BABI NA TALATIN DA UKU

3.2K 506 250
                                    

Double update💕😍 in baki liƙa vote ba aje ayi, fatalwan da yawa naga.

TAZARAR DA KE TSAKANINMU 🤦🏼‍♂🤦🏿‍♀
✍🏾KHADIJA SIDI & SAFIYYAH UMMU-ABDOUL

    BABI NA  TALATIN DA UKU

Kasa zama sallahn yayi,  shigewa cikin gidan yayi kamar mai shirin tashi sama. Koke-koken mata ya ke ji zuciyar sa na ƙara tsinkewa. Haka ya lallaɓa ya shiga sasansa ya zauna a kujerar falo. Ba komi ke masa yawo a idanu ba sai yanda da hannunsa ya cusa ɗansa a cikin rami, sannan yana kallo aka maida ƙasa aka rufe shi.

Tiryan Tiryan komi ya dinga dawo masa kamar mai bita, tun daga kai ta asibiti don a cire cikin, zuwa haihuwar da tayi bai dire a ko ina ba sai inda ya sheganta ɗansa.

"Yaa Rabbi ka yafe min, Emjay ka yafe min" ya ce yana mai dafa kansa.

"Ai da bin sa ka yi ƙarshen soyayya" Ayush da tun shigowar sa take kallonsa tace tare da jan tsaki. Sai a sannan ya ɗaga ido ya kalle ta haɗe da kula da zaman ta a wajen.

"Ayush Muhammad Jamoh yaro na ya rasu" ya ce mata cikin sigar neman ɗauki, kallonsa take cikin yanayin rainin wayau, ba ta san sanda ta kece da dariyar rainin wayau ba haɗe da ɗiban dambun naman da take ci tare da kai shi baki.

"Wai dama kana da ɗa ne? Ina ce tuni ka yar da kwallon mangwaro" tace masa cikin tuna masa Kalamansa gareta lokacin da ya faɗi mata ya saki Amatullah.

"Aisha!!!"

yace cikin daka mata tsawa, ita kuma tattara kwanon dambunta tayi, ƙara kallonsa tayi ta saki dariya kafin ta shige ɗaki ta rufo ƙofa har da saka makulli.

Ɗumin da yaji na sauka a fuskar sa ne ya sanya shi sharewa, sai a lokacin ya tabbatar da kuka fa yake, kuka akan mutuwar yaron da ya ce ba nashi bane.

***
Dee Yusuf na idar da sallah ya kauce zuwa gefen Baban Sasa saboda sallah da su baba Anas ke yi.

Azkar ɗin da annabi ya koyar na bayan sallan farali yayi, cikin natsuwa wanda hakan ya zama masa jiki tun bayan da aka koyar da shi.

Fara'a sosai Baban Sasa yake yi yana mai jin ƙauna Dee na ƙaruwa a zuciyarsa, Godiya ya shiga yi ma Allah da ya sa hakan ya tabbata.

A kan idonsa Dee ya yi Raka'a biyun da zai cika na sallah, mamaki sosai ya cika Baban Sasa ganin sallah yayi a natse cikin kwarewa.

"Dan Yusuf jika na" Baban Sasa ya ce yana mai shafo shi cike da ƙauna.

"A'a fa, ka ji min tsoho, ni dai jini na kawai zaka bani" yace cikin shaƙiyanci.

"Ja'iri!!!" Baban Sasa yace yana mai kai masa duka.

A wannan gaɓan su ka idar da sallah, baba Zubairu tsam ya tashi ya nufi Dee ya miƙa masa hannu.

"Allah ya ƙara ma rayuwa Albarka, mene sunan" yace masa bayan sun yi musabaha.

"Dawood!" Dee ya amsa cikin farin ciki.

"Dauda dai ko?"

Baban Sasa ne ya tambaya. Dee na girgiza kai ya ce
"Ah ah fa tsohon nan kar ka ɓata min suna, Dawooda ne, haka sunan ya zo cikin alqur'ani, inda Allah ya jero sunayen annabawa 25 acikin suratul An'am, haka kuma suratul Saba'i inda Allah yayi magana akan falalar da ya bawa annabi Dawood, haka suratul Namli in da Allah yayi magana akan ilimin da ya bawa annabi Dawood, haka kuma suratul Saad inda Allah yayi maganar Khalifancin da ya bawa annabi Dawood a doran ƙasa, haka da sauran wajajen ma"

"Ummmmm" "ummmm"

Abin da ke fita daga bakin su kenan jin yanda Dee ke musu bayani cikin nutsuwa da tsari. Dee ya kare da

TAZARAR DA KE TSAKANINMUWhere stories live. Discover now