BABI NA GOMA SHA BIYU

2.9K 338 96
                                    

FIKRA WRITERS ASSOCIATION

TAZARAR DA KE TSAKANINMU 🤦🏼‍♂🤦🏿‍♀

✍🏾KHADIJA SIDI & SAFIYYAH UMMU-ABDOUL

    BABI NA  GOMA SHA  BIYU

Baba Anas wanda shi kan shi maganar Baban Sasa ya masa tsauri girgiza kai ya shiga yi, Jan hannun Baban Sasa cikin dabara tare da faɗin

"Baba ai ina ga zai fi kyau ka ɗan shiga ciki ka huta, ka jima a waje"
Cikin cijewa yayin da Baba Anas ke jan sa be fasa faɗin
"Ai to ka bari Anas na yi masa wankin babban riga, ɗan tselan uwa, ta Allah ba taka ba, jika ta dai na maka katangar karfe da ita....."
"Baba faɗa ba naka bane tun da TAZARAR da ke tsaƙaninsu ya ƙara ƙarfafa" Baba Anas ya ce yana jan Baban Sasa zuwa cikin gida.
Su Baba Zubairu  ma baya su ka rufawa Baban Sasa, mahaifin Amatullah ne kaɗai ya rage tsaye gaban Dee wanda ya sunkuyar da kai kamar an ajiye dutse.

Cikin sassanyar murya Baba Salihu ya
"Ban san da wani ido zan kalle ka ba, ban san da wani baki zan baka hakuri ba, ni mahaifin Amatullah na so ka da ɗiyata, ko ba don komai ba ko don kuskuren da na aikata dangane da Mahaifiyar ka a baya....."
Yanda yaga Dee ya ɗago kanshi a karo na farko su ka haɗa idanu, da yanda ya ga idanun sa sun kaɗa sun yi jajur ya sanya Baba Salihu shanye maganar sa, kana daga bisani ya furta
"Allahu akbar Allah ya jikan Yusuf da rahama, babu shakka kai jinin sa ne, ina mai fatan za ka yafe mana a karo na biyu Yusuf"
Yana gama faɗin haka shima ciki ya shige cike da danasani, dan kuwa da ya taimakawa Mahaifiyar Dee da ya girma cikin musulunci.
Allah kaɗai ya san tsahon mintocin da yayi nan tsugunne, har sai da jama'a su ka fara taruwa suna tambayar lafiya? Sannan ya tashi da kyar ya na mai goge hawayen da suka rufe fuskar shi. Har ya karasa ga motar shi kafin ya juya ya kalli kofar gidan su Amatullah, gani ya ke kamar za ta fito ta ce duk ba gaske ba ne, ganin babu ita babu alamar ta ya sanya shi buɗe motar, ya shiga ya zauna, Amma kunna motar ya gagare shi

"Amatullah shikenan yanzu na rasa ki?"

Cewar Dee ya na mai kifa kan sa bisa sitiyari yayin da maganganun Baban Sasa ke masa yawo cikin kwakwalwar kan sa.

"Amatullah..... Amatullah........."

Amatullah kuwa tana cikin tilawa saƙon ɗaurin aurenta ya isa kunnuwanta, ba ta yanke da karatun ba cigaba ta yi tana mai godiya ga Allah ba don tana son auren ba amma don ta san aure wata dama ce da Allah ya ke ba wanda ya so, ba wayon mutum ba dabararsa ke sanya ya yi aure a duniya ba, sannan matukar lokacin mutum yayi to babu shakka za a ɗaura ga kuma mijin da Allah ya riga ya tsara.
Shigowar Mahaifinta ne ya sanya ta kasa kunne Jin ya na magana da Gwaggo, ya na mai rokan Allah kariya daga dukkan sharri a gidan auren Amatullah.
"Mairo na so a ce yaron nan ya iso kafin a ɗaura auren nan, wallahi sai dai a yi duk abin da za ayi shi zan ba Amatullah." 
Amatullah ta tsinkayo mahaifinta na faɗi, ajiye Qur'anin tayi don jin wani yaro babanta ke magana akai.
"Wa kenan baban Hafiz?" ta tambaya a sanyaye don za ta iya rantsuwa ta dade ba ta ga mijinta cikin tashin hankalin nan ba.
"Wancan da Amatullah ke so" ya faɗi kai tsaye.
"Wanda Hajiya tace bamaguje ne?" ta ce a ɗan firgice.
"Ahlil kitaab ne, ya zo da shahadar sa a zuci so kawai yake a sanya masa a laɓɓansa amma ya zo an riga da an ɗaura auren Amatullah." Amatullah tana jiyo tausayi da buri a cikin muryar mahaifinta.
'Dee Yusuf ya zo don ya musulunta' ta faɗi a cikin zuciyarta tana mai jin wasu zafafen hawaye suna gangarowa kuncinta.
" Baban Hafiz mu kaddara hakan ne Alkhairi, ka manta duk wani abin dai auku a rubuce yake, Allah da kansa ya faɗi a zancensa mafi gaskiya LIKULLI AJALIN KITAAB" tace muryarta a sanyaye, Amatullah ba ta iya jin sauran zantuttukan iyayenta ba ta tashi ta jiki na rawa ta fice waje, jama'ar gidan na amarya amarya amma ina hankalin ta yayi waje domin kuwa ba ta da buri da ya wuce kanin Dee Yusuf ko da kuwa shine gani na karshe da za ta ma sa a rayuwar ta.
Sai da ta ganin motar ya dauke ma ta, sannan ta juya a hankali kamar wacce kwai ya fashewa ta shige gida. Dakin ta ta koma tana mai kuka kamar ranta zai fita, shike nan Tazarar da ke tsakanin su ya tabbata, shike nan za ta rayu da wanda ya fi kowa ganin ta a matsayin kaskantaciyar halitta. Tunanin da su ka dinga tunzura kokenta kenan. Fadi ta ke
"Innalillahi wainnailaihi ilaihi rajiun, Ni Amatullah na rasa masoyi!!!"
***

TAZARAR DA KE TSAKANINMUWhere stories live. Discover now