suka karasa gurin sa, suna masu saita shi da bindigu, dan shirin ko ta kwana.

     Asalin mai gadin ne ya gane Zaid" da sauri ya karasa gunsa yana fad'in zaidu... Inna"lillahi wa'inna ilaihim"raji'un,  take sauran suka gane waye a gurin da sauri suka d'auke shi zuwa cikin gidan, zuwa wannan lokacin tuni ya sume.

******
Hajiya azumi" na shirya fa, cewar Jamila.. OK tom kawai ki d'au hanya ai kingane kwatancen. a d'aya bangaren hajiya azumi ta bata amsa kasancewar duk maganar da suke sunayin ta a waya ne.

to shikenan Kawa ta nagode.

daga haka Jamila ta sauke wayar, jakar ta ta d'auka, sai key d'in mota.

Kasancewar mai gidan ta ba mazauni bane yau ma anyi sa'a baya kasar ma gaba d'aya.

sauri2 ta isa gun motar ta, key tayi wa motar, mai gadi ne ya bud'e mata gate d'in gidan ta fice yana binta da adawo lafiya.

******
Da hanzari mai gadi ya nufa part d'in Alhaji" ya nufa, kwankwasa wa ya shiga yi jikin sa sai rawa yake.

Alhaji Tahir"da dama ba wani isheshen bacci yake samu ba, dan yau ciwo gobe lafiya haka yake fama.

               da sauri ya fito daga d'akin sa, yana fad'in lafiya... dan ya gane muryar mai gadin gidan sa ne. jikin sa sai rawa yake sabida yasan ko meye yake kiran sa kanshi to ba alkhairee bane dan wannan kiran baiyi kama da na lafiya ba.

Yana fitowa mai gadi ya shiga nuna masa 'kofa, kallon sa yakai kan kofar dan ganin mai yake nuna masa. idanun sa ne suka Sauka kan security d'in gidan da suke d'auke da mutum a hannun su. Kasancewar gurin da wadataccen hasken solar.

'karasa wa gurin securities d'in sukayi da zaid dake sume.

kallon Zaid dake hannun su Alhaji" yayi, take ya gane shi. da sauri ya karbe shi daga hannun su ya durkushe a gurin tare da Zaid a hannun sa. Inna"lillahi wa'inna ilaihim"raji'un.  Zaidu zaidu.... Kai ne?  Sub'hanallah... Zaid"! sambatu Dad ya shiga yi, tamkar yaro ko wanda ya zare, yi yake yana jijjiga Zaid d'in.

Saidai shi bai masan mai yakeyi ba.

*******
Ko da hajiya Jamila ta isa titin gidan, parking motar ta tayi a d'an nisa da gidan.fita tayi daga motar ta rufe ta, a hankali ta karasa gidan, a sad'ad'e ta shiga samun yaran da suka sa aikin tayi a gidan.

UMAIMAH! Where stories live. Discover now