BABI NA GOMA SHA TAKWAS

2.8K 345 102
                                    

TAZARAR DA KE TSAKANINMU 🤦🏼‍♂🤦🏿‍♀

✍🏾KHADIJA SIDI & SAFIYYAH UMMU-ABDOUL

    BABI NA  GOMA SHA  TAKWAS

Ganin Dee da ta yi ba ƙaramin fama mata gyambo ta yi ba, haka ta maƙale a ɗakinsu ba tare da ta fito ba don gaba ɗaya ta rasa gane kanta. Ko ɗakin Baban Sasa ba ta shiga ba, haka ɗakin Hajiya iyaka wainda ta ci karo da su kafin ta shige su ne su ka san da dawowarta.
A nan tsakar gida Hajiya ta tsinci labarin dawowarta, duk da ba lale tayi da dawowarta ba sai ta tsinci zuciyarta da yi mata ƙuna akan rashin shigowar ta gaisheta.

***

Angon Amatullah wato Saifullah kuwa  bai so dawowa Nijeriya ba duk da kuwa ya kammala karatun shi sakamako kawai ya ke tsimayi. Ayush ce ta takura lallai su dawo a yi maganar auren su a wuce wajen. Gashi har yanzu ya kasa buɗa baki ya faɗa mata halin da ake ciki na game da auren shi da Amatulah, ya so ya hure mata kunne su yi zaman su can su nemi aikin yi ko da kuwa na shekara guda ne amma Ayush ta yi kememe ta ki, ita aure ta ke so, in kuma auren na ta ne ba zai yi ba sai ya faɗa mata. Akan wannan batu su ka dawo gida, in da Saifullahi ke cikin halin haula'i.

Bayan Sallar isha'i Saifullah ya shigo ɗakin mahaifiyar tasa, so yake ya nemi shawararta akan yanda zai faɗi ma Ayush ba tare da ya rasata ba sanin da yayi in dai wannan fannin ne Hajiyarsa ba ta da part two.

"Ka haɗu da yarinyar nan ne?"

Ta tambaye shi, yanayin da ya kallo ta cikin rashin fahimta ya sa ta ƙara da
"Amatullah fa" tace tana kallon sa.

Tsoro take kar ya zo ya faɗa tarkon son yarinyar don ta san kwana bakwai Baban Sasa da Baba Anas su ka ɗauka suna addu'ar gina soyayya tsakanin wa'inda ke samun saɓani.

Sannan ta yarda da ƙarfin addu'ar don tana yi a duk lokacin da su ka samu saɓani da megidanta.

"Ni wallahi gaba ɗaya na manta da wata halitta haka, ni yanzu mafita na zo ki sama min, Ayush! Ban son na rasa ta Hajiya" ya ƙarasa yana marairaicewa. Shiru ta yi tana tunani kafin ta samu mafitar da cikin farin ciki ya bar ɗakin tare da niyyar ɗaukan hanyar Kano Washegari.

"Ka nemi yarinyar can dai komi dare yau, na san yan sa ido sun fi ɗaurawa a kanka" ya tsinkayi muryar hajiya sa'ilin da ya ke barin ɗakin.

Ficewa yayi yana tunanin yanda zai yi da ita, ji yake ina ma kashe rai ya halatta a duniya da tuni ya aika ta lahira don ya ji dadin rayuwarsa da Ayush.

Har ya zo wucewa ya ga Siddiƙa kanwar Amatullah za ta shiga ɗakinsu.
"Uhmmmn wacece nan" yace cikin ɗan ɗaga murya.

"Siddiƙa ce" ta faɗi tana ɗan tsayawa.
Sai ta ya matso kusa da ita sannan yace
"ki ce ma Amat ta kawo min abinci ɗaki" yana gama faɗi ya sa kai ya fice.

Da murna ta shiga ɗakin lokacin Amatullah na zaune suna hira da mahaifiyarsu wanda rabi da rabi ne hankalinta a wajen.

"Yaya Amatullah wai ki kai ma Yaya Saifullah abincinsa ɗaki, kin ji yanda ya kira sunanki, Aamat ya ce, wallahi Yaya Saifullah ɗan gayu ne..."

"Dilla rufe ma mutane baki, ba ɗan gayu kaɗai ba" Amatullah ta katse ta cikin tsawa, ba ta ga dalilin da zai sa ya nemi ta kai masa abinci ba.

'Zai so ki fa, kuma ki saki jiki ki sabar masa da jikinki, da farko a kwai wuya amma shine soyayya' ta tuna kalaman maman Jaafar. Nan sai ta ji sanyin jiki.
Kenan har ya fara sonta tun da har ya nemi ta kai masa abinci.

'da farko a kwai wuya'
ya sake faɗo mata a rai, nan ta tsorata ainun don in akwai abin da ta tsana abin da zai sa ta ji zafi a jikinta. Ta tuna a littafan da ta karanta yanda aka sa amare na sumewa in aka kai su. Ba ta san lokacin da hawaye su ka soma gangaro mata ba, kawai ɗuminsu ta ji.

"Amatullah haramun ne tsaurara kiyayya, balle wannan mijinki ne wanda Aljannarki ke tafin ƙafarsa. Ga abincin sa can maza ɗauka ki kai masa" Goggo mairo ta faɗi bayan ta sa hannu ta goge mata hawayen. Cikin sanyin jiki ta ɗauki abincin ta kai masa ɗaki.

Film yake kallo ƴar America, ganin ta bai sa ya kashe ba duk da kuwa abin da ake haskowa ya saɓa ma shari'a. Duƙar da kai tayi don tun da take abin da bata taɓa gani ba kenan.
"Daga kai ki gani, ki ga yanda su ka dace da juna, shin ni ɗin ya dace na gauraye gumi da bagidajiya irinki? Kalle su fa, wai ke har kina tunanin kin kai mace da za a gani a so?
Na so tsine ma ranar da aka ɗau cikinki don ranar bai zama mai adalci a rayuwata ba"

yace yana mai jan farantin da ta shigo da shi ya soma cin abincin da hankali kwance.

"Hijabin nan naki ƙarni ya ke yi, ki yi hakuri ki bani waje ko iskan zai yi daɗi" ya ce yana nuna mata hanyar fita.

Tsoro ya hana mata fita tun a farko, don ta san yana iya ƙulla mata wani sharrin, ga shi ta zauna, amma zaman bai mata amfani ba.

Kuka ya taso mata bayan fitowarta daga ɗakin, tsayawa ta yi ta tattaro duk wani natsuwa nata kafin ta isa ɗakin Baban Sasa, nan hira sosai su ka yi, sannan ya bata tukuicin hira da sanya tariyarsu sati biyu masu zuwa.
Yana faɗa mata lokacin za ta tafi ne, take ta ji duk wani natsuwar tafiya ya ɓace.

"Baban Sasa zan yi missing ɗinka don Allah kara lokaci" ta samu kanta da faɗi.

Kallonta yayi cikin dariyar su ta manya ya ce
"Ai muna tare, ki yi hakuri kuma ki bi mijinki, Allah ya sanya alkhairi ya muku Albarka, Nan da sati daya Saifullahi zai haɗo mana lefan ki bisa al'ada, kasancewar tsatso ɗaya kuka taso ba zai sa a toye mi ki hakkin ki na lefe" ba ta amsa ba anan ta sanya kuka mai tsuma rai, gaba ɗaya ta haɗa masa tun daga wanda ta ƙunso daga ɗakin Saifullah har zuwa na Tariya ga fuskar Dee Yusuf da ta gani a gate sai mata gizo ya ke a idanu.

***

Baban Sasa ne ya ruguzawa Saifullahi shirin shi na zuwa Kano a washagari, maganar tarewa nan da sati biyu, da na lefe da gidan da za su zauna ne gaba ɗaya ya ɓata masa lissafi. Yayi kokarin ɗaga tariyar ta hanyar ba da uzirin rashin kammala ginin sa da ya fara, Amma Baban Sasa ya ce wannan ba wani abu ba ne, zai iya zama ɗaya daga gidadan shi, ya zaɓi duk wanda ya masa a fara gyara. Haka ya kasance cikin bakin ciki da dana sanin biyewa Aysuh da yayi su ka dawo.

Magungunan mata da su tsumin da 'yan uwan Gwaggo ke angaza mata ba karamin tayarwa da Amatulah hankali su ke ba, tun tana musu alkunya ta na karɓa in ta shiga bandaki ta zubar har ta gaji ta fili ta ce musu su daina ɓata lokacin su, ita ba sha ta ke ba kuma ba ta ga dalilin sha ba. Haka kuma baccin ran da su ka nuna bai sa ta canza ra'ayin ta, har su ka gaji su ka bar ta da halin ta.

Satin biyun nan sun zo masu ne kamar kyaftawar ido, ba ta wani wahalar yin gayya ba sai su zulaikha da ya zama mata dole. Ana saura kwana uku aka nuna lehenta, wanda ya fi na duk wata ya mace da aka aurar a gidan.
Ranar bikin ta ci leshin ta masu kyau da atamfa ta dinga canzawa kowanne da hijab da ya shiga da shi.
Wannan shigan ya fi komi ɗaga hankalin Saifullah don a rayuwarshi bai taɓa fuskantar tozarta wa irin sa ba, wai shi kamar sa ana bikin sa duk da auren suna kawai ya tara amma a ce matarsa zulum zulum cikin Hijabi.

TAZARAR DA KE TSAKANINMUWhere stories live. Discover now