BABI NA TALATIN DA SHIDA

3K 302 102
                                    

 

TAZARAR DA KE TSAKANINMU 🤦🏼‍♂🤦🏿‍♀

✍🏾KHADIJA SIDI & SAFIYYAH UMMU-ABDOUL 

    BABI NA  TALATIN DA  SHIDA

"ki yafe min, ina Amatullah ita ma na yi mata ba daidai ba, a yafe ni"

Cewar Hajiya ta na mai share kwalla. Kai Gwaggo ta girgiza ta ce 

"ah ah sam ban taɓa rike ki cikin rai na ba, balle kuma Amatullah da take ɗiyar ki, Allah ya yafe mana baki daya"

"Aameen ya Allah, na gode Allah ya saka da alkhairi, ya bawa Amatullah miji na gari"

Gwaggo na mai darawa ta ce

"Ai kuwa dai Allah ya riga ya bata, sai dai fatan Allah ya ara mana rai mu sha biki"

Cike da mamaki Hajiya ta ce

"Toh madallah, Aameen, ko gun su Baban yaran nan kin ga kuwa ban ji ba"

"Eh ai dazun nan shi Baba Anas da Baban ne tare da mahaifin Amatullah su ka yanke hukuncin, idan Allah ya tabbatar nan da wata daya ma su ke so a yi auren"

Gwaggo ta karasa maganar daidai lokacin da su ka zo mararrabar bangaran na su. Nan ta yiwa Hajiya sallama tare da bata shawarar fita sabgar Saifullahi da matar sa. Ta bar Hajiya cikin tunanin ko wanene mijin da Amatullah ta samu haka?

***

Dee Yusuf kuwa tun da Mimi ta faɗa masa Amatullah ta fita idda ya ke mata naci, yayi yayi Amatullah ta dinga zuwa office din sa, ta ƙi, dan haka in dai ba shi da aji toh lalle za ka ga motar shi department din su Amatullah, ko kunya ba ya ji a matsayin shi na malami cikin makarantar. Duk in da aka gama lectures kuwa shi ne ke mayar da su gidan daliban da Mimi ta ke.

Kamar yanda su ka saba, zaune su ke dan harabar gidan Mimi, kasancewar waje ne mai sirri. Tun da ya ɗauko su daga makaranta ya lura da yanayin Amatullah, kamar ta na cikin damuwa. Amatullah ta na zaune da shi ne, Amma zuciyar ta tunanin wayar da ta yi da Baba Anas a safiyar ranar ne, maganar sa ke ta dawo mata cikin ran ta,

"Amatullah na kira ne a matsayin waliyin auren ki da Baba ya bani, ya ba ni wuka da nama akan hukunci da hidimar auren ki, shin akwai wanda kuka sasanta? Idan akwai ki sheda masa muna so mu gan shi gobe idan Allah ya kai mu, bayan magariba in Sha Allah....."

"Amatullah!"

Da sauri ya dago ta na kallon Dee da  ya kira sunan ta a karo na uku.

"Wai menene?"

"Babu"

Ta bashi amsa a takaice. Shiru yayi ya na nazari akan ta, ita kuwa rasa yanda za ta tunkare shi da maganar Baba Anas ta ke

"Maman Emjay stop behaving like a chikala! Please kin riga kin wuce wajan!"

Abin da Mimi ta ce mata kenan lokacin da ta faɗa mata yanda su ka yi da Baba Anas, ta kuma ce mata ba ta san yanda za ta faɗa masa ba. Kamar wacce ake zaro maganar daga bakin ta ta ce

"Baba Anas ya kira ni, ya ce ya na so ya gan ka gobe after magrib"

"A haba da Allah?"

Cewar Dee ya na mai washe baki, cike da ɗoki ya ce

"Halan cewa zai yi ya bani ke for better for better"

"In sha Allah"

Cewar Amatullah ba tare da ta san sanda kalmar ya fito daga bakin ta ba. Hakan ba ƙaramin burge Dee yayi ba, ya ce 

TAZARAR DA KE TSAKANINMUWhere stories live. Discover now