BABI NA ASHIRIN DA TARA

4.3K 460 262
                                    

TAZARAR DA KE TSAKANINMU 🤦🏼‍♂🤦🏿‍♀
✍🏾KHADIJA SIDI & SAFIYYAH UMMU-ABDOUL

    BABI NA  ASHIRIN DA TARA

"Abuja zan je mid semester tare da Dee. In na ce in je Yola yanzu wahala zan yi"
Maganar da ke ta shawagi cikin zuciyar ta kenan.

'Shin bayan dangantakar jini akwai dangantakar zuci tsakanin Dee da Mimi ne? Kamar dai akwai, toh idan ma akwai ni tawa a wa? Ko ba komai ai addini ya riga yayi tazara a tsakanin mu.. .. '

Da wannan muhawarar cikin ran ta su ka isa gida. Godiya ta yiwa Baba Anas sannan ta shiga ta gaida Baban Sasa wanda har lokacin ya na da burin komawar ta gidan Saifullahi. Gwaggo kuwa gaisuwa ke haɗa ta da Amatullah, da ta gaishe ta ɓangaran uwar jinyarta ta ke wucewa.

Ba ƙaramin kula da gyara ta ke samu wajan Mama ba, duk ta na ji a jikin ta dan kuwa in dai wajen gyara ne Mama ba ta tausaya mata.
Yau ɗin ma gaishe da Gwaggo ta yi in da ta aje mata Emjay kafin ta wuce wajen Mama. Ferfesun naman rago mai romo da kunun gyada Mama ta ajiye mata, Sai da ta tabbatar ta ci da shanye roman tas sannan ta ce maza ta shirya ta zo ta zauna ruwa mai dan zafi da ta tanadar mata domin a samu ɗinkin ya fara haɗe kan sa.

Saifullahi a na shi bangaran tun bayan da Amatullah bar gidan sa gaba ɗaya gidan ya daina masa daɗi, wani sa'in ma kukan Emjay har gizo ya ke masa a kunne.

Tsananin yanda  ya ke kewar su ya sanya ya ke Allah Allah ranar auren sa da Ayush ya zo, kila idan ya ga masoyiyar ta shi kusa da shi ya manta da batun Amatullah. Toh amma sharaɗin da Baban Sasa ya yanke ba ƙaramin damuwa ya ƙara masa ba, kullum da tunanin yanda zai bulluwa lamarin ya ke kwana ya ke tashi har dai ya yanke hukuncin tunkarar Ayush da maganar a yi ta takare ko zai sami sauki cikin ran sa.

Sati biyu kenan da yanke ɗanyen hukuncin dole ya ajiye ta a gidan wanda yayi daidai da saura sati shida ɗaurin auren su. Shiryawa yayi asubar fari ya nufi hanyar Kano.

Kallo ɗaya za a gano tsananin damuwar da ya ke ciki, duk yanda ya so ya ɓullo ma Ayush da zancen ya kasa ga bikin sai matsowa yake yi.

Kamar ko yaushe tarbo ya samu cike da maƙulashe, Ayush ta cika shi da kwalliyan ta mai rikita shi, ga ƙamshin da ke fita daga jikinta na ƙara narkashi duk da ba su yi tasirin cire masa firgicin da ke ransa ba.

Hira su ke jefi - jefi yana mai kara bayyana mata sirrin zuciyar sa da kuma tarin burikan da yake da na rayuwar auren su.  Sai da ya gama samun ta, ya tabbatar da ta gama natsuwa da Kalamansa haɗe da yarda da dacen da tayi na samun sa a matsayin miji sannan ya ce

"Aisha...."

Har cikin ranta ta ji muryar ta shi musammam yanda ya kira ainihin sunan ta, kallon shi ta ke ba tare da ta amsa ba, ganin haka ya cigaba da faɗin

"Ban san yanda zan mi ki bayani ki gane ba, amma zan yi iyakar kokari na, kuma kin san dai ba zan taɓa cutar da ke ba ko?"

Ayush da gaban ta ya fara faɗuwa ta ɗan gyara zama sannan ta ce

"Ina Jin ka, Baban Sasa ya ce ba za ka aure ni ba ne?"

Kai ya girgiza ya na mai mamakin yanda ta kama sunan Baban Sasa haka, ya ce

"Ya sallam! Ko kusa! Me zai sa ki yi tunanin haka?"

Cikin yatsine ta ce
"Toh ai yanda na ga ka na ba da labarin kakan na ka ne ai komai mai ma zai iya faruwa, bare kuma ka ce shi ya aura maka matar ka"

"Auren ya mutu....."

"Sorry?"
Ayush ta faɗa domin son Jin ya sake maimaitawa, dan gudun kar dai kunen ta ke zagi. Shi kuwa Saifullahi ya girgiza kai sannan ya kara da

TAZARAR DA KE TSAKANINMUWhere stories live. Discover now