BABI NA SHIDA

3.1K 332 40
                                    

FIKRA WRITERS ASSOCIATION

TAZARAR DA KE TSAKANINMU 🤦🏼‍♂🤦🏿‍♀

✍🏾KHADIJA SIDI & SAFIYYAH UMMU-ABDOUL

    BABI NA SHIDA

***
Kusan mintuna talatin ta yi nan zaune ta na ta sakar zuci, kafin daga bisani ta koma ɗakin zuciyar ta cike da farin ciki.
Washegari kamar yadda ya ma ta alkawari ya na dawowa ya mata waya domin shaida mata ya dawo. Babu damar zuwa library, ɗaya daga cikin ajin su Amatullah su ka zaɓa in da su ka yi za su hadu bayan la'asar.
Amatullah ta so gayyatar Zulaikha zuwa karatun amma ta nuna mata ita ba ta da bukata, babu laifi ta na gane course din. Ranar wuni tayi tana duba lokaci. Tana idar da sallar la'asar duk da marar ta na mata ciwo alamar ta kusa fara al'adar ta, hakan bai hana ta fara shiri ba. Atamfa ta sa fara Mai adon koran ganye. Dinkin ya zauna a jikin ta ya mata cicif da ke Amatullah irin matan nan ne da Allah ya ma sura mai kyau. Wata kawar Zulaikha da ta shigo dakin wacce tun da Amatullah ta sanya atamfar ta ke bin ta da kallo ta kasa daurewa ta ce
"mashaAllah wannan jiki na ki Amatullah, gashi kullum ki na cikin hijabi abin ki dan kuwa da mazan makarantar nan zasu gan ki babu wannan hijabi ai da an sami matsala"
Kafin Amatullah ta bata amsa Zulaikha ta ce
"Da hijabin ma makaleta su ke, ba ki ga yanda Dee....."
"Zulaikha!"
Amatullah ta katseta cikin gargadi. Kafada Zulaikha ta daga ta sauke tare da fadin
"Toh baki na kanin kafata"
"Ya dai fi mi ki sauki, kun ga tafiya ta ni"

Hijabin ta ta zura, ta na jiyo kawar Zulaikha na tambayar wani Dee ta ke nufi, cikin ran ta ta ce kwa dai ji da shi. Tun daga nesa ya hango ta tafe. Sanye ya ke cikin farar shadda dinkin jamfa, tsaye  gaban ajin da su ka yi za su hadu, jingi ne jikin bango kafafun sa harde, hannun sa biyu cikin aljihun sa. ya kura ma ta ido tamkar karo na farko da ya fara ganin ta kenan. Komai game da Amatullah birge shi ya ke. Kamannin ta, kamalar ta, tafiyar ta, muryar ta........
"Salamun'alaikum"
Muryarta ce ta katse masa tunanin da  ya ke, fuskarsa cike da murmushi ya furta
"Wa'alaikum salam Mama nah, na yi kewar wannan muryar Mama nah"

Murmusawa ta yi cike da kunya ta ce
"Ka dawo lafiya? Ya hakuri kuma?"

Baki bude ya ke kallon ta har sai da ta tsargu, ta ce
"Lafiya me ya faru?"

"Murmushi? Ni kike ma murmushi Amatullah? Ahhh my ancestors will be proud of me o!!! I've made it in life!"

Dariya Amatullah ta ke sosai ta ma kasa bashi amsa. Dee Yusuf ya kara da
"Alhamdulillah Mama nah, hakuri mun gode Allah. Ina san dariyar ki, dan Allah kar ki dena"
Ganin dai idan ta biye shi nan za su tsaya ya ta sakin baki ta daga littafin da take dauke da shi tare da furta
"Our tutorial Sir?"
Ya na mai murmushi ya nuna mata hanyar shiga anjin ya na mai furta

"Yes Ma'am, Lady first"

Cikin jin kunya ta wuce gaba, ya na biye da ita su ka shiga ajin. Mutane kalilan su ka tadda ciki, hakan ya ba su damar yin karatun cikin jin dadi da kwanciyar hankali. Dee Yusuf ya iya koyarwa kwarai da gaske tamkar dama sana'ar shi kenan. Wajan awanni biyu ya dauka ya na koyar da ita har sai da aka kira magariba ya ce da ita.
"Toh Mama nah ya kamata mu tsaya anan ko? Kin ga lokacin sallah yayi"

Kai ta gyada masa alamar "eh" cikin ranta kuwa cewa ta yi ka dai je ka yi sallah, ni kam Allah ya kawo min sauki yanzu yanzun nan. Har kofar hostel ya rakata, ya tsaya su yi sallama Amatullah ta ce
"Kar na sa ka yi missing sallah, na gode gwarai"
Yana murmushi ya ke duba agogo, kana ya ce
"Ina fatan dai kin gane?"

Kai gyada alamar "eh" sannan ta kara da

"Sai Allah ya kai mu gobe?"

"Toh Mama nah, sai anjima"

Sai da ta tabbatar ya tafi sannan ta shige hostel zuciyar ta cike da annashuwa, da a ce Dee Yusuf ne Malamin su ai da ba haka ba.

***
Bayan sati biyu, zaune su ke a ajin da yan Agric Education ke ɗaukan darasi a can sashin horar da malamai (Faculty of Education), Jakanta ne su ka sanya marabi tsakaninsu, bayanin Bond yake mata yadda ba a taɓa mata ba, fahimtarsa take cikin haddacewa. Kallonsa ta yi tare da fadin
"me ya sa ka zaɓi anatomy maimakon chemistry? Ban taɓa ganin wanda koyar da chemistry ya ma kyau ba sama da kai"
Murmushi ya bi ta da shi, sanyin muryarta na ratsa shi.
"Ni kuwa menene sirrin muryar nan taki, zan so jin sa yana mai rera waƙa" yace yana basar da tambayar da ta yi masa.
"Ayya mana Yusuf, maimakon ka so jin ayoyin Allah da muryar"  dariya yayi cikin basarwa ya ce
"Kuma fa, yauwa dama akwai abin da nake so na fada miki" ya ƙarasa cikin tattaro duk wani natsuwa na shi, nan gabanta ya shiga faɗi cikin sauri, bata shirya ma jin maganar ba duk da ya daɗe yana  cewa za su yi, kullum ya ce sai ta kawo dalilin fasawa yau ba ta san me za ta ce masa ba.
"Uhmm ina jin ka" tace masa, duk da ta san zancen bai wuce na tona asirin zuciyarsa wanda ƙwayar idanunsa sun daɗe da tonawa.
"Amatology 10CU"aka ce daidai san da ya ɓude baki da niyyar magana.
Hamza ne ya bayyana gaban su, sanye cikin riga mara hannu da wando wanda be kai har kasa ba. Amatullah ya tsurawa idanu, idan ya san da Zaman Dee Yusuf be nuna alama ba. Cikin kokarin boye rashin jin dadin ganin sa Dee ya ce
" Amatullah meet Hamza, aminina" Yana mai murmushin yake, Hamza kuwa tuni ya gano rashin jin daɗin ganinsa da Dee ya yi.
Zama tsayuwa yayi a kujerar da ke gabansu, kallon Amatullah yake na ƙurilla wanda har hakan ya saukar mata da rashin natsuwa.
"Malam tashi mu wuce dama mun gama tutorial ɗin yau, sai mun yi waya mamanah" ya faɗi cikin ɓacin rai, yafi kowa sanin halin abokinsa Hamza, ko kara aka ɗaura ma zani in dai zai samu dama toh sai ya kwance, hakan na daga cikin dalilin da ya hana masa ganin Amatullah duk yadda ya so yi.
A ɓangaren Hamza kuwa ayyanawa ransa mallakar Amatullah a shimfiɗarsa yayi ko da hakan na nufin ɓata duk wani alaka tsakanin sa da Dee Yusuf.
Ba a san ransa ba, haka yana ji yana gani su ka yi sallama da ita, yau ko rakiya ba ta samu ba, nan ya bar ta, ya ja Hamza su ka fice.

***

"wa ya faɗa maka inda nake?"  Dee Yusuf ya samu kansa da faɗi bayan sun yi tafiyar kurame na dan wasu mintoci
"Facebook" ya faɗi yana dariyar ƙeta, "Baba ashe babbar Haja ka samu shi yasa kake ɓoyeta, oboi fully loaded ina ma zan ganta without Hijab" ya ƙara faɗi yana mai kwatanta surarta da hannunsa. Baƙin ciki sosai ya cika Dee Yusuf har ya rasa abin da zai ce. Kafin daga bisani ya tsaya cak, gaban Hamza ya sha, ya na mai daura hannu bisa kafar Hamza ya ke kallan sa ido cikin ido ya furta
"Hamza Amatullah mace ce mai daraja a guna, ina rokan ka arziki ka tauna harshen ka kafin ka furta lafazi dangane da ita, na yafe ma ka yanzu, Amma na rantse maka da Allah ka kuskura ka sake sai na bata ma ka!!!!!"
Bai ƙara komi ba ya wuce ya barshi a nan, shi kan shi Hamza yayi mamakin Amininsa, kamar yadda Dee ya cika da mamakin kansa, wai shine da kishin mace har haka.
Addu'a ya shiga yi bayan ya zauna a ɗaya daga cikin kujerun simintin da ke gaban hostel ɗinsu na Danfodio.
"Yaa Ubangiji kar ka sanya Amatullah juyan baya bayan na yaye mata lullubin da ke tattare da ni.
***
Tun bayan da ya amsa kiran Baban Sasa yake cikin ƙunci, gaba ɗaya tunaninsa ya ɗauke akan musababbin kiran.
" In ba so kake ƙasa su rufen ido ba ka dawo a ɗaura aurenku" kalaman baban Sasa su ka dawo masa kamar a lokacin ya ke faɗi masa.
"Watau wannan bagidajiyar ba ta ji magana ba kenan" ya fadi ya mai jan tsuki, da aka aka kira su jirgin su zai tashi. Jiki a sanyaye ya Mike ya isa inda ake bukatar su, ba don soyayyarsa da Baban Sasa ba babu abin da zai sa ya koma Nijeriya a wannan lokacin.
Duk kwanakin da ya ɗauka kafin isowa Nijeriya bai ga daɗewarsu ba illa ma sauri da ya masa, hakan ya sa da ya tsinci kansa a kofar gidan Jamoh kamar yadda ake kiran gidan ya ji gaba ɗaya ya tsani kasancewarsa ahlin gidan.
An yi murna da zuwan sa, tarbo na musamman mahaifiyar Amatullah ta yi masa wanda hakan al'adar ta ne tun yana ƙarami.
Sai da ya ci yayi Nak sannan ya fara ganin gari, da yake shi ba mai wasu abokai bane tun asalinsa balle yanzu da yake ganin zama cikin masu ƙaramin tunani na nufin koma baya, duk da ma'anar ƙaramin tunani a wajen Saifu daban yake da saura.

***
"A sanya biki nan da sati biyu, mu ne dangin amarya mu ne dangin ango"  fadin baba Zubairu kasancewarsa babba gaba ɗaya a gidan ya sanya ba wand ya ja da zancen sa.
"Kai Saifullah sai ka samu lokaci ka je ka ɗauko kanwar taka don ta san halin da ake ciki" Baba Anas mahaifi ga Saifullah ya fadi. Shi dai Saifullah bakin cikin duniya ya taru ya cika masa ƙirji, bai  ce komi na sannan bai iya gardama ba ya tashi ya mike. Bai jira wani ɓata lokaci ba samaru ya wuce.
Amatullah na zaune tana jiran kiran Dee Yusuf inda ya kan ce da ta fito zuwa koyon karatu. Karan wayarta ne ya dawo da ita daga duniyar tunani, ganin lambar a kulle ya sanya ta saurin ɗauka don a tsammaninta Dee ne bai network ya sanya haka nan.
"Ki fito wajen basket ball din ku" aka ce haɗe da kashe wayar, kamannin muryar da na mahaifansu ne ya sanya ta tunanin ko daga gidan su ne.
'kila Baban Sasa ya samu cikawa' tace tana mai share hawayen da ya gangaro mata na rashin madafa. Cikin sauri ta ja hijabin ta ba tare da ta damu ta dubi kan ta a madubi ba bare ta dan gyara maikon da ke fuskar ta, ta fice fuuu don ba za ta so abin da take tunani su tabbata ba.

Isar ta wajan basketball ta tsaya cak ganin wanda ke tsaye bakin mota, duk da dai baya ya bata hannun cikin aljihu bai sa ta kasa gane shi ba, ba ta san lokacin da ta fara tasbihi ta na mai neman tsari daga ubangijin ta, fad'i ta ke

"Allahumma ajirni fi musibati......."

TAZARAR DA KE TSAKANINMUWhere stories live. Discover now