BABI NA ASHIRIN DA UKU

2.8K 353 87
                                    

TAZARAR DA KE TSAKANINMU 🤦🏼‍♂🤦🏿‍♀
✍🏾KHADIJA SIDI & SAFIYYAH UMMU-ABDOUL

    BABI NA  ASHIRIN DA UKU

Ɗakinta ta koma, ta ɗauko jakar ta da take ɗan ajiyar ta, ko da ta ƙirga chanjin da ke ciki ko makaranta ba zai kai ta ba, balle ayi maganar dawo da ita gida. Bakin gado ta zauna tana zancen zuci. Ta san duk abin nan da Saifullahi ke mata dan cikin da take ɗauke da shi ne, cikin da ba ita ta sakawa kan ta, tsabagen rashin adalci irin na mijin ta. Nan ta sha alwashin hafe cikin ko da kuwa hakan na nufin karshen zaman ta da Saifullah ne.

Wasa wasa Amatullah na ji ta na gani ya hana ta zuwa makaranta, wayar ta kuma ya kashe, Su Gwoggo kuma ya tsara mu su karyar wayar Amatullah ta sami matsala, idan kuma suka kira daga ya ce ta na makaranta nan za ta wuni, sai ya ce ta na bayi. Tun abin ba ya damun Gwaggo har ta fara tunanin ko lafiya.

Gashi ko abinci idan ta girka ba ya ci balle a kai ga magana mai daɗi ta shiga tsakanin su. Duniya ta yiwa Amatullah zafi, ji ta ke kamar ta na gidan kurkuku har tsawan kwana uku. A na hudun ne da safe Saifullahi na fita, itama ta sanya hijabin ta. Dan kudin da ke hannun ta ta biya kudin mota ba ta zame ko ina ba sai gida.
A zaure ta tadda Baban Sasa zaune bisa tabarma tare da Baba Anas. Yanda ta shigo mu su afujajan kamar an koro ta ne ya sa suka tsora, in da a tare su ke tambayar lafiya? Gaban Baban Sasa ta zauna ta na kuka hawaye ɗaya na bin ɗaya, ta ce

"Baban Sasa ya hana ni zuwa makaranta, kwana uku kenan ya hana ni, ya ki kai ni ya kuma ki ba ni kudin mota da na tafi....."

"Innalillahi wainnailaihi rajiun, wai shi Saifullahi ya hana ki zuwa makaranta? Bayan nan ya zo ya gaishe mu kafin ya shige cikin gida ya ce da mu ya dawo daga kai ki makaranta ne? Shin dama ba lafiya lau ku ke zaune ba Amatullah? Me ya sa ba ki kira kin sheda mana a waya ba?"
Tambayoyin da Baba Sasa ya jero mata kenan. Shi kuwa Baba Anas gyada kai kawai ya ke.

"Wallahi Baban Sasa karya ya ke, ya hana ni zuwa makarantar, hatta wayar ma shi ya kwace tun ranar da na kira... .."

"Daina rantsuwa Amatullah, wallahi idan dai Saifullahi ne zai aika, jairi ka na ganin shi sim sim yaran nan bai da girma sai na jikin sa!"
Baba Anas ne ya katse ta. Cike da bacin rai ya tashi ya shiga ciki a fusace kafar shi ko takalmi Babu. Baban Sasa kuwa shi har a lokacin bai yarda Saifullahi zai iya aikata hakan ba, duk da kuwa Amatullah ba ta taba masa karya ba.

A dakin Hajiya ya tadda shi, yayi rashe rashe ya na cin wainar gero da kunu. Kallo ɗaya ya yiwa mahaifin na sa ya tabbatar da bacin ran da ke tattare da shi

"Babu shakka, dole ka rashe a nan kana cin kumallo hankali kwance tun da ka hana 'yar mutane zuwa makaranta"

Cewar Baba Anas ya na kallan sa cike da takaici, in da Saifullahi ya kware ya na mai fuzar da wainar da ya kai bakin sa jin maganar da mahaifin na shi yayi, har ya na kwarewa. Baba Anas bai kula da kwarewar da Saifullahi yayi ba, ya kara da

"Matar ka tana zaure, ka taho maza ka yiwa Baban Sasa dalilin hana ta zuwa makarantar da ka yi har tsahon kwana uku, da kuma dalilin kwace wayar ta da ka yi, mugu azzalumi! "

Har ya juya zai tafi ya dawo, ya na mai nuna sa da dan yatsa ya ce

"Ka tabbatar ka na da kwakkwarar hujja na aikata wannan zalincin, ka da ka manta na ɗau alkawarin yanda ka yiwa Amatullah kwatankwacin yanda zan yiwa uwar ka...."

Furucin yayi daidai da fitowar Hajiya daga uwar daka, ta na mai sallallami ta ta ke tambayar Baba Anas ko lafiya.

Saifullahi ya nuna da danyatsa ya ce
"Ga ki ga shi ai! Ka da ka sake ka kara minti biyar cikin gidan nan! Ka fito maza ka same mu!"

Ya juya ya fita a fusace. Saifullahi ma aje abinci yayi ya biyo bayan sa, Hajiya na tambayar ba'asi ya ce da ita ta jira zai mata bayani.

Shigar sa zauren ya tadda Amatullah zaune kusa da Baban Sasa har lokacin ba ta dena kuka ba. Bakin ciki da takaicin ganin ta ne ya tokare ma sa ƙirji, Baba Sasa kuwa bin shi yayi da kallo mai wuyar fassara. In da Baba Anas ke bin shi da harara. Kusa da Amatulah ya tsungunna, cikin nuna kulawa ya ce

TAZARAR DA KE TSAKANINMUWhere stories live. Discover now