BABI NA TAKWAS

3.1K 374 177
                                    

FIKRA WRITERS ASSOCIATION

TAZARAR DA KE TSAKANINMU 🤦🏼‍♂🤦🏿‍♀

✍🏾KHADIJA SIDI & SAFIYYAH UMMU-ABDOUL

    BABI NA TAKWAS

Shirun da kowa yayi ba ƙaramin ɗagawa Amatullah hankali yayi ba, musammam da ta kai kallan ta ga Gwaggo, yanayin fuskar Gwaggo ne ya sanya hawaye zuba daga idanun ta. Cikin ranta fadi ta ke

"Allah ya sa za ki yafe min Gwaggo"
"Uhum"

Gyaran muryar Baban Sasa ne ya dawo da Amatullah cikin hayyacin ta, nan ta tsincin kan ta tana mai faɗin

" Wallahi Baban Sasa na rantse da Allah ban karya alkawarin da na dauka ma ka ba..... wallahi, dama shi ne kullum ya ke cewa ba ya so na....."

"Shi wa?"
Baban Sasa ya tambaya a dake, yayinda ya tsare Saifullahi da idanu.

"Yaya Saifullahi"

Ta bashi amsa cikin kuka.

"Biri yayi kama da mutum, Ni na ce mu ku wannan yaron da kuke gani zai aikata, dena kuka Amatullah, me ma zai sa ka dauki muryar ta haka ba tare da izinin ta ba? Ka mata adalci kenan? "
Cewar Mahaifin Saifullahi ya na mai nuna shi da danyatsa, Saifullahi wanda be taba zatan Amatullah za ta ma sa haka ba shi ma kai ya sunkuyar cike da fargaba.

"Saifullahi menene gaskiyar wannan maganar?"
Cewar Baban Sasa ya na mai kallan Saifullahi, wanda ya dukar da kai cikin ladabi ya furta

"Baban Sasa ni kuwa me zai sa na ki jini na? Me zai sa na ki Amatullah? Me zai sa na kasa son abin da ka ke so? Har ga Allah ina nan kan baka na na yi mu ku biyayya, shi ya sa ma na aje duk abun da na ke na taho daga uwa duniya domin cika ma ka buri, da wani ido zan kalle ka? Da wani baki zan furta kiyayya ga Amatullah gare ku?"

Idan aka ɗauke Mahaifin Saifullahi da Amatullah babu wanda be gamsu da jawabin Saifullahi ba. Musammam Baban Sasa wanda har gyada kai ya ke cikin gamsuwa da jin dadi, ya furta
"Na gode maka Saifullahi, yanda ka faranta min Allah ya faranta ma ka"
Saifu kuwa wani dadi ne ya sake rufe shi, in da Amatullah ke fuskantar kishiyar haka musammam jin Baban Sasa ya ce
"Ina Amatullah?"

"Na'am Baba"

"Na ji na amince ba ki karya alkawarin da ki ka ɗaukar min ba, Allah ya gani kauna ce ya sanya na so hadin auren nan tsakanin ku da ɗan uwan ki, amma yanayi ya nuna akwai dan targanda saboda haka ga umarni na gare ki......"

Ya dan takaita yayinda idanun sa ke bisa bangon dakin kamar mai nazari. In banda kukan Amatullah babu abin da ke tashi cikin dakin. Kana ya nisa yayinda ya mayar da kallan sa ga Amatullah sannan ya furta

"Ki shedawa ko shi wanene wanda ki ke biɗa, mun bashi sati biyu ya zo ya gabatar da kan shi a gare mu, daga randa sati biyun nan ya cika kuma babu wanda ya zo gare mu da batu na auren ki toh fa ku sheda ranar zan sanya auren Amatullah da Saifullahi wata biyu da izinin rabbil samawati......."

Yayin da hantar Amatullah ta kaɗa, shi kuwa shi kuwa Saifu bakin ciki ne ya sake lullube shi, wannan shi ne ga koshi ga kwanan yunwa, wannan masifa ta tsoho yaushe za ta kare ne haka! Mitar da ya ke ta yi cikin ran sa. Har Baban Sasa ya sallame su kowa yayi na shi wajan. Baba Anas Mahaifin Saifullahi ne ya kira shi daki domin yi masa nasiha akan abun da ya faru. Ita kuwa Amatullah dakin ta ta koma ta ci kukan ta ta koshi. Babban tashin hankalin ta shi ne shin ya za ta yi da fushin mahaifiyar ta da ta san ko shakka babu a kule ta ke d ita, sai kuma na tuggun da Saifullahi ya kulla mata. Tun da take a rayuwar ta ba ta taba soyayya ba, asali ma bata taba ji tana san wani da namiji cikin rayuwar ta ba face Dee Yusuf, shi kuma ba wai ya furta kalmar so a gare ta ba bare ta sa ran zai iya gabatar da kan sa cikin sati biyu domin kubucewa shiga hannun makirin namiji kamar Saifullahi. Abin da ke dan kwantar mata da hankali shi ne idan ta tuna Dee Yusuf ya na ta jaddada mata akwai maganar da ya ke so su yi, gwara ta koma makaranta idan ma son ta ya ke ya fada mata in ya so ta ce idan da gaske ya ke ya kawai ya zo ya gaida Baban Sasa, da wannan ta sami karfin gwiwar fitawo falo.
Kallon da mahaifiyarta ta bi ta da shi ne tun a ɗakin baban Sasa ya kashe mata duk wani kwarin guiwa da take tunanin ta na da shi. Saifullah ya shammace ta, ba ta taɓa jin kunya irin na yau ba duk da ba wani tashin hankali bane iyayen su ka nuna duk da ransu bai so hakan ba.
Tsoron keɓantuwarsu da mahaifiyarta take amma duk da haka ba ta fasa zaman jiranta ba tare da ɗauko mus'hafin da Dee ya bata ta shiga tilawa a cikin suratul Yusuf.
Tana kai Ayar "WA'UFAWIDU AMRI ILALLAH.." taji wasu hawaye na zubo mata tare da jin wani irin ni'imomi na ratsa ta jini da ɓargo. Lallai Allah mai lura ne a kan bayinsa ta fassara karashen Ayar.
'Gashi ya kawo miki ɗauki cikin ruwan sanyi, ku yi aurenku da Dee hankali kwance' zuciyar ta mai kaunar tarayyarta da Dee ta fadi mata.
'Amma ya za ki yi da fushin mahaifa? Shi Dee din ma ya fada miki yana son ki ne' ɗayan zuciyarta mai fidda gaskiya ta nusar da ita, hakan ya sanya ta ji kawai babu abin da ya fi mata fiye da ta isa makaranta ta ga Dee Yusuf.
Shigowar mahaifiyarta ya tsaida mata tunanin da take, bata ce da ita kanzil, amma kwatakwata babu wani rahama ko annuri a tattare da fuskarta.
"Ki yi hakuri Gwaggo shi ya tunzura ni na fadi haka ban san zai yi recording ba" tace tana mai kama kafar mahaifiyarta cikin kuka. Janye kafafunta tayi, tace mata
"Ai duk wanda yace shi bai haifu ba, zai yi fiye da wannan ma" ta janye jiki ta bar ɗakin.
Duk yanda Amatullah ta so ta bata hakuri kafin ta tafi ya gagara saboda gaba ɗaya ba ta dawo ɗakin ba. Haka jiki a saɓule ta yi shirin komawa maranta, cikin shigar ta da ta saba wato hijab.
A kofar gida ya ganta, ta tsayar da mai keke kenan domin fitar da ita titin da za ta hau Bus.
"Malam jeka abin ka"
ya faɗi yana kallon ɗan keke. Kallon sa take, in ba ƙarya idon ta ke mata ba farin ciki ne tsantsa a tattare da shi.
"Mrs Danliti Yusuf ya dai? Zo na taimaka na rage mi ki hanya"
yace yana mai buɗe mata motar, har ta yi niyyar wucewa ta hango Baba Muhammadu kuma idanunsa akansu. Murmushi ta sakar masa kana ta shiga ciki tana mai faɗaɗa murmushi ta.
Suna wuce harabar gidan su ta gimtse fuska tare da fad'in
"Menene amfanin hakan da ka ke yi? Menene afanin bata min suna a wajen iyayen mu? Menene amfanin mutum mai fuska biyu?"
Shiru ya mata kamar ba zai amsa ba, kafin daga bisani ya ce
"Kin san duk a cikin iyayenmu mata ban da sama da mahaifiyarki. Ba wai ina son bata ƙi a wajan iyayen mu ba ne, ba wai na ƙi ki bane fa. Akwai tazara a tsakanin mu, har ga Allah ke ba irin matar da na ke burin aure ba ce, you're too local for my liking, ina san wayayyiyar mace ta burgewa wanda duk wanda ya ganta zai san ta amsa sunan ta mata ga Saif."
Ya fada ne ya na mai kallan ta ta wutsiyar ido, ya kara da
"Kin ga wannan Danliti da ki ke so?....."

TAZARAR DA KE TSAKANINMUWhere stories live. Discover now