27

1.3K 109 11
                                    

Tunda safe Abba yabi jirgi zuwa Abuja, saidai ko da ya'ki says Airport d'in, babu mus"ab babu alamun sa.

Sosai hankalin Abba ya tashi ganin iya bincike anyi tun daga Airport har zuwa guraren shiga mota, shiru kake ji babu wanda yace yaga ko da mai kama da mus"ab d'in ne, har yamma Abba yana tare da jami"an tsaro dan gano inda mus"ab d'in yake,

       Anje har kamfanin layin mtn, anyi bin diddigin layin mus"ab d'in saidai wayar har lokacin a kashe ta ke. tun bayan inda yayi waya da iyayen sa a Airport kenan bai sake amfani da layin ba.

                 Abba bai samu ya koma a ranar ba Sai kashe gari, cike da gajiya da tashin hankali ya koma kano.

Wanda har ya kasa boye irin halin damuwar da yake ciki.

Mami kasa jurewa tayi lokacin da Abba yayi mata bayanin duk yadda akayi, kuka ta saka masa tana kiran.... Shikenan Abba na rasa d'ana shi ma....!kamar yadda na rasa kowa nawa... Rarrashin ta ya shiga yi yana nuna mata ba wai sun rasa mus"ab bane, suyi ta addu'a Allah zai bayyana shi.

Baby" ma ganin yadda Mami da Abba suke cikin damuwa ne yasa itama tashiga damuwa har da hawayen ta duk da idan dan ta ita ne mus"ab d'in ma Kar ya dawo saidai kuma ganin yadda Mami take ta kuka ne yasa ta ji tanason yin addu'ar Allah ya bayyana mus"ab, d'in a Karo na farko da taji zata iya masa addu'a tun farkon al'amarin.

*********
Wasa wasa karamar magana ta zama babba, babu Zaid babu salma" sosai hankalin Dad ya tashi, da wannan al'amarin, har yar rama saida yayi duk inda ya kamata ayi cigiya anyi amma ji kake shiru,

A bangaren Rahamu" tuni taron biki ya watse sai yan zuwa jaje.

Sosai ta tashi hankalin ta, a cewar ta watan tonon asirin ta ya tsaya, sosai tayi rama saboda wannan masifa, gashi abu a gun wanda addini ma bai dame shi ba, babu addu'a bare yadda da kaddara.

Abunda yafi damun ta shine tsayawar cikar burin ta.

A bangaren Ummi"sosai ta tashi hankalin ta kan cewa Rahamu"ce ta salwantar da Zaid d'in dan a cewar ta tun lokacin da aka soma zancen auren hankalin ta bai kwanta ba dan haka akama Rahamu ta bayyana inda takai Zaid d'in.

Saida iyayen ta suka nuna mata bacin ransu akan zancen kafun ta hakura ta shiga addu'ar Allah ya bayyana zaid d'in.

*******
Bangis kamar yadda ya fad'awa salma cikin daren ya shigo gun ta, haike mata yayi ya shiga yin yadda yaga dama da ita babu tausayi bare tausaya wa.

Saida ya tabbatar ya gajiyar da ita ta yadda ko d'an ya tsan ta bata iya daga wa kafun Sauka kan ta.

duban ta yayi a kaskance, yace wannan shine sakamakon raina mun hankali da kikayi, akwai saura kuma, wayar shi ya nuna mata duban ta takai kan wayar fuskar Zaid" ta gani a ciki gashi zaune duk bakin sa jini alamun yaci duka.

Kuka ta fashe da shi tana fad'in dan Allah bangis ka barmu mu tafi haka idan ni nayi maka laifi ai shi Zaid babu abunda yayi maka, dan Allah ka sake shi.

Wani mugun maka yakai wa bakin ta.

Au dama har haka kike son shi da har kike rokona in sake shi? lallai! to billahillazi kin koma janyo masa dan yanzun babu sassauci... bari indawo Zanzo kanki.

Ficewa yayi daga d'akin yana huci kamar wani kumurci.

Wani mugun kuka salma tasa tana dafe cikin ta dake mata mugun ciwo.

Zeema dake labe a kofar d'akin tana jin su, tana jin alamun fitowar bangis da sauri ta labe ta baya, le'kawa tayi taga ya shige cikin gidan, a sad'ad'e tabi bayan sa.

Wani gini taga ya nufa wanda yake incomplete, a hankali ta dinga bin bayan sa, har ya shige ginin.

a sad'ad'e ita ma ta shiga wani d'aki taga ya bud'e da key, ya shiga.

UMAIMAH! Where stories live. Discover now