25

1.4K 187 16
                                    

For u my kawar arziqi Asma'u Adili (maman Ramadan) 😘our friendship means a lot to me🙌🏻😘🙌🏻 Thank you so much for spporting me💋

Koda bai taba kasance wa da mace ba, yasha krantawa a English novels, da sauran littafan da kan iya bayya na yadda mace virgin zata iya kasancewa.

          shiru yayi na yan seconds, daga bisani ya Sauka daga kanta, ransa na tsananin 'baci,

toilet d'in ta ya fad'a tsarkake jikin sa yayi yana fitowa ya d'auka wandon pyjams d'insa ya saka, har lokacin baby kuka take a cikin bed cover da taja ta rufe jikin ta.

      Saida ya Kalle ta na yan dakiku ransa na baci a kanta kafun yafita daga d'akin.

Baby najin fitar sa, tashi tayi daga bed d'in, toilet ta shiga tana ci gaba da kuka.

Mus"ab, Koda yakoma d'akin sa, kasa bacci yayi yashiga tunani....

Yanzun wannan yar yarinyar har tasan namiji?

dama yar iska ce ta yau dari iyayen sa da aljanu ta aureshi, to ko tad'auka shi wawa ne bazai gane ba?
                           Ai Koda yake jin sha'awar ta dole yana son abu Nagar tacce inda zaiyi foundation da kansa ba wai ya hau gini kan foundation d'in wani ba.

Kodai ya fad'a wa su Abba"  ne?

To mai zance musu? watakila kuma aljanu ne sukayi amfani da ita.......... Kai..... Aljanu?

Haka Mus"ab ya dinga sake2 a ransa game da al'amarin UMAIMAH.

A ranar dai sai bacci barawo ne ya sace ta.

A bangaren baby" sosai tasha kuka akan abunda yafaru tsakanin ta da Mus"ab.

*****
Rana bata 'karya saidai uwar diya taji kunya.

A yau ne Zaid yake kammala karatun sa a jami'ar Abuja.

Sosai yayi farinciki da wannan ranar na cikar d'aya daga cikin burikan sa, saidai a wani bangaren na ransa yanajin babu dad'i, wanda hakan baya rasa nasaba da rashin baby a tare dashi.

Ummi" ma tazo tundaga Niger domin taya shi murna.

Rahamu" kallon su kawai takeyi dan kuwa itama a nata bangaren tana ta shirin ta.

Saida aka kwana biyu da gama karatun Zaid,

Rahamu ta same shi a d'aki, duban ta yayi lokacin da ta shiga d'akin.

Zaid"ina fatan kana sane da abunda yake gaban ka,?

Kirjin sa ne ya buga, ransa babu dad'i ya amsa da...

Eh ina sane.

Murmushi tayi kafun tace..

to yaushe kake ganin ya kamata a soma shiri?

tamkar wanda ake turawa yayi magana dole, yashiga cewa...

Mommy ai ko yaushe kika tashi ayi kawai ko yau ne ma,

Yaudararren Murmushi tayi, haba dai d'an mommy? Sai kace abun gudu inaga kawai za'ayi shi nan da sati uku masu zuwa.

to mommy hakan ma yayi,

Yawwa zanyi magana da Alhajin.

daga haka ta fita daga d'akin.

Zaid sauke ajiyar zuciya yayi, daga hannuwan sa yayi zuwa sama.

Y"Allah ka kowo mun d'auki a cikin wannan al'amarin da yake faruwa dani,

Shiru yayi yana ci gaba da addu'a a zuciyarsa, dan harga Allah ransa baya masa dad'i yadda yake ko'karin bin umarnin matar sau da 'kafa.

UMAIMAH! Where stories live. Discover now