BABI NA GOMA SHA UKU

2.8K 325 120
                                    

FIKRA WRITERS ASSOCIATION

TAZARAR DA KE TSAKANINMU 🤦🏼‍♂🤦🏿‍♀

✍🏾KHADIJA SIDI & SAFIYYAH UMMU-ABDOUL

    BABI NA  GOMA SHA  UKU

Ɗago kai Saifullah yayi ya ga me Baban Sasa ya ke yi ya dai ji yana shafa masa kamar mai neman tubarrukin maraya.

"Watau Baban Sasa in a ce kowa zai dace da fitowa daga tsatson mutum irin ka ai ba sauran tashin hankali" ya faɗi bayan sun haɗa idanu.

Dariya Baban Sasa yayi yana mai jin wani sanyi na ratsa shi don ya kasa gaskata abin da kunnuwar sa su ka jiye masa.
"Nagode da biyayyarku gareni Ubangiji Allah ya baku zaman lafiya" Baban Sasa ya ce yana mai murmushin farin ciki, Aameen yayi nauyin fita daga bakin Saifullah, sai yaƙe yake yi don shi bai son a tsawaita addu'ar ma balle a dace da yinsa a bakin ƴan Aameen.

"Bari na shiga wajen amaryar in tabbatar da dagaske na kada kai" yace yana mai miƙewa.

"Ja'iri ai ni ɗin nan nine masoyinta na asali kai sai manaji" baban Sasa yace shima cikin dariya.

Ficewa Saifullah yayi don ya gaji da ɓoye halin yake ciki, neman inda zai zuba su yake yi. Bai ɓata lokaci ba ya wuce ɗakin mahaifiyar sa ba tare da ya ankara da mahaifinsa da ke zaune a ƙarƙashin bishiya ba tare yake da Baba Salihu suna tattauna abubuwa da su ka jiɓinci danginsu.
Haka su ka ɗaga kai su ka kalle shi, kallo ɗaya za ka masa ka san yana cikin tsananin tashin hankali. Shiru Baba Salihu yayi yana mai addu'a a cikin ransa yayin da Baba Anas ya tashi kamar wanda aka tsikare shi ya bi bayan Saifullah.

***
Zaune ya iske Hajiya tayi tagumi da hannunta duka biyu, tun bayan fitar mijinta ta rasa ina za ta sa ranta taji sanyi, shike nan mafarkin da tayi ba mai tsawo bane balle ta sa ran tabbatuwarsa. Ba za ta ce ga lokacin da Madina ta fita daga gidan ba.

"Yanzu Fisabilillahi kin yi abin da duk wata uwa yaci tayi kenan? Kalli lokacin da Amatullah ta nuna ba ta so kina ganin in uwarta ba ta mara mata baya ba za ta iya furtawa ne? Ku kenan Ɗanku banza ko? Ni wallahi sakin ta zanyi ku neme ni ku rasa" ya ce yana mai sakin kuka kamar wani ƙaramin yaro.

Har cikin ranta take jin kukansa tsanar Amatullah na ƙara mamaye zuciyarta. Ko Baba Anas da ke tsaye bakin ƙofa ya ji kukan Saifullah har cikin ransa har ya fara tunanin bai yi ma ɗansa adalci ba. Yana shirin shiga ɗakin ya ji hajiya ta ɗora da faɗin

"kul! Sakin Amatullah daidai yake da nawa sakin" tace cikin muryar lallashi da son tare kuka.

"What!!! Hajiya me kike faɗi ne" Saifullah ya faɗi a firgice.

"Eh haka mahaifinka ya ce, yanzu maganar da ake sai dai muyi mata gashin ƙuma, kar ka kuskura ka nuna baka son auren, mu bi ta da kisar mummuke" tace kai tsaye, hakan ya sanya Baba Anas yaye labule.

"Kin san Allah sadiya, daidai da kuka na tabbatar Amatullah ta yi a gidan aurenta sai kin yi mafiyinsa. Ba zan hana ku ba fa, duk abin da kuka shirya ku aiwatar ni kuma zan tabbatar da na aiwatar da mafiyinsa gareki" ya ce daga bakin ƙofa ya juya ya fice daga ɗakin.

Shiru duk su kayi babu abin da ake ji a falon se shesshekar kukan hajiya wanda maimakon ya sanyaya zuciyarta ƙara rura wutan ƙiyayyar Amatullah da mahaifiyarta kawai yayi..

Sun zauna fiye da mintuna goma sha biyar kafin Saifullah ya samu ƙarfin tashi ya bar ɗakin sakamakon kiran Sallah da aka yi.
Jiki a sanyaye ya bi jam'i ya koma ɗakin sa, duk wani notin tunaninsa ya kwance akan mafita kafin can da kyar ya tuna da ai dama kiran gaggawa aka yo masa ya dawo, kuma kullum hanyar da aka hau ta nan ake sauka.
Ji yayi kamar ya jawo lokaci zuwa tsakankanin magariba da isha'i da iyayensa kan zauna.

TAZARAR DA KE TSAKANINMUWhere stories live. Discover now