7

1.5K 146 6
                                    

Sake duban Pic d'in dake jikin yagani tabbas yarinya ce, Inna"lillahi wa'inna ilaihim"raji'un,, yashiga maimaita wa... rasa wani hali yake ciki yayi dan kuwa tsakanin farinciki da bakin ciki ya rasa wanne zai yi,, sai zubawa mujallar ido da yayi,, har abokan tafiyar sa suka zo bai San a wani muhalli zai saka yanayin sa ba, haka yabisu suka tafi.

         Koda suka koma damuwa takasa barin zuciyarsa,, hakika idan zaiwa yarinya adalci to kuwa ya mai data ga iyayenta tunda har address d'insu ansaka,, yasan bazai wahala gun maida ita gida ba. Saidai shi miye makomar shi? Yatashi a mara gata kenan? Wanda bashida wani tsaya yye ko dan uwa da zai duba yaji sanyi,? haka ya dinga saka da warwara,, wattannin su2 a kauyen su baubani,, saidai zakayi mamakin yadda baby tayi baki kamar me. tunda yafara ganinta yaji a jikinsa duk inda tafito to gidan masu dashi ne,, adalci d'aya zaiwa rayuwar ta matu'kar yanason ganin farinciki ya ke waye ta to fa shine ytaimaka mata ya maida ta gida,, Allah bazai barka ba Zaid zai dubeka ko dan Kyakyawar zuciyar ka,, Kaci gaba da tawakkali dashi domin shi d'in abun dogaro ne,, wannan shine abunda zuciyarsa take fad'a mai.

             Yau laraba"kuma a yau ya yanke kan zai sanar da baubani zaije neman danginsu, saidai kuma antashi da baubani cikin. Ciwo mai tsanani wanda har baisan wanda yake kansa ba,,, wannan ne yasa ya ha'kura, aka shiga nemawa baubani magani,, saidai Sam babu sau'ki ganin haka ne yasa yanemi matar baubani kan ko Za akai shi asibiti cikin gari agani,,, dubn sa tayi tace... kayi ha'kuri zaidu amma a gaskiya bazan baka baubani zuwa asibiti ba. Saboda wannan ciwon nasa da kagani,, garin nemar wa kanwar ka magani ne yasame shi,,

         Inna"lillahi wa'inna ilaihim"raji'un"baaah bangane ba,

Labari tashiga bashi.... Baubani yashiga nemar wa kanwar ka magani tun lokacin da ya fahimci asiri ne akai mata,, to makarin asirin ba ta hanyar da baubani yabi yake ba kuma akwai tsarin qarqari a Jikinta ta yadda duk wanda yayi ko'karin nema mata lafiya,, abun zai Shafe shi, dan haka kawai muyi ha'kuri aci gaba da na gida dan ciwon sa ba na asibiti bane,, ta'karasa fad'a idonta na cikowa da kwallah.

            Sosai Zaid yashiga tashin hankalin jin abunda yafaru da dalilin ciwon baubani,, saidai babu yadda ya iya saidai ya zubawa sarautar Allah ido. yau satin baubani da kwanciya cuta asubar fari yace ga garinku nan.

Tashin hankali... Wanda ba'a sa masa rana,, sosai Zaid da matar baubani suka shiga tashin hankali mawuyaci saidai babu yadda suka iya domin basu isa hana Allah ikon sa ba, bayan sati da mutuwar baubani matarsa tasamu Zaid inda take shaida masa zata koma garinsu can gurin yankin bidda kauyensu yake,, godiya sosai Zaid yayi mata na irin taimakon da sukayi musu,, Shima had'a musu kayansu yashiga yi,, yanemi abun Hawa suka wuce garin Abuja bayan sunyi sallama da jama'a,, zuciyoyin kowa babu dad'i tsakanin Zaid da matar baubani suka rabu.

            Bayan sun shiga garin Abuja,, mai mashin ya tambaye shi inda zai sauke su,, nazari yashiga yi,, har daga 'karshe baisan lokacin da ya ambaci unguwar su baby"ba

         Cikin ikon Allah ya fad'a daidai,, mai mashin kuwa yakai su unguwar saidai baisan layin ba dan haka sai Sauka sukayi, nan yashiga tambaya har yadace da kwatwncen da akai masa, duk wannan bulayin da yakeyi baby tana hannun sa. tangamemen gate d'in da aka kwatan ta masa ya duba had'i da sake duban number dake jikin gidan. tabbas gidan ne,, shiru yayi yana nazarin yadda zai shiga,, yayinda baby ta zuba masa idanuwanta.

ganin lokaci sai tafiya yake... dan yanzun gurin karfe 4 yamma ne gashi ko azahar baiyi ba bare la'asar shi yasa ya tattaro sauran karfin zuciyar da yarage masa ya nufi gate d'in gadan gadan.

'kwan'kwsa wa yayi,, mai gadi ne ya le'ko ta yar'karamar 'kofa dan ganin mai buga gidan,, ganin mata shi a tsaye yasa ya bude kofa had'i da tambayar sa malam lafiya? ba tare da ya lura da baby dake hannunsa ba,

UMAIMAH! Where stories live. Discover now