BABI NA BAKWAI

3.4K 369 227
                                    

Bari mu riga yan WhatsApp. In kun tattaro mutunci za ku na riga su samun update😉💖❤️

FIKRA WRITERS ASSOCIATION 


TAZARAR DA KE TSAKANINMU 🤦🏼‍♂🤦🏿‍♀

✍🏾KHADIJA SIDI & SAFIYYAH UMMU-ABDOUL 

    BABI NA BAKWAI 

"Salamun alaikum"


Ta faɗa cikin faɗuwar gaban abin da zai biyo baya. Juyowa yayi fuska murtuke, bin ta yayi da kallo tun daga sama har kasa, irin wannan kallon na hadarin kaji.


 A wulakance ya amsa da


"Waalaikumus salam, na baki minti goma cal ki haɗo kayanki ki fito"


Iya abinda ya ce kenan ya buɗe mota ya shige. 


"Ki haɗo kayan ki mu tafi?"


Ta daɗa nanatawa cikin ranta, shikenan ta faru ta ƙare ramamme ya zagi maye. Karfin hali ta yi ta ƙarasa jikin motar, da ya ke ya ɗaga gilashin sai ta kwankwasa a hankali. Sai da yayi minti biyar kafin ya sauke tare da faɗin 


"Menene kuma? Ba ki ji abin da na ce ba ne?"


"Dama cewa na yi ya jikin  Baban Sasa?"


"Oh so ki ke na ce ya mutu ko? Toh ya nan daram da ran sa......"


"Alhamdulillah"


Amatullah ta furta ta na mai ajiyar zuciya ta juya ba tare da ta sake tambayar ba'asi ba. Tana zancen zuci ta isa hostel, har ta wuce shi ba ta sani ba sai ji ta yi ya kira sunan ta


"Amatullah?"


Juyowa ta yi ta na mai murmushin yake domin ɓoye ma sa damuwar da ta ke ciki. Sanye ya ke cikin shadda brown ɗikin yar shara, kan sa sanye da irin wannan hular ta yarbawa, ƙafafunsa cikin baƙin takalmi, hannun shi mai sanye da baƙin agogo ɗauke da leda baka. Kallo daya za ka masa ka amince da jimla daya, "Dee Yusuf namiji ne", namijin ma ɗan kwalisa, amma sam bai ɗaurawa kan sa girman kai kamar Saifullahi ba. Abin da Amatullah ke ayyanawa a ranta ke nan, a zahiri kuma cewa ta yi

"Yi hakuri, wallahi ban gan ka ba ne, ka kira ni ko? A ɗaki na bar wayar"


Kallo ɗaya ya mata ya gane damuwar da ke tattare da ita, haka kuma bai yi jinkirin tambayar dalili ba, ya na kokarin sanya idanun sa cikin na ta ya furta

"You're not ok, me ya faru? Ba ki da lafiya ne?"

Kai ta girgiza al'amar "ah ah" kafin daga bisani ta kara da 

TAZARAR DA KE TSAKANINMUWhere stories live. Discover now