Ummi"ce zaune akan kujera yayinda kan baby ke kan cinyarta,, kalaba take mata itakuwa ta zubawa sama ido tamkar wacce ke neman wani abu,, sauke mata kanta ummi tayi tace ina zuwa baby kallonta kawai tayi... Kissing forehead d'inta ummi"tayi.
Ummi"tana wucewa da minti biyar, ta tashi tana wuri wuri da ido ta fita, daga palon tangal tangal ta fita daga part d'in ba tareda kowa ya lura da ita ba Kai tsaye part d'in mommy ta nufa tana gyngyada Kai tana zazzaro idanuwanta,, tana shiga palon tasamu mommy kwance akan d'aya daga cikin cushions d'in katafaren palon.
da alama bata shirya ba bacci ya d'auke ta agun,, zuwa tayi saitin kanta ta'kura mata ido ko 'kyaftawa batayi... juyawa hajiya Rahamu"tazo yi dan sake gyra Kwanciyarta idonta yasauka akan baby da ta kafeta da idanuwa. a matukar zabure ta tashi har tana yarda zani gurin yin gefe d'aya tana neman ta ina zata arce ganin da gske dai yarinyar kallonta take kuma da dukkan alamu haukarta ce ta nuna mata haka. Shi yasa ta daidai ta natsuwarta... taja hannunta duk da har lokacin,, da akwai fargaba a ranta amma haka ta kokarta. janta take har zuwa kofar part d'inta. kafun tarike dukan hannayenta tsabar karfun hali tashiga marinta had'i da yimata gargadi itakuwa ko hawaye babu a idanuwanta sai Jan da sukayi...... Ummi da tunda tafito Palo bataga baby ba yasa tashiga neman ta... tana fitowa compound d'in gidan... Idanuwanta yasauka kan su.... Sosai ranta yabci da irin yadda hajiya Rahamu take dukan baby tamkar wata babba..... da sauri ta karasa ta fizge yarta cike da bacin rai tashiga cewa... haba Rahamu "wannan wani irin d'aukar alhaki ne zaki samu yarinya karama haka kiyita duka tamkar kinsamu sa'ar ki a gskiya wannan abun yayi yawa bazan d'auka ba... ehh Lallai kam lubabatu... Nuna mun kina da mahaifar haihuwa,, amma Kisani nima ba juya bace kuma wlh kishiga hankalin ki dani a cikin gidan saboda wannan banzar musakar yar ta.... d'au.....! Ummi ta sauke mata wani irin mahaukacin Mari da ya"matukar bata mamaki wanda har takasa boye hakan.... jin Jina Kai ummi tayi had'i da fad'in,, Rahamu... Kisani zan iya jurewa komai naki amma bazan jurewa kaskanta mun ya ba. Kuma inaso Kisani wannan yakasance rana ta 'karshe da zaki d'ora hannunki akan fuskar yata,, bare kuma kibita da munanan kalamai kuma Kisani ba a jefar jarabawar ubangiji da mummunar Kalma dan nasani ita da yajarabce ta da wannan lalurar bawai dan ta masa wani abu bane.... haka kema da ya azurtaki da lafiya bawai dan yafi sonki bane dan haka a gunshi muke fatan dacewa da rahama,, wlh kiyi gaggawar adana 'kazaman kalamanki akan yata domin itace duniya ta Kisani zan iya yin komai domin ta... Idan nace komai tofa ina nufin komai! tana kaiwa nan tadauki baby da ke faman zaran ido... Suka wuce.
Rahamu"kam tsabar mamaki da tsoron lubabatu daskarar da ita sukayi a gurin,, da 'kyar taja jiki zuwa d'aki wayarta ta janyo jiki na rawa ta dannawa boka Kira take tasanar dashi abunda yafaru,,, cewa yayi da ita karta samu damuwa Za ayi maganin lubabatun har baby...... Kafun sukayi salllama still zuciyar ta naci gaba da tunaninka kan abunda yafaru tsakaninsu.
Abunda Rahamu bata sani ba shine.... Bokanta shi yasa aljanin jikin UMAIMAH"zuwa part d'in Rahamu dan a razana ta,, saboda yana bukatar kud'i,, kuma yasan daga ta razana zata Kai kukanta Gare shi (wa"iyazu, billa)
************
Rayuwar UMAIMAH"tana ci gaba da kasancewa cikin tabin hankali,, wanda a kullum ummi sake shiga fargaba da tashin hankali take ga dad d'inta yanzun Sam yadaina bata wata kulawa wanda hakan nada nasaba da asirin da Rahamu tasa aka banka mishi.Zuciyar ummi kullum cikin was wasi da tunanin mafita wa rayuwar yarta take haka addu'a kullum yi take,, saidai abun na UMAIMAH"sai godiyar Allah. dan sam babu wani ci gaba,, ko ummi taso yin wani yunkuri kan lafiyar yarta sai takasa, hakan yasa ta zubawa sarautar Allah ido tana matukar kulawa da yarta da taimakon uwani mai aikinta.....
'karfe1 na rana ne lokacin UMAIMAH"tana bacci ummi tanufi d'akinta dan gabatar da sallar azahar,, uwani ma tana sashensu na masu aiki tana tata sallar,
UMAIMAH"ce tafarka, tashi tayi tana ta dube dube tamkar mai neman wani abu,, a haka ta kama handle d'in kofa tafita,, lokacin duk ma aikatan gidan sun shiga sallah,, dan haka tasamu ta fice daga gidan ba tare da kowa yaganta ba,, tafiya take bingil bingil kanta ko d'an kwali babu ga kitson ta na kalba yasauka akan gadon bayan ta, doguwar riga ce a Jikinta mara hannu,, duba d'aya zakai mata kasan mai tsada ce, yayinda kafafuwanta babu takalma.........tafiya take ko hutawa batayi har tafice daga unguwar gaba d'aya.
*************
Ummi bayan tayi sallah,, tafito kitchen tashiga ta d'ebo abinci taci,, uwani ce ta shigo dan jin ko akwai abunda Za ai mata,, a a uwani babu abunda nake bukata yanzun saidai zuwa anjima sai muyi hidimar girkin dare ko? tafad'a fuskarta cike da fara'a.... Murmushi uwani tayi to hajiya a tashi lafiya,, har uwani tamike ummi ta dubeta tace.... Uwani duba mun ko baby ta tashi dan yau ta jima tana bacci,, amsawa uwani tayi da to hajiya,,d'akin tashiga saidai me... Wayam babu baby babu alamun ta, cike da mamaki da fargaba ta tura kofar toilet duk da tasan da wahala baby ta kasance a ciki,, saidai nan d'in ma Wayam babu ita babu labarinta take hankalinta yatashi a sanyaye ta fito tace hajiya bata ciki fa..... Cike da fargaba,
Wani dummm! 'kirjin ummi yabada sauti bata ciki fa kikace uwani Kodai baki duba da kyau bane? Uwani da gumi yagama jikata tace wlh hajiya Naduba bata nan,,
Ai ummi bata jira jin mai uwani zata sake fad'a ba tanufa d'akin,, saidai babu baby babu alamun ta,, a haukace ummi tashiga bincike part d'in ta ko mai kama da baby babu, compound d'in gidan ma nan ma shiru,, part d'in Rahamu taje saidai bata nan,, dan shaf ta manta kwanan ta biyu da yin tafiya tana Niger gurin wasu yan uwansu,, take jiri jiri yasoma dibarta Inna"lillahi wa'inna ilaihim"raji'un...... Shine kalmar da tashiga maimaita wa,, karfin kalmar ne kawai yasa ta iya karasa wa palon ta,, gumi take kota ina,, uwani da sauran masu aikin gidan take suka shiga neman baby a cikin unguwar da makotan unguwar,, amma har bayan la'asar babu alamun ko mai kama da baby dan haka suka koma gida dan asan abunyi....
Tashin hankali wanda ba'asa masa rana!
Xinnee smart 👌💋💕😂✌️
YOU ARE READING
UMAIMAH!
RomanceDad! Mi... ji.. n... UMAIMAH.. ne! ****ta Yaya musaki yasan soyayyah? Wannan wani salon munafurcin ne!