BABI NA GOMA SHA BAKWAI

2.8K 339 58
                                    

TAZARAR DA KE TSAKANINMU 🤦🏼‍♂🤦🏿‍♀

✍🏾KHADIJA SIDI & SAFIYYAH UMMU-ABDOUL

    BABI NA  GOMA SHA  BAKWAI

"Ya na ga ka wani saki baki ka na kallo na? I don't get you! Yanzu kamar kai wa ya isa ya maka auren dole? Sai dai ka na so kai ma"

Cewar Aysuh cike da tsiwa, ta na magana ne idanun ta cikin na sa. Ganin dai in yayi sake allura ce za ta tono garma, dan haka Saifullahi na mai sosa kyeya ya furta

"Ayush kenan, Allah ya sa mu dace...."

"Ba Allah ya sa mu dace ba, answer me! Yanzu akwai wanda zai iya ma maka auren dole?"

Ayush ta sake katse shi ta na masa irin kallon nan mai cike da alamar tambaya.

"Aysuh?"
Ya kira sunan ta da kakkausar murya.

"Yea? Ina jinka"

"Kin yarda da ni?"

Kai ta gyada masa ala'mar eh. Hannun ta biyu ya riƙe kana ya ce

"Alhamdulillah, toh ina so ki yarda ki kuma amince babu wani mahaluki a duniyar nan da ya isa ya sanya tazara a tsakanin mu"

Cikin jin dadin maganar ta sakar masa murmushi mai kayatarwa tare da faɗin

"I trust you Boo, and I love you so so much"

"I love you more Ayush"

Cewar Saifullahi, cikin ransa ya na mai yakinin kare hakkin soyayyar su daga dukkanin fitinar Baban Sasa.

****

Sai da ya ƙara kwana uku bayan bikin jana'iza kafin yayi haramar komawa Zaria. Ranar juma'a da safe ya tashi da shiri cikin ran sa ya na mai baƙin cikin komawar sa makaranta. A ɗaki ya tadda mahaifiyar shi, zaune bisa gado, kallo daya za a mata a tabbatar da damuwar da ke tattare da ita. Gaban ta ya je ya durkusa, cike da lababi ya ce

"Mummy, wannan damuwar da na ke ganin ki ciki ya na breaking heart ɗina, it makes me want to stay with you and forget about going back to school Mummy...."

"Shhhhh!"

Ta katse shi ta na mai dafa kan sa, kan ta ce

"David my son, damuwa ya zama dole, rashin masoyi abu ne mai wuya, you will not understand, I hope you don't have to experience it in your life my son....."

'I have Mummy, I've lost Amatullah forever'
Cewar Dee cikin zuciyar shi.

"Amma rayuwa ba za ta tsaya ba, life goes on, so ina ba ka umarnin komawa makaranta, ka gama karatun ka, make sure you graduate with flying colors, kar ka manta ka na da ƙanne that are looking up to you, make us proud as always"
Ta karasa maganar ne yayinda ƙwalla ya cika idanun ta. Cikin sassanyar murya ya furta

"I will Mummy, I shall make you proud"

"Ni kuwa  David ya batun yarinyar nan da ka ke so? Kasan mutuwar nan bai bari mun yi magana ba, Kun sasanta? Yaushe za ka je Hadeja?"

Gaban sa ne yayi mummunar faɗuwa, ya so Allah ya mantar da ita ba dan komai ba sai dan gujin bacin ran da za ta shiga idan ta ji yanda aka wulakanta shi kasancewar ya so ya musulunta sanadin soyayya.

"Ina jin ka David, ko dai da matsala ne?"

Ta sake tambayar shi cike da damuwa ganin yayi shiru. A hankali ya furta
"Mummy forget about that girl, she is as good as dead to me"

Shiru ta yi ta na duban sa, cikin ran ta tana so ta tambayi dalilin canjin ra'ayin Dee, amma kuma yanayin sa da kuma yanda ta ji muryar sa yayinda da ya ke maganar ya sanya ta sake shawara. Ta ce
"I understand"

TAZARAR DA KE TSAKANINMUWhere stories live. Discover now