26

1.4K 131 23
                                    

Mami" ce ke ta faman kiran wayar Mus"ab saidai abun haushin tun d'azu abu d'aya ake fad'a mata shine a kashe wayar ta ke.

          Hmmmmmm! ta sauke numfashi, cikin 'kosawa da tunanin ko lafiya? baby dake zaune kusa da ita duban ta tayi, saidai bata iya tace komai ba, tadai fahimci layin Mus"ab take kira kuma ga dukkan alamu baya tafiya, a ranta cewa tayi Allah yasa ma Kar ya dawo!

             Mami" kallon baby tayi... Ummi" wai kin kuwa gwada kiran yayan naki?
Shiru tayi daga bisani ta ce a a Mami, saboda Sam bata iya karya ba shi yasa ta fad'a wa mamin gaskiya.

Shiru Mami tayi tana duban ta,  har saida babyn ta tsalgu da irin kallon da mamin take ma ta.

  Ummi" tunda ya tafi kunyi waya ma kuwa?

a sanyaye tace a a Mami.

Wani irin abu ne ya darsu a zuciyar mamin, saidai kuma bata da hujja ko dalili to kuma Kar yaran nan su maida su kananun mutane mana.

  Amma ko ma dai Menene, idan Mus"ab d'in yadawo, za ta saka musu ido.

*************
Hajiya azumi" a duniya ke kad'ai ce masoyiya ta Sam bani da kamar ki, kinyi mun halarci, naso ace yaya na ke ce wacce ya aura amma ya Je ya auro dangin mayu,

  Hajiya Jamil ce mai wannan zancen tana dafe da ka fad'ar hajiya azumin,

Murmushi hajiya azumi tayi,  haba Jamila ai ni dake d'aya ne garki manta da mahaifiya ta da mahaifin ki uwa d'aya uba d'aya ai ta wuce wasa..... Abunda nake so kawai ki gane nidai mai kaunar ki ce.

Lemo hajiya Jamila ta kai bakin ta... Saida ta zuka da kyau, kafun ta sauke cup d'in daga bakin ta.

    Aminiya ta, ga Mus"ab a hannu kuma kawar da shi zamuyi, dan haka meye next target?

garki damu Kawa ta, Adai kaddamar wa magajin, domin idan kanason cin dukiya da kyau, to ka kaddamar wa da magajin ta wanda ya mallake ta kawar dashi bazai yi wuya ba.

Hhhhhhaaahhhhaa, kai kawata kuma zancen ki dutse,.

Wani gyada Kai azumi tayi, tana jin kanta ita ga boss, a ranta tana saka yadda zata ci wa Jamila Amana!

******
Wai salma" dun ubanki ba nace ki kira Zaid" ba?  Mommy wlh na kira shi amma a kashe ake cewa tun d'azu.

         a birkice hajiya Rahamu"ta je d'akin ta inda Kawayen ta suke cike, wayar ta ta shiga nema,

Garden d'in gidan ta zagaya, kiran wayar Zaid" tayi a kashe dai,

Shiru tayi gaban ta na tsananta fad'uwa, wata shawara ce ta zo mata.

Da sauri ta danna layin bokan ta, yana d'auka ta soma masa bayani Zaid" tun bayan awa uku dagann yaje ya d'auko friends d'in sa shiru har yanzun bai dawo ba. Itafa tana tsoron kar ya gudu ya tona mata asiri.

           kashe wayar boka yayi bayan yace da ita ta da kace shi. Shiru tayi tana jiran kiran boka, tsawon mintina talatin.

   Yana kira da sauri ta daga jiki na rawa.

Boka ne yashiga yi mata bayani,

Rahamu"ki kwantar da hankalin ki babu inda Zaid" ya gudu, yana nan saidai banga mai ya hana shi dawowa ba.. dan haka Kuci gaba da shagali ko ranar d'aurin aure ne kiyi ko'karin ganin an d'aura auren ko baya nan!

Murya na rawa Rahamu" ta shiga cewa boka kenan zai iya kai wa ranar d'aurin auren bai dawo ba? 

bance ba! saidai kiyi amfani da abun na fad'a miki.....!

yana kaiwa nan ya katse wayar.

Jugumm! Rahamu tayi,, daga bisani ta ja jiki zuwa jikin gidan, tana kokarin danne damuwar ta.

UMAIMAH! Where stories live. Discover now