32

1.5K 152 26
                                    

For u, kawaye na abokan rigima ta kawayen Rahamu 🤣Mum nadeer😍Mrs Mahmoud 😘Eashert Mustapha 😍, Allah ya raya zuri'a yabar zumunci 🤗😍

Ammi"na bonu ammi anya mus"ab ba guje mun yayi ba? Kamar sauran samari na na baya.    ta fad'a hakan tana mai fashewa da kuka. kafadar ta uwar ta dafa.

SIDEEFA" ina ji a jikina mus"ab tsakani da Allah yake sonki, musamman idan kikayi duba da irin hidimar da yake da ke ga tarin kulawa, wanda ke kanki kinsan a kaff samarin da sukayi sonki babu kamar mus"ab, dan haka ni ina ganin addu'a zamuyi Allah idan da alkhairee Allah ya dawo da shi gare ki kuma Allah yasa ma dai yana lafiya.

Ammi" kina gani jarabawa zanyi amma dole saina biya mus"ab shine kawai wanda nake tunanin zai biya mun shine wanda zai d'auka nauyi na ba tare da gajiya wa ba, saidai Ammi lokaci d'aya ace na kira shi amma babu amsa hasalima wayar bata zuwa. Ammi ina tsoro idan Shima ba iyayen sa bane suka ce bazai aure ni ba banda ubangiji kamar sauran masu zuwa kwana biyu su gudu. Ammi"wlh hankali na bazai taba kwanciya ba ina matu'kar son mus"ab.

mus"ab bugun zuciya ta ne, Ammi"wlh kirjina zafi, ta karasa fad'a tana dafe saitin zuciyar ta, sai wani irin wahalallen kuka take.

Rungume ta Ammi tayi a jikin ta tana mai tsananin tausayin yar ta, mus"ab namiji ne da duk yar da tara sa shi zata iya zubar da hawayen ta a kansa.uwa uba gashi da tausayi.... wanda shine silar soyayyar sa da sideefa.

  Ci gaba tayi da rarrashin yar ta.

********
A gaskiya ina da jan aiki a gabana dan matar nan Sam naga alamar da gaske takeyi.

Mus"ab ne mai wannan tunanin, a daki sai zagaye yake, kwakwasar da ake ce tasa ya bud'e kofar mai aikin Rahamu ce, na kurmaye tai masa hajiya tana son ganin ka a sashen ta, gyda mata kai yayi.

Kafun yayi gaba, d'an jin gina Laure tayi tace ohhh ko ta Yaya zan sanar dashi kar yaci abincin da hajiya zata bashi?

Karaf!...a kinnin mus"ab.

Yace au"wani kulli tayi kenan?

Kamar Kar yaje sai kuma ya fasa kawai sai ya nufa apartment d'in kai tsaye.

A sanyaye Laure ta bi bayan sa tana ta saka yadda zata taimake shi.

Yana shiga ya zauna kan d'aya daga cikin kujerun parln.

Kamar ko yaushe cikin izza da isa ta fito, tana faman tazgar kai.

Karewa Zaid kallo tayi bayan ta zauna, zama na irin nida parlour na,

Wasu takardu ta mika masa,

Amsa yayi gaban sa na duka.

Alamu tai masa na kurame tana magana, irin wannan takardun zaka d'auko min a safe d'in Alhaji.

Gaban sa ne ya fad'i, saidai bai ce mata komai ba hka kuma bai mata alamar komai ba.

Laure... Laure " ta shiga kwalawa mai aikin ta kira, sai ga Laure da hanzarin ta.

Ga...ni hajiya.

Ki kawo abinci, to tace, jikin ta a sanyaye ta d'auko ta kawo gaban mus"ab ta a jiye.

Rahamu" da kanta ta zuzzuba masa had'i da mika masa.

Karba yayi, ya kurawa abincin ido, tana zama ya bita ya mika mata abincin kallon sa tayi had'i da murmushi, tace ka ci mana, tana yi tana kwatanta maganar ta da hannu.

      Spoon d'in ya d'auka ya debo abincin ya nufa bakin ta da shi, girgiza Kai ta shiga yi tana cewa Kai nifa bazan ci ba naka ne kai kad'ai jeka jeka ka ci, tana maganar tana ja baya, shi kuwa dariya yayi tamkar wani zararre, yashiga ko'karin dura mata abincin gadan2, ihu Rahamu" tasa

UMAIMAH! Where stories live. Discover now