24

1.2K 101 9
                                    

A razane, ta farka.. haske taga gari yayi, tashi tayi.

bed d'in musab ta duba gani tayi babu kowa a Kai.

da sauri ta fita daga d'akin, tana shiga d'akin ta, ta fad'a toilet ta d'aura alwala.

Sallah tayi bayan ta gama tayi shiru kan sallaya, tana nazarin rayuwar ta da mus"ab.

A da kullum so take bacci ya d'auke ta dan tayi mafarki da shi saidai yanzun yadda yake nuna mata halin mugunta yasa Sam ta tsane shi, dan shi d'in mugu ne, hawaye ne suka sauko mata, cinyar ta,
ta bud'e tana kallon yadda gurin ya caccabe,

   Sai sulili yake mata, turo kofar d'akin yayi, kallo d'aya tayi masa ta d'auke kanta,

Shi d'in ma harar ta yayi, baice mata komai ba ya miko mata waya, yana mai yi mata gargadi da ido,  akan karta yadda tayi wani abu da zaisa a gane bata jin dad'in zama da shi.

a kasalance ta karba wayar, karawa tayi a kunne,

Hello"

Ta fad'a cikin muryar ta mai nuna sanyin ta.

UMMIN Mami" ykk?

Cikin murna da jin muryar mamin ta ce..

Mamina, ina lafiya sai kewar ki, ta karasa fad'a kamar zatayi kuka.

Ayya ummi garki damu, insha'Allah ai kunkusa dawowa, zaki ganni. Ince dai yayan naki baya takura ki?

Kallon shi tayi... Shi d'in ma kallon ta yayi dan wayar tana hands free ne.

Mami ce tace hello ummi"kina Jina?

.... A a....a Mami inajin ki, ta amsa a daburce.

Nace babu dai wata matsala ko?

A a Mami babu, to shikenan Allah yayi miki albarka.

Amin Mami, kina maida hankali a karatun naki ko? Eh Mami.

To shikenan sai anjima.... Mami!

Ta dakatar da ita...

Shiru mamin tayi daga bisani tace ina jin ki.

Mami"nidai inason zan dawowa gurin ki.

ayya Babyna,, garki damu zaki dawo very soon, kinji?
Gyda Kai tayi kamar mamin tana ganin ta, dariya Mami tayi tace baki amsa ba.

A sanyaye tace, OK Mami... I love you!

Love u more.... Silly girl....

Mami tafad'a tana dariya, had'i da kashe wayar,

hannun ta na rawa ta mika masa wayar, amsa yayi yana duban fuskarta da hawaye suka gama wanke wa,

A hankali yakai hannun sa zai share mata hawayen, da sauri taja baya tana fashewa da kuka, a lokaci d'aya kuma tana cewa.

Dan Allah kayi ha'kuri bazan Kara yin kukan ba,, ka gani ma,.na daina.

tafad'a tana gogge hawayen ta.

Shiru yayi, Yna kallon ta duk sai yaji wani iri, ganin yadda duk tayi wani iri jikin ta sai rawa yake,, shiru yayi thinking.... so is that how wicked I am!

fita yayi daga d'akin zuciyar sa babu dad'i.

Ummi yana fita takoma ta zauna tana ta faman sheshekar kuka.

******
What's wrong with me..Sam da ba haka nake ba!

Mai yasa yanzun nake son komawa wani abu daban gashi yanzun yarinyar nan har ta fara tsorata dani kamar wani dodo.

UMAIMAH! Where stories live. Discover now