BABI NA TALATIN DA BIYAR

3.2K 351 156
                                    

TAZARAR DA KE TSAKANINMU 🤦🏼‍♂🤦🏿‍♀

✍🏾KHADIJA SIDI & SAFIYYAH UMMU-ABDOUL 

    BABI NA  TALATIN DA  BIYAR 

TAZARAR DA KE TSAKANINMU 🤦🏼‍♂🤦🏿‍♀

✍🏾KHADIJA SIDI & SAFIYYAH UMMU-ABDOUL 

    BABI NA  TALATIN DA  BIYAR 

"Ban kyauta ba na sani Babe, kin dai san ke nake so, ki yi shiru ki faɗa min abin da kike so ayi, yanzu kina ihu cikin dare kowa zai san ciki gare ki kuma ba za mu iya ɗaukan ko wani mataki ba" yace mata cikin raɗa, sai a lokacin ta tuna zancen ta da Jamila, take ta haɗiye duk wani kuka da kururuwa da ya ke zuwa mata.

"Ba wai bana son haihuwa da kai bane honey pie, Kai ma ka san son da nake maka ya sa na bar kuɗi da jin daɗin rayuwa don na kasance tare da kai" tace ganin ya bata goyon baya, ita kanta ta san wasu abubuwan da take masa ne ya sanya ya ke mata abin da ya ke mata, itama ba yin kanta bane, shi ya kulle ta a akurki. 

"Na sani babe, amma ai baki taɓa natsuwa kin min bayani ba, na taɓa hana ki abin da kike so ne?" ya sake fadi bayan ya janyeta daga bahaya zuwa cikin ɗakin ta su ka zauna a kan gadonta. 

"Tell me what you want babe, your wish is always my command your highness" yace mata yana kallon cikin idon ta. Nan ya mata kwarjini sosai ta kasa cewa komi, shiru tayi ta sunkuyar da kai amma tunawa da tayi dama na zuwa ne sau ɗaya in ta wuce dole sai mutum ya jira wata.

"A cire cikin nan don Allah, mu jira har mu koma gidan mu, ka ga a gidan nan wace tarbiyya zamu ba yaya, ko mun yi a ɗaka da ya shiga cikin gida za a wargaza masa" ta faɗi a hankali. Kiris ya ƙunduma mata Ashar, amma ya danne saboda in ya biye mata da faɗa shi ke da asara in ta zubar.

"Haka ne kuma fa, kinga ban taɓa tunanin nan ba, yanzu dai ki bari sai mu kai ayi flushing din sa out, this week will be a very busy week Amma I promise you ba za a wuce next week ba zai bi ma kwararar" yace yana rungumarta, ji yake kamar ƙaya yake runguma a jikinsa, tunanin dole ya nemo yanda zai shawo kan Amatullah yake don tabbas itace macen rufin asiri macen arziki.

Lallashinta ya dinga yi yana mata alkawura na ƙarya da in da kan aurensu ne toh tabbas za su zama na gaskiya ne.

Kiran sallah na biyu ya tayar da shi daga gareta, alwala yayi ya gabatar da raka'atanil Fajr sannan ya wuce masallaci. Daga yanayin kallon da ya ga iyayensa na masa ya san tabbas sun ji muryar Ayush, addu'a yayi Allah ya sa Hakan ya sa su tausaya masa su maida masa da auren Amatullah.

***

Sati ɗayan da ya wuce babu abin da yake sai fafutukar son Magana da Amatullah, kasancewar ta koma makaranta ya sanya abin ya masa wahala. A tunaninsa hostel take, sai ya kwashi jiki ya je gaban Amina hall ko Ribadu hall ya zauna  yana ƙirga masu shiga da fita hostel ɗin.

 Ganin hakan bai cika masa burinsa ba ya koma zaman faculty of pharmaceutical sciences. Nan ma haka yake ƙarasa shawagin sa ba tare da ya ganta ba, sau biyu yana hango ta a aji suna ɗaukan darasi nan zai hakince ya jira amma kamar wacce ke rufe ido ba ya sanin lokacin da suke ficewa. 

Asali duk zuwan shi Mimi ce ke ganinsa sai ta fitar da su ta wata ƙofar ba wanda ya ke jira ba.

"Ai nan gani nan bari malam" takance a ranta a duk lokacin da ta hango shi. 

Ya kan kira Amatullah amma in zai kira sau ɗari ba ta ko ɗagawa, haka saƙonni daban daban na ban hakuri, soyayya da alkawari duk sai dai ta karanta ta share. 

Yau ma kamar yanda ya saba ya shigo sashin na su, ya iske suna karatu, nan ya nemi izinin malamin akan yana son ganin matarsa. Amatullah bata an kare da shi ba sai ganin da tayi yana nuna ta da yatsa.

TAZARAR DA KE TSAKANINMUWhere stories live. Discover now