BABI NA UKU

4K 404 52
                                    

Bari mu riga yan WhatsApp 😉
Bamu san fatalwa ooo.
UMMU-ABDOUL da KHADIJA SIDI ke muku fatan Alkhairi

Much love💖♥️❤️💕

A bakin gate ta iske abokan tafiyarta, nan su ka mata caa kowa da abin da yake tambayarta.
"Cewa yayi yana sonki hala" shine tambayar da ya fi tsaya mata, Zulaikha dai bata ce komi ba don ta san ita ɗin mai laifi ce.
"Haka kawai sai ya ce yana so na? A wajen photocopy fa muka haɗu kwanaki banda canji ya bada Naira 20 din ni shaf na manta ma" ta samu kanta da zabga ƙarya don bata son wani abu ya fito na abin da ke tsakanin ta da Dee.
"Har na fara murna, don wallahi ko ni da nake matar aure ina kyasa Dee Yusuf, in fa ya ce yana sonki mu ɗin gaba ɗayanmu za mu shiga wani sawu na masu aji ne" Faɗin Zuwaira da su ke kira da maman Jaafar. Ajinsu ɗaya, a shekarun za ta girme su amma kuma ƙawarsu ce, yanzu ma kasuwar da za su shiga ita za su raka siyayya.
Ba ta ce komi ba amma ita da ta san alkawarin da ke kanta ta san hakan ba mai yiwuwa bane ko da a ce shi ɗin kimtsattse ne ba tambaɗaɗɗe kamar yanda ta ke kallonsa ba.
Da hirar Dee Yusuf su ka isa kasuwa, ita dai jin su take yi don ba su isa kasuwa ba har sai da kawayen ta su ka  hasko kalan yaran da za su haifa in aurenta da Dee Yusuf ya tabbata.
Daga kasuwa gidajensu su ka wuce suna fatan Allah ya Raya su zuwa sati biyu da karatun zango na biyu zai kankama. Sai a lokacin Amatullah ta samu ta keɓe da Zulaikha saboda su biyun hanyarsu ɗaya.
"In kashe ni za a yi ma kawai a kashe ko? ke babu abin da yayi tsalle ya tsinka miki mari" Amatullah ta ce tana hararar Zulaikha.
"Afuwan bibty, kin san na yi tunanin in na tsaya saura ma za su tsaya kuma ba zamu iya daƙile zancen ba, me ya ce miki?" ta ƙarasa tana mai neman karin bayani akan abin da ya wakana tsakanin kawarta da dodonta.
"Me kuwa zai ce min, da na gaji da tsayuwa ba tare da ya ce komi ba na yi wucewata na bar shi tsaye" Amatullah ta samu kanta da yin ƙarya a karo na biyu.
'wai me ye kike ɓoyewa ne' ta samu zuciyar ta da faɗi.
'ai sirri da daɗi' ɗayan sashi na zuciyar ta ke bada wannan amsar.
"Toh Allah shiga tsakanin nagari da mugu" ta tsinkayi zulaikha da faɗin haka. "Aameen" tace tana canza labarin su zuwa ga batun jarrabawar da su ka yi a ranar.
***
Sai da la'asar ta shiga gidan su, nan ta iske yan uwa da iyayensu kowa yai mata murnar kammala jarrabawa da fatan samun nasara.
"Baba mun dawo, ya karfin jikinka" tace yayin da ta shiga ɗakin baban Sasa, Shima addu'a ya bi ta da shi sannan ya ce da ita
"Ina so na shaida aurenku Baiwar Allah! Na ce a kira min Saifu, don ba zan so ƙasa ya rufe ido na ban cika ba, tun da har Allah ya bani tsawon ran kaiwa lokacin da duk kuka isa aure" jin sa take yi yayin da idanunta ke kallon laɓɓansa yana faɗa mata su, sai a lokacin ta ga tsantsan kamanninta da shi, sai a lokacin ta ke yarda da zancen da ake na suna kama da Saifullah don tun tana yarinya ta haddace babu mai kama da Baban Sasa sama da Saifullah.
"kin yi shiru Amatu" yace yana taɓo ta.
"Baaba, ashe haka nake kama da kai" tace tana dariya ƙasa ƙasa, shi ma sai ya shiga dariya.
"kin ga kenan duk wanda ya shiga gidanku zai tuna da ni ya min addu'a" ya ce cikin dariya. Haka su ka dinga tsokanar juna cikin nishadi, kiran sallan magariba ne ya tayar da ita bayan ta sa masa ruwan alwala a buta.
***
Yana zaune a harabar sashin su a jami'ar kimiyya na gwamnatin ƙasar Rasha da ke birnin Moscow watau MATI Russian State Technological University Moscow, tattaunawa su ke yi da abokan karatunsa akan sabuwar injimin da su ke kerawa don wani baje koli da jami'ar ke shirin aiwatarwa nan da kwana biyar, a nan wayarsa  ta ɗauki ƙara. Kamar ba zai ɗauka ba amma jin kiɗan da ya tanadar ma jininsa ne ya sa shi saurin ɗauka, tsoronsa kar a ce Baban Sasa ne ya rasu, don shi ya san son da yake ma tsohon nan ko iyayen sa albarka.
"excuse me" ya ce yana mai zuwa gefe tare da tattara duk wani natsuwa da ya mallaka ya doka sallama bayan ya ɗaga.
"Saifuna ba zaka dawo in ganka ba" yace cikin halin ciwo.
"Alkawari Baba ba zan ƙara sati biyu ba, kai dai kar ka yarda ka bi su ko sun zo ɗaukan ka" yace cikin shaƙiyanci hakan ya sanya baban Sasa tuntsirewa da dariya. Ya tambaye shi jikin sa, da sauran ahlin nan ya amsa yana mai ƙara jin jinjina masa zancen zuwansa. A haka su ka yi sallama, ya koma wajen abokan karatunsa yana mai ba su hakuri.
Kwana goma ya ƙara akan ranar da su ka yi waya jirgi ya sauke shi a filin jirgin sama na murtala Muhammad da ke birnin ikko ƙarfe goma sha biyu da rabi na dare.
Kallo ɗaya za ka masa ka san bakin fata ne duk da rinewar da fatarsa ta yi ya rikiɗe kamar wani bakin bature. Shi ɗin ba wani dogo bane sannan babu mai kiransa gajere, zanensa na mallawa na kwance a gefen fuskarsa hakan na ɗaya daga cikin abin da ke ƙara maida fuskarsa abin kauna ga mata kamar yadda wata budurwar sa ta faɗa masa.
Daga ikko jirgin da ke tashi zuwa Kaduna ƙarfe shida na safiyar washegari ya bi, daga nan ya ɗauki shatar mota har Amaru.
Babu zato su ka tsinkayi muryarsa yana sallama, nan gida ya kacame da murna, duk ihun da ake Amatullah na zaune a ɗaki bata ko motsa ba cike take da fargaba da tsoro, cigaba da karatun ta tayi a cikin littafin Nurturing Eeman in children na Dr Aisha Hamdan. Wannan shine ɗabi'ar da ta fi so in ba ta  komi toh ta samu littafin ƙaruwa na addini ta dinga karantawa.
***
Tun da ya shigo gidan idon sa ke kan yan matan da yake gani yana kasa kunnen wacce za a kira da Amatullah, dukkansu babu na yarwa saboda wasun su na da gaɓa-gaɓan jiki wasu kuma yan firit amma duk kyawawa ne daidai misali.
Bai manta hotonta da ya gani ƙarshe shekarun goma da suka wuce ba, ko a lokacin ya san ita din mai kyauce da abokansa za su yaba da ita. Bare kuma yanzu da aka ce ta shiga Jami'a, ya san zai same ta da wayewa, dan shi a rayuwar sa ya na san wayayyiyar mace.
Sunaye mabambamta ya ke ji ana kira duk babu Amatullah har dai ya hakura tare da sa ran ko tana makaranta ne.
Washegari Zulaikha ta kawo mata ziyara tare da duba jikin Baban Sasa, sun fito za ta raka ta ne su ka ci karo da shi a ƙofar gida. Sun gaisa cikin mutunci su ka wuce yana mamakin yanda duk in da ya gilma cikin zaria mata sanye da zumbura zumburan hijabi, su wainnan ma abin takaici har da safa ko me su ke rufewa oho 'watakila kutare ne' ya samu zuciyar sa da fadin haka. Tsaki yayi ya cigaba da abin da yake a kan wayarsa, a haka ta dawo, ta sanya kafa ɗaya kenan a cikin gidan kenan ta jiyo muryar yar gidan goggonsu ta bayanta tana fadin
"A'ah su Amatullah yan boko ne a garin" Hakan ya sanya ta juyowa cikin fara'a tace
"A'ah su matan aure ne a garin" nan su ka sa dariya, Hakan ya zama sarar su duk suka haɗu sai su yi amfani da kasancewarsu abokan wasanta su gasa mata magana akan rashin aure da boko. Shi ke nan da sun kira ta yar boko sai ta kira su matan aure.

TAZARAR DA KE TSAKANINMUWhere stories live. Discover now