10

1.7K 144 22
                                    

This is for you beb "(SURAYYAHMS) 😂🤣u made me laugh today 😂😂,, can't express how much happy I am, I just pray for you that may God make u happy more than the way you made me,
Ina kuma tayaki murnar fitowa d kyakyawan sakamako
All the best 🤝🏻 💕💋💕🙏

Wani irin murmushin farinciki, salma"tayi,,dan bata d'auka mommyn zata amince da wuri haka ba, shi yasa taji wani farinciki,

Yayinda hajiya Rahamu"  tashiga kitsa nata tunanin zuwa lokacin da zata tabbatar dashi, tabbas akwai amfanin da salma zatai mata wannan karon Sam ba zatayi wasa da damar ta, dole burinta yacika!

*****
Salma gani d'aya taiwa zaid taji tana 'kaunar sa, wanda hakan baya rasa nasaba da kyan fuskar sa da kyan kyakyawan'kirar jikinsa, dan zaid akwai Kira mai kyau duk da ba wani babba bane dan a yanzun bai fi shekaru 25 ba,, salmar ma ta girme shi da shekara 1.
Saidai saboda yanayin siran tar ta bazaka ce ta girme shi ba dan siririya ce sosai, tanada doguwar fuska da dogon hanci saidai baka ce wanda bata godewa Allah da kalar da yabata ba saida tashiga cikin jerin marasa godiyar Allah ta hanyar shafa man kanti dan haka ma bazaka ce mata baka ba saidai kanayin tozali da 'kafar ta zaka sheda hakan dan sosai kafar ta takeda baki duk da irin kashe mata kud'i  da take na mayukan dake haska bakar kafa, saidai kafar sam taki karbar hasken.

Wannan kenan!

Rayuwar Zaid" a gidan Alhaji Tahir yuguda"  rayuwa ce mai tattare da tsantsar farinciki da sakewa wanda zai iya cewa sai yanzun ne yake rayuwar freedom dan idan ya had'a da rayuwar da yayi a baya tabbas waccan zai iya sata a rayuwar bauta!

Sosai yake girmama ummi yake bata matsayin mahaifiya dan ko babu komai ta cancanci wannan matsayin, dan ita d'in mace ce mai saukin Kai fara'a mutumci da tausayi tunda yazo gidan take ko'karin sakewa dashi had'i da bashi wani gurbi na musamman a cikin gurbin da uwa kan baiwa d'an ta.

Wannan alkhairee nata yana dad'a saka shi jin a duniya bashi da iyaye sama dasu domin Alhaji Tahir ma, haka yake masa yana ko'karin bashi ha'k'kin sa na matsayin da a gunshi,, dan tuni yasa aka gyra masa sashen da a da yake matsayin na Khaleel.

Yake zaune a ciki haka ma, bangaren sitirru saida aka tabbar da an sha'ke clothes set d'insa da kaya na alfarma.

A bangaren karatun sa ma, tuni ya rubuta jamb, inda yasamu shiga jami"ar Abuja... A inda yasoma karantar liktanci,,

Shakuwar sa da UMAIMAH"kuwa sai abunda yaci gaba, dan haka Zaid"  bashida matsala a gidan hatta hajiya Rahamu"  bata nuna masa komai,

Saboda shirin ta da Allah ne kawai yasani, saidai shi Zaid yakasa yarda da ita wanda shi kansa yarasa dalilin rashin yardar.

*****
Zaune yake a garden d'in gidan yana duba takar dunsa dan kullum haka yake matu'kar yadawo makaranta d wuri, sanye yake da riga da wando na kaftan, wanda suke kalar ruwan madara d'inkin gajeren d'inki ne, sosai kayan sukayi kyau a jikinsa kansa yasha askin saisaye, wanda babu gashi kuma ba tas aka kwashe kan ba.
hannun sa kuwa daure da agogon azurfa, mai kyau da tsada sai takalman sa budadu masu kalar brown.

a kasa yake zaune kan carpet, yayinda baby take daga gefen shi a zaune itama tasha kwalliyar ta cikin doguwar riga mai sirrin hannu, rigar kalar coffee ce dan haka tadace da kalar kyakyawan fatar jikin ta. Kanta babu d'an kwali dan haka ma dogon gashin ta yake a bayyane,, wanda akaiwa kitson Kalba da suka kwanta a gadon bayan ta,, kunnenta d'auke yake da d'an karamun eye rings.

Wasa take da ci yayin dake gurin tamkar 'karamar yarinya,, wanda a lokacin kamata yayi tana ajin islamiyya,, saboda yammaci ne,

Saidai dalilin lalura gata a zaune tana wasan da yan shekaru uku hud'u ne yakamata suyi bawai ita da a yanzun take da shekaru 14 ba.
Zaid ne yake wannan tunanin yayinda yake dubanta,, cike da tausaiya wa, wani murmushi ne yasu'buce masa lokacin da yaga itama tanayin murmushin wanda baisan dalilin yinsa ba kawai ya tsinci kansa da taya ta murmushin.

UMAIMAH! Where stories live. Discover now