MABUƊI

9.5K 559 40
                                    

FIKRA WRITERS ASSOCIATION

TAZARAR DA KE TSAKANINMU🤦🏼‍♂🤦🏿‍♀

✍🏾KHADIJA SIDI & SAFIYYAH UMMU-ABDOUL

MABUƊI

Kashim Ibrahim library (KIL) babban ɗakin karatu ne cikin Jami'ar Ahmadu Bello da ke birnin Zariya. Kamar kullum yauma ɗakin karatun cike ya ke fal da ɗalibai maza da mata kasancewar lokacin jarabawar zango na farko na shekarar (first semester) ya matso. Ɓangaren da ta san ya fi kowanne rashin hayaniya ta samu ta raɓe. Sanye ta ke cikin shuɗin hijab dogo har kasa. Sam ba ta damu da ta shafa ko hoda ba bare a kai ga jambaki, irin bakaken matan nan ne da su ka amsa sunan "black beauty". Duk yadda ta so ta mayar da hankali ta gane karatun da ke gaban ta, hakan ya gagara ba dan komai ba sai dan zaman da wani ya yi kusa da ita. Zuwan ta be fi da awa daya ba sai gashi shi ma ya zo, kuma ya rasa in da zai zauna sai kusa da ita duk girman library din, mitar da ta ke yi cikin ran ta kenan tana mai jan tsaki ɗaya na bi ma ɗaya.
Tana cikin wannan halin ne ta ji kamar an gogi kafar ta wanda hakan ya sa ta saurin janye kafar da sauri, a fusace cike da alamar tambaya ta kai kallan ta gare shi. Tsintar idanun ta cikin na sa ya tabbatar mata da ya na sane ya sanya kafarsa ta gogi na shi, ko shakka babu irin 'yan iskan mazan nan ne ma su yiwa mata goge, da be sami dama ba shi ne ya ke bin ta da kafa.
Kallan da ta ke masa ne ya sanya shi janye tashi kafar da sauri tare da faɗin
"Sorry Mama na! ..."

Maimakon ta ji sanyi cikin ran ta,  sai ma daɗa tunzurata da yayi, wato yana nufin bai ma san kafar sa na gogan na ta ba ne, ko tsabagen shaiɗana ne da zai wani kira ta da "Mama na" tunda ya sami kafar tsohuwarsa ai dole ya goga. Take ta ji karatun ma ya fita daga ran ta, cikin zafin nama ta haɗa ya nata ya nata, har ta na bugewa da tebur tsabagen ɓacin rai ko gaban ta ba ta gani da sosai.
Fuuu ta fice a fusace. Kai tsaye Queen Amina Hall ta nufa inda nan ya kasance hostel ɗin da take.
Da ke bayan isha'i ne, ɗalibai samari da yan mata wanda su ka sha karatu da wanda ba ma su sha ba duk sun taru mararrabar hostel sai cafta ake. Sam ba ta kula da su ba, bare ta damu da sheƙe ayar wasu daga cikinsu ke yi na rungume rungume da shafe-shafe da ta ke jin labarin wasu kan yi, kan ta a kasa ta ke gifta su, zuciyarta na mata tuƙuƙi don gaba ɗaya niyyarta ta shanye handout biyu na course din da za su yi jarrabawa ta gaba. Daf da za ta shiga hostel din ta ji an tab'o kafadar ta,  tsayawa ta yi cak kafin ta jiyo a hankali saboda jin da ta yi hannun namiji ne mai taɓo ta, wa za ta gani? Wannan mutumin nan ne dai ya biyo ta, har ya iya daga hannun sa ya taba ta cikin mutane......ji ka ke tas!!! Hannu ta sa ta dauke shi da marin da sai ya ga wuta a idon sa ba tayi tunani kafin aiwatarwa ba don gaba ɗaya ji ta yi banda cin mutuncin matatantaka da yayi har da musulunci da hijabin da ke jikinta ya ci wa mutunci.
Gaba ɗaya hankalin jama'ar wajen ya dawo kansu,  hasken lantarkin da ke ci a wajen kamar an ƙara masa haske don ya sadar da abin da ta aikata ga bawan Allahn nan. Jikin kowa yayi sanyin ganin wanda ke tsaye gaban ta hannun sa bisa kunci, bai yi zaton haka daga gareta ba hakan ya sanya marin zuwa masa a matsayin ba zata kamar yadda ya zo masu a hakan. Sanannan saurayi ne cikin Jami'ar wanda hatta wanda su ka shigo Jami'ar a wannan shekarar sun san da zamansa saboda shuhura.
Ga mamakin kowa har ita mai marin wacce ta yi mutuwar tsaye ba tare da ta yi Dana sanin marin da ta yi ba, don tsayuwar da tayi jira ta ke kome ma zai faru ya faru don kwatakwata babu nadama ko karaya a tare da ita, sai gani kawai ta yi ya mika mata abu, ko da ta ware ido da kyau ta dubi abin da ya ke miko mata sam bata gaskata ba, a hankali ta mayar da kallan ta ga fuskar shi wanda ke dauke da murmushin da ya sanya kwarjini da kyawun fuskarsa bayyana, cikin nuna halin ko in kula da marin da ya sha ya furta
"Ga shi, wayar ki ne da ki ka manta..."
Hannun ta na rawa ta karɓa ba tare da saurari cigaban abin da yake shirin faɗi ba. Ta na karba ya juya, cike da takama da ko in kula ya ke tafiya yayinda ta bi bayan sa da kallo, shin wannan waye shi?
"Ya Allahu ka rufa min asiri ni Amatullah..."
Cewarta, a hankali ta juya ita ma cikin sauri ta na harhaɗa kafafu, daliban da ke gurin nan su ke ta cece ku ce akan abin da ya faru gaban su, daga masu ba ta kyauta ba, sai masu da su ne sai sun tattaka ta, sai masu Allah shi Kara

" Toh ai shi Dee Yusuf ya ɗauka kowacce mace ce ta rako mata, wallahi ta burge ni da ta kwashe shi da mari" ta ji wasu na faɗi daga bayanta.
"Dee Yusuf!" ta so ta sake faɗi amma ina, zancen zucin da ta ke ya sa ta dena ji yadda ya kamata, kwakwalwarta ta dena sawwara mata daidai har ta isa ɗakin kwananta da ke gini na takwas ɗaki na goma sha biyu (block 8 room 12).

***

Littafanta kawai ta ajiye saman gadonta, buta ta ɗauka ta fice ba tare da ta ce da Ahalin ɗakin uffan ba, kama ruwa ta je tayi sannan ta yi alwala, ɗakin ta koma ta gabatar da wutiri, sai a lokacin ta samu ɗan natsuwa, duk da haka ba ta motsa daga saman dardumarta ba, sam bata lura da kallon da kawarta ke mata ba.
"Amatullah! Amatullah!! Amatullah!!!" sai a kira na uku ta ji ko dan ƙawar ta ɗaga muryarta ne ba ta sani ba.
"Zulaikha sai ki firgita mai rai wallahi, ji tsawar da kika min" ta karasa tana mai jan gajeruwar tsaki, mamaki a karo na biyu ya sake kama Zulaikha saboda ta tsaki na ɗaya daga cikin ɗabi'un da Amatullah ta tsana.
Tashi tayi ta ninke dardumarta, sannan ta haye gadonta da ke saman na zulaikha ba tare da ta ce da ita da ke jiran bayani komi ba.
Ɗauko takardunta tayi don ta cigaba da dubawa amma ina babu abin da ke shiga, ga shi jarrabawar da za su yi gobe na physics department ne da duk wani mai karanta abin da ya jibinci kimiyya da ke aji ɗaya a jamiar yake yinsa, sannan adadin wainda ke maimaita jarrabawar kan fi rabin adadin masu rubutawa a karo na farko, saboda haka dukkan su ke tsorace da darasin.
"Zulaikha na sadaƙar kawai zan sake physics dinnan" tace cikin karyewar zuciya.
"Allahumma Ajirna" Zulaikha tace iya karfinta.
"Kin shigo kafin lokacin da kika ɗibar ma kanki, kin shigo a firgice kin yi gamo ne?" Zulaikha tace tana shafa hannunta cikin sigar lallashi.
"Marin wani Yusuf Dee yake ko wa nayi fa anan gaban Amina" tace iya gaskiyarta, yayin da Zulaikha ke hango kwantacciyar firgici a idon ƙawarta. Ba Ta dena shafa hannunta ba, ba ta ce komi ba kuma, so take ta tuna in da ta san sunan Yusuf Dee din, kamar wacce a ka raɗawa ta tuna.
"Wai Dee Yusuf kika mara? Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun, me ya kai ki Amatullah?" ta haɗa duka ta faɗa mata ba tare da ta jira amsar cewa shi ɗin ta mara ko wani ba.
Hawayen da ta ga Amatullah na fitarwa ya kara tsinka mata zuciya. Zikiri take a hankali duk wanda ya zo bakinta, yayin da Zulaikha ta haura saman gadon tana lallashinta.
"Kinga ba wani abin damuwa bane, Shine Sec Gen na SRC (Student Representative Council) Watau shugabanin ɗalibai masu wakiltar sauran ɗalibai, kuma shine in charge of student affairs department.
Wasu sun ce bafullatani ne wasu sun ce babur amma kin tuna Halima ta statistics kin san yar Margi ce, toh ita na ji tana faɗin ɗan garin su, kin san yadda ake rububinsa hakan ya sanya masa girman kai, kuma Kinga kudin SRC na ɗiban su, amma ina jin kamar faculty of medicine yake na ji dai ana fadin first class guy ne, yana dai da yan kora ni shi ne kawai tsoro na amma banda haka bana jin komi" Zulaikha ta ƙarasa cikin tabbatar da abin da ta ke fadi. Kallon ta Amatullah take cike da mamaki, ta san ajinsu ɗaya, kawarta ce, tare su ke komi a ina ta san duk waɗannan bayanan da ita ba ta taɓa sani ba, ƙarshenta ma za ta iya rantsewa ba ta taɓa ganin wani halitta irin ta wanda ake kira da Dee Yusuf ɗin ba.

TAZARAR DA KE TSAKANINMUWhere stories live. Discover now