BABI NA GOMA SHA TARA

2.8K 327 28
                                    

TAZARAR DA KE TSAKANINMU 🤦🏼‍♂🤦🏿‍♀

✍🏾KHADIJA SIDI & SAFIYYAH UMMU-ABDOUL

    BABI NA  GOMA SHA  TARA

Rana ɗaya aka yi komai aka gama. La'asar na yi Baban Sasa ya ce a shirya amarya a kai ta ɗakin mijin ta. Nan fa amarya kuka har da majina, musammam da aka ce ta zo ta yiwa Gwaggo sallama.

Hannayen ta biyu ta sa ta riƙe ƙafar Gwaggo da kyar aka iya bambare hannun aka wuce da ita ɓangaran Hajiya.

Nan kuwa ruwan habaice habaice su ka sha daga dangin Hajiya. Haka ma Hajiya wacce ta dubi Amatullah da ke tsugunne gaban ta fuskar ta rufe da lafaya, buɗar bakin ta sai cewa ta yi

" Toh mu dai babu abin cewa tunda ta faru ta kare ramamme ya zagi maye, Allah dai ya sa za ki iya kula da mijin na ki, dadin ta dai namiji mijin mace hudu ne....."

"Bare ma ɗiyar ta mu ai san kowa kin wanda ya rasa ce, wajan kula da iya zaman duniya ba a ce mata komai, uwar gida sarautar mata ba, kowa ya zo bayan ki ya ke...."
Cewar kanwar Gwaggo yayinda yan uwa Gwaggo su ka kara karfafa mata gwiwa da guɗa.

"Toh ai sai ku tashi a kai ta, Allah ya sa a dace"

"Allahumma amen"

Cewar dangin Gwaggo, in da su ka tayar da Amatulah. Kamar yanda su yan uwan Hajiya da yayyan Saifullahi ba su fasa yada habaici ba haka su ma dangin Gwaggo ba su fasa guɗa ba.

Ɗakin Baba Sasa aka kai Amatullah, nan aka tarad da Mahaifin ta tare da su Baba Zubairu da Baba Anas. Daya bayan ɗaya haka duka su ka mata faɗa tare da sanya albarka, ko da aka zo kan Mahaifin Amatullah sai cewa yayi

"Tashi ki tafi dakin mijin ki ɗiyar albarka, duk abinda za ki yi ki yi da halin ki, ba ni da haufi kan ki, kin haifu Amatullah, Allah ya sanya mi ki albarka"

Ya karasa maganar ne yayinda yar kwalla ke shirin fita daga idanunsa. Nan ma fa Amatullah ta ce ba ta tashi, aka yi aka yi, ta cije kuka ta ke harda wayyo Allah.
Mahaifin ta ne da kan sa ya riko hannun ta, sannan ta yarda ta mike, har mota ya kai ta sannan ya barta hannun manya ya koma ciki. Yan uwa da abokan arziki su ka shige mota, aka dauki hanyar gidan amarya.

***
Tafiya ce ɗoɗar daga Amaru zuwa filin mallawa da ke sabon layi, filin cikin na gadon su Baban Sasa ne ya mallaka, sanda ake yanka filayen ana siyarwa ya so ya siyar sai kuma ya yi tunanin gine shi.
Babu laifi gidan ginin zamani ne, flat ne, drive in mai dauke da daki uku kowanne da bandakin shi ciki, da kuma madaidaicin kitchen, sai kuma katon falo guda. Su Zulaikha ne su ka yi kokarin zauna mata kafin ango ya zo kar a barta ita kadai.  Amma shiru babu Saifullahi babu alamar shi, dan haka sallama su ka mata, ta na ji ta na gani su ka barta ita kaɗai duk magiyar ta da su zauna amma umurni ne daga baban Sasa cewa kada wanda ya kwana a gidan duk da hakan al'adar mutan zaria ne. 

Amatullah gwanar tsoro, suna fita ta sa mukulli ta garkame ɗakin ta, ta shige toilet ta dauro alwala bisa dadduma ta shiga jera salloli ta na rokan Allah sauki bisa lamarin ta, nan bacci mai nauyi ya sace ta.

Yunwa ne ya tada ita da asubar fari. Sai da ta yi sallar asuba, ba tare da ta cire hijabin da ta yi sallah da shi ba, a hankali ta bude kofar ɗakinta ta ɗan leƙa falon, duhun da ta gani ya bata karfin gwiwar fitowa ta na mai haska falon da wayan ta domin neman hanyar kitchen.

Babu shakka su Gwaggo sun tsantsara mata falon na ta da kayan alatu, kujerun ta ruwan zuma da kanana filullukan da aka jera ba karamin shiga yayi da labulen falon ba. Ganin kofofi hudu daya ya ɗan yi kusa da dakin ta, sai kuma ɗayan bangaran yamma kusa da kofar shigowa falon, sai kuma ɗayan wanda ke can gefe guda ya sa  Amatullah ta yi turus, dan kuwa ba ta san wanene wanne cikin su ba, gashi yunwa ta ke ji kamar ta yi ihu.
Lissafin ta wannan na kusa da ita zai iya kasancewa dakin mai gidan, wancan na kusa da kofa ya zama na baki, dan haka na can gefe shi ne kitchen, kai tsaye to nufe shi.
Zuciyar ta daya ta kama mubudin kofar ta bude ta na mai tura kan ta ciki. Hasken wutan lantarki ne ya fara ziyarta idanun ta, kafin idanun ta ya gane mata wanda ke tsaye gaban fridge daga shi sai gajeran wando, ya bata baya hannun sa dauke da gorar ruwa. Da sauri ta juya cikin rawar jiki, wayar da ke hannun ta ce ta sullube ta faɗi kasa. Karar faduwar wayar ya sanya shi jiyowa fuskar shi cike da mamaki. Bacin rai ne ya maye gurbin mamakin da ya bayyana fuskar shi ganin Amatullah, cikin sauri da tsungunna ta dau wayar da niyar ficewa, ya dakatar da ita cikin tsawa ya ce

"Ke wace irin bagidajiya ce wai? Zo nan Malama!"

Tsayawa ta yi cak idanun ta kasa, ita ba ta fita ba, haka kuma ba ta karasa in da ya ke cikin kitchen ɗin ba.

"Ba da ke na ke magana ba! Ki zo na ce!"

Ya kara daka mata tsawa a karo na biyu in da ta tsinci kan ta tana mai karasawa gaban sa, da kyar ta yi karfin hali ta kai kallan ta ga fuskar sa ba tare da ta kalli kirgin sa ba, yanayin kallan takaici da ya ke mata ya sa ta sake yin ƙasa da na ta idon ka na ta furta

"Ban san kana kitchen ɗin ba......"

"Iya ka tarbiyar da aka koya mi ki kenan? Ba ki iya gaisuwa ba? Ga gidadanci ga rashin tarbiya...."

Lebben na kasa ta cije cikin takaici da jin zafin furucin Saifullahi, kafin ta kai ga ba shi amsa sai ji ta ya ce

"Bani hijabin nan!!!!!"

Jin maganar kamar kunnen ta ke mata zagi ya sa ta ɗaga kai da sauri ta na mai fidda idanu. Kai ya girgiza ya ce

"Yes kin ji ni da kyau, ki ciro hijabin jikin ki ki bani yanzun nan!!!!"

Baya ta ja tana mai girgiza kai yayinda zuciyar ta ke dukan uku uku ta furta

"Dan Allah dan annabi ka yi hakuri....."

"Dalla malama hakurin me ki ke bani, just do as I said ko kuwa ni na cire mi ki! you are so irritating!!!!"

Hawaye ne ya fara zuba daga idanun ta, ganin ba ta da niyar bin umarnin shi ya sanya shi tinkarar ta, ganin haka itama ta fara ja da baya tana fadin

"Menene haka wai ya Saifullahi?"

"Just remove the damn thing and give it to me!"

Jiki na rawa ta ciro hijabin, ta rike hannun ta idanun ta kallan kasa yayinda hawaye daya ke bin daya. Kallo ya bita da shi, kasancewar ba shiri bacci ya sace ta daren jiya, atamfar da aka kai ta da shi ne jikin ta. Kai ya girziza ya na mai nuna ta da hannu tun daga sama har kasa ya ce

"Just imagine! Na tabbatar da wannan atamfar a jikin ki ki ka kwana tsabagen gidadanci! God you're so local Amatullah!!!"

Ya sa hannu ya fizge hijabin daga hannun ta ya yi wulgi da shi cikin kwandan sharan da ke cikin kitchen, in da Amatulah ta bi shi da kallo, kafin ta dawo da kallan ta ga Saifullahi. Ya na nuna ta da dan yatsa ya ce
" Ni Saifullahi, wanda aka ɗaura min auran ki akan dole, daga yau har ki karaci zaman ki gida, na umarce ki da ki dena saka waccan abu, Kar na sake ganin ki da hijabi Amatullah! Na haramta mi ki saka hijabi cikin gida na!!! Bagidajiya kawai!!!"

Ya na gama magana ya fice yana huci kamar zaki. Ya bar Amatullah zube a kasa ta na sharbar kuka, shin ashe akwai ranar da za a haramta mata sanya hijabi? Kuma mijin ta? Wannan masifa har ina!

"Innalillahi wainnailaihi ilaihi rajiun"

Furucin da ta ke yayinda tsanar Saifullahi ke kara ratsa zuciyar ta.

TAZARAR DA KE TSAKANINMUWhere stories live. Discover now