BABI NA ASHIRIN DA BAKWAI

3.8K 447 239
                                    

TAZARAR DA KE TSAKANINMU 🤦🏼‍♂🤦🏿‍♀
✍🏾KHADIJA SIDI & SAFIYYAH UMMU-ABDOUL

    BABI NA  ASHIRIN DA BAKWAI

kafin su samu farfaɗowa daga suman zaunen da su ka yi su ka tsikayo shi yana faɗin
"Sannan wallahi kar ki bari na dawo na isko ki a gidan nan, banza fasiƙa"

Wani irin abu ya tokare ma Mimi a wuya, ta na jin ana faɗin maza ba su da kirki ba ta taɓa yarda ba sai yau da ta ga zahiri.

Yanda Saifullahi ya gifta ta a fusace ya sanya Mimi jan gefe gudun kar ya buge ta. Ta koma wajen Amatullah ta na kokarin karɓan Emjay daga hannun ta ta ce
"Yi hakuri Amatullah, I don't even know what to say, da na san zuwa asibiti da zuwan mu gidan nan abin da zamu jawo mi ki kenan wallahi da ba mu zo ba, kin ce cousin din ki ne ko? Tashi mu kai ki gida kafin ya riga mu"

Maimakon ta sakar mata Emjay, sai daɗa riƙe shi ta yi gam. Ta na mai duban Amatullah da idanun ta da suka riga su kafe ta ce

"No Mimi, ba zan bi ku ba, ki tafi kawai"

"Why? Saboda me?"

Mimi ta tambaya cike da mamaki. Amatullah ta ɗaura Emjay kafadar ta, ta na mai jijjaga shi, cikin wani irin yanayi mai wuyan fassarawa, yanayi na tsantsan kunar zuciya ta ce

"Ya kira ni fasiƙa, ya shegentar da ɗan sa, duk dan a dalilin na shiga motar Dee, kuskuren shiga motar ɗan uwan ki ya janyo wannan kazafin a gare ni Mimi, yanzu sai na ƙara shiga ku kai ni gida? iyayen mu su gan na fito daga motar ɗan uwan ki? Ta Yaya zan wanke kai na?"

"Iyayen ki sun san wacece ke Maman Emjay, they know what their daughter is capable of doing saboda sun san sun bawa diyar su tarbiya mai kyau..."

"Hakan ya sa ba zan bari daidai da second ɗaya zargi irin wannan ya gifta a zukatan su ba, na gode Mimi.....I will find my way"

"Maman Emjay a wannan lokacin har kina tuna wani bayan ke, ba ki tunanin halin da ki ke ciki? you have to wake up and start loving your self" mimi tace tana mai danne takaicin da ya taso mata.

Ba ta san me yasa mata da dama basu damuwa da ƙaunar kansu ba, a dai barsu da son zuciya (selfishness) amma sam ba su san wani abu wai shi self love ba balle self esteem.

Amatullah na mai runtse idanu, murya can kasa ta ce

"Go ...... just go Mimi"

"I'm so sorry Amatullah"

Cewar Mimi kafin ta juya ta fita jiki a sanyaye. Sai bayan fitar ta Amatullah ta sami damar bawa Emjay nono, gaba ɗaya kwakwalwar ta ce ta daskare yayin da idanun ta ke kan Emjay wanda yana shan shanono ya na mai sakin ajiyar zuciya.

***

Yanda ya ga Mimi ta shiga motar ta zauna jiki sanyaye ya sanya shi faɗin

"How is she?"

"Very hurt....."

Cewar Mimi, kafin ta juya ta na kallon Dee, cikin neman bayani ta ce

"Menene dangantakar ku? What was she to you? Me ya sa mijin ta zai zarge ka da neman matar shi na aure? What is happening Dee?"

Ajiyar zuciya ya saki, ya na mai wasa da sitiyarin motar ya ce

"It's a long story Mimi, Zan ba ki labari. Amma zancen neman matar shi wallahi sharri ne irin na namijin da bai san ciwon kan sa ba, Amatullah is the most decent person I know in my life, please mu tafi kafin wannan jahilin mijin na ta ya dawo, wallahi zan iya bugun shi...."

"Ya sake ta!"

Cewar Mimi ba tare da ta kalli Dee Yusuf ba. Ji  yayi kamar kunnen sa ne ke masa gizo.

TAZARAR DA KE TSAKANINMUWhere stories live. Discover now