31

1.5K 117 6
                                    

Aisha Abubakar, na manta daga wani group d'inne gaskiya amma ai kinsan kanki, anyway 😁kinyi ko'kari but still dai baki canka duka ba 🤣 so here is ur page 😍sauran da kukayi trying am great full😘🤗

Sosai yake kallon abun zuciyar sa na wani irin bugu, sake zazzage jakar yayi, wani fad'uwar gaba ne yasake ziyar tar sa.

A hankali ya sulale kasa yana mamaki Kodai idonsa ne?

Kayan Zaid"ne yagani wanda aka ajiye sa gidan marayu a lokacin yana jin jiri kayan da yake sanye da su ne, wanda mus"ab d'in yasan yana jin jiri yana da irin kayan saboda pictures d'in sa na jarin ta da yagani a lokacin tabbas yana da irin kayan shi ma.

Mai hakan yake nufi, diary d'in da yagani ne yasa yaja tunga gefe ya soma karantawa jikin sa na tsuma.

11/2/18.
Nasha yiwa kaina tambaya ni Zaid" Kodai ni d'in ba halastaccen d'a bane? Wanda kunyar abunda iyaye na suka aikata yasa suka jefar dani......

tiryan tiryan ya soma bin diary d'in, wani gurin yayi gumi da ajiyar zuciya wani gurin yayi hawaye, har yakawo haduwar UMAIMAH da Zaid d'in haka ya dinga bin labarin daki daki Sala Sala, sanka sanka.

....bai tashi daga inda yake ba saida ya ya karance sa tsab. wani irin gumi ne ya shiga wanke masa jiki, da uban tausayin Zaid d'in da UMAIMAH"wacce ko tantama ba yayi itace ummi UMMIN gidan su yar Abba da Mami.

to waye Zaid"?

d'an uwanka ne wanda babu tantama ciki d'aya kuka fito wata kila ku yan biyu ne wannan ne yasa aka kasa gane ba kai bane Zaid. to amma ai iyaye na basu taba fad'a mun cewa inada d'an uwa ba bare inji ta Yaya suka rasa d'an su.

Amma inason haduwa da Zaid" ya zama dole in had'u da Zaid" but how?

Zuciyar sa ta tambaye shi, numfashi ya sauke, dole ina bu'katar inje kano dan sanin halin da iyaye na suke ciki saidai kuma babu dama mai zance wa su dad idan zan tafi kano bayan bani da kowa Bana magana.

uppppss"i have to think about it.

********
a hankali Zaid yake samun lafiya, wanda sosai hakan yake faranta ran iyayen sa, ga wata irin natsuwa da suke gani tattare da d'an nasu wanda hakan yake sake saka su farinciki.

a bangaren UMAIMAH" ma sosai abun yake bata mamaki. ganin wani irin kulawa da yake bata, haka kuma ko batazo asibtin ba shi zai neme ta dole Mami ta turo ta, sosai take mamakin sauya war sa lokaci d'aya.

Zaid"kam lafiya kawai yake jira ya samu ya bayyanar musu da gskiyar shi ba d'an su bane, dan sosai yake mamakin da suka kasa gane cewa shifa ba d'an su bane, har mamakin wannan kamar yakeyi yana matu'kar mamakin wannan wace irin kama yake da d'an su har haka?

Shikam jira yake ya warke ya fad'a musu gaskiya, daga bisani ya bayyanar da iyayen UMAIMAH" a gurin su, su karbi yar su, ko ba komai yayi farinciki sosai da ganin irin hannun da UMAIMAH" take. Kuma yana ji a jikin sa dole d'an su ya sake ta ya aure a barshi dan UMAIMAH tasa ce shi shi kad'ai!

Yau ma yana kwance kan gadon sa na asibiti kasancewar har yanzun ba'a sallame shi ba.

Baby" tayi sallama had'i da shigowa, matsawa tayi ta ajiye basket d'in dake hannun ta.

Kusa da shi ta ja kujera ta zauna, sai binta da ido yake,

Ina yini?
Yaji sassanyar muryar ta tana gaishe shi.

Murmushi ya sakar mata had'i da lumshe kyawawan idanun sa, daga bisani yace..

Ykk?

A kasalance ta amsa da,

"lafiya

Ko zaka ci abinci yanzun?

Idan Kinga ya kamata na ci ai sai inci,

UMAIMAH! Where stories live. Discover now