BABI NA GOMA SHA BIYAR

2.9K 329 46
                                    

FIKRA WRITERS ASSOCIATION
TAZARAR DA KE TSAKANINMU 🤦🏼‍♂🤦🏿‍♀

✍🏾KHADIJA SIDI & SAFIYYAH UMMU-ABDOUL

    BABI NA  GOMA SHA  BIYAR

Allah ya kai su Dee Yola lafiya, kasancewar da daddare su ka isa, Nan family house din mamacin aka sauka, in da su ka tarar da yan uwa da abokan arziki suna tsimayin isowar na su. Tun a daren ranar Dee da ƴan uwan mamacin su ka fara shirye-shirye bikin birne gawar, wanda za a yi nan da kwana goma sha biyu zuwa sha uku. Kamar yanda kwanaki su ka yiwa Dee tsawo, haka su  yi ma Amatullah, kwana bakwai da aka ba su hutun midsemester ɗin ya zame  mu su kamar shekara bakwai, a ɓangaran Dee; rashin Amatullah da mijin Mahaifiyar ta shi ba karamin karamin girgiza shi ya yi ba, gashi shirye shiryen birne gawar kaɗai ya isa ya gajiyar da ɗan adam. A ce an rasa mutum amma sai an yi gagarumin biki ranar da za a rufe shi? Shi kam Dee wannan na ɗaya daga cikin al'adar kiristanci da sam bai ma sa ba.

Amatullah kuwa a nata ɓangaran yanda matan gidan kan kira ta da Amarya duk da tana hango isgilanci a sautinsu yayin da su ke ambato mata wannan sunan ya hana ta sukuni, Ba wai isgilancin ke ƙona mata rai ba, jin da take hakan kamar danganta ta da saif ne ya fi komi ɓata mata rai.

Angon na ta kuwa tun da ya sa kafa ya tafi babu wanda ya sake jin ɗuriyar shi, hatta Baba Anas yayi kokarin samun shi a waya, amma abin ya gagara, shi kuma bai kira ya shaida mu su isar sa Russia ba.

Ranar Laraba da safe ta tashi da matsanancin tsanar gidan, tunanin wajen zuwa ta ke yi don ta samu sauyin iska.

"Zulaikha"

Kawai taji ɓarin zuciyarta ta ambato mata hakan ya sanya ta sakin murmushi.

Kamar yadda ya ke al'ada garesu gaida iyayensu bayan sun idar da azkar hakan ta tashi ta yi, haka kuma kamar yadda mahaifiyarta ta umurce ta duk ta shiga ɗakin Hajiya ta kan ɗan ɓata lokaci, don ko jiya sai da ta kama mata ninkin kaya sannan ta fito.

Cikin sa'a ta samu Baba Anas zaune yana sauraron sashin hausa na radiyon BBC, gaishe su tayi a ladabce sannan ta yi shiru tana ƙara sunkuyar da kai.

"Ƴar Baba Anas da magana a bakin nan"

Baba Anas ya ce cikin sakin murmushi. Ƙara sunkuyar da kai ta yi. Harara Hajiya ke watsa mata tana zagin ta a zuciya, ita da Amatullah za ta hakura da shigowa ɗakin ta da ya fiye mata komai.

"Ehmm! Amatullah Ina saurarenki" ya ce yana mai rage sautin radiyon sa don ya ji me take tafe da shi.

"Baba don Allah izininka nake nema, ina son in duba ƙawata Zulaikha" tace gaban ta na faɗuwa, tsoro bai sake cika ta ba sai da ta ɗan ɗaga kai ta kallo sashin Hajiya ta ga harar da ta watso mata, ta ke ta shiga da na sanin tambaya tun farko. Gani ta yi shine mahaifin mijinta a tunanin ta zai iya bata izini makwafin mijin nata.

"Allah ya dawo da ke lafiya, kar dai ki kai almuru a waje" yace yana murmushi.

"Na gode Allah ya kara girma da lafiya" ta ce cikin farin ciki.

"Aameen Ƴar Baba" yace Shima cikin farin ciki.

Da haka ta tafi ɗakin mahaifiyarta cikin farin ciki, jinta take zaman ta a gidan Jamoh kamar wacce ke zaune a gidan maza.

Da wannan farin cikin ta iske mahaifiyarta ta faɗi mata yanda su ka yi da Baba Anas, tana kallon yadda murmushin fuskar mahaifiyarta ya ke dusashewa a hankali.

"Yanzu ke sai ki ɗauki jiki ki fita tsigau tsigau se kace wacce ba ta da mafaɗa, ko da can kan ki yi aure haka kike fita kamar baƙar Leda balle yanzu da aure ke kanki? Mijinki kawai zai baki izini in bari ki fita, sakarai mara kishin kai" Gwaggo ta faɗi tana tashi daga wajen.

TAZARAR DA KE TSAKANINMUWhere stories live. Discover now