BABI NA GOMA

3K 358 104
                                    

FIKRA WRITERS ASSOCIATION

TAZARAR DA KE TSAKANINMU 🤦🏼‍♂🤦🏿‍♀

✍🏾KHADIJA SIDI & SAFIYYAH UMMU-ABDOUL

    BABI NA  GOMA

Kamar saukar aradu haka maganar Dee ya sauka kunnen Hajiya, wacce ta yi ƙaryan zagawa bayi amma ta ɓige da zuwa soro domin ganin wannan saurayi da Baba Anas ke ta zuzutawa, wato wanda aka zaɓa akan Saifullah.
"Sanadiyyar abin da ya sami mahaifiya ta, Ni da ke Amatullah kowannan mu za mu iya yin addinin mu, Wallahi babu abin da zai hana ki musuluncinki, ki dubi girman Allah ki amince da aurena... "
Kalaman da ke mata yawo cikin kwakwalwar ta kenan, musammam jin Dee ya ce
"Wallahi babu abin da zai hana ki musuluncinki"

"kenan shi ɗin ba musulmi bane"
ta faɗi tana mai toshe bakinta kamar ba ta son wani ya jiyota. Matsar da kunnenta tayi tana so ta jiyo wani abin da zai tabbatar da zarginta. Babu abin da ta jiyo sai shesshekar kukan Amatullah, ta tsaya kusan mintuna uku tana jiran jin abin da za ta ce amma shiru sai kukan da take yi. Hakan ya sa ta juya don ta koma cikin gida jikin ta na rawa tsabagen daukan gulma.

Amatullah kuwa kuka ne ya ci karfin ta har ta kasa magana. Tausayin kan ta da shi Dee ta ke ji domin kuwa ta san Dee haramtacce ne a gare ta duk kiyayyar ta da Saifullahi.
"Amatullah ki bar kuka ki amsa min, za ki aure ni?"
Amatullah ta girgiza ma sa kai alamar ah ah. Komawa yayi ya sake zaman dirshen a kasa. Kamar mai rada ya furta
"Why?"

"Saboda TAZARAR DA KE TSAKANINMU"
Ta mayar masa cikin yanayin muryar da ya tambaye ta, ba ta gushe ba ta cigaba

"Babu aure a tsakanin mu, haramun ne a musulunci, mahaifin ka na da daman auren mahaifiyar ka ko da kuwa ba ta canza addini ba, domin kuwa shi namiji ne, ni kuwa ban da wannan damar, ba zan iya auren ka ba..."

"Saboda me ya sa? Why? Me ya sa mace ba ta da wannan damar sai namiji?"

Ya sake katse ta cikin nuna rashin gamsuwa.
"Haka shari''a ta ce, Saboda ita mace rauni gare ta, ba kamar namiji ba..."

"Ba zan cutar da ke ba Amatullah, ba zan bari a cuce ki ba, na daukar mi ki alkawarin zan kare duk wani hakki na ki a matsayin ki na ƴa mace kuma mata ta..."

"Hakkin ubangiji fa? Za ka taya ni kare shi?"
Amatullah ce ta katse shi a karo na farko. Shiru yayi yana kallon ta na wasu yan mintina kafin daga bisani ya furta
"Har da hakkin ubangiji...."

Tashi ta yi tsaye ta na mai share hawaye, shima din tashi yayi idanun sa bisa fuskar ta. Kallonsa ta ke cikin yanayinda kwayar idanun ta su ka kasa ɓoye tsananin soyayyar da ta ke ma sa, haka shima haka na shi soyayyar ke bayyane cikin kwayar idanun shi. Cikin sassanyar murya ta ce
"Ina so ka fara daga yanzu, ka taya ni kare hakkin ubangiji ta hanyar fita daga cikin rayuwa ta"

"Amatullah!!! "

Ya furta a hankali amma cikin tashin hankali. Hannu ta daga ma sa

"Please........ don't make it more difficult for me, addini na ya fiye min duk wata soyayya da na ke ma ka ko ka ke min, idan har yanda ka ce gaskiya ne, stay away from me"

"Idan kuma na karbi addinin na ki fa?"
Baki bude ta tsaya ta na kallon shi domin kuwa tabbas tambayar na sa ya mata bazata, nisawa ta yi, kana ta ce
"Idan za ka karɓi addinin ba dan ni ba, ba dan soyayya ta ba, domin soyayyar dan adam abu ne mara tabbas, idan za ka karɓa domin soyayyar Allah da manzon sa, Ni ma na ɗaukar maka alkawari ba zan cuce ka ba, ba zan bari a cuce ka ba, Zan kare duk wani hakki na ka a matsayin ka na miji na...."

Ta na gama fadin haka ta juya ta fice da sauri. Nan ta bar Dee tsaye kamar mutum mutumi, yayinda zuciyar sa ke radadi, cikin ran sa kuwa fadi ya ke lalle Allah ya jarabce shi da soyayya mafi zafi a rayuwar shi.
Hajiya kuwa ko da ta koma kasa zama tayi, magana na cin ta, ko da ta tuna da Karin maganar na da bahaushe kan ce zafi-zafi a kan daki ƙarfe tuni ta aje tsintar shinkafa sai ga ta cikin dakin Baban Sasa
"Baba Ka yi min rai ka hakura da haɗin nan" ta ce cikin shesshekar kuka har da majina.
Ba Baban Sasa kaɗai ba har Baba Anas da Baba Mahmud da ke zaune tare da mahaifin su sai da su ka kaɗu.
"Sadiya na daɗe da sanin kina da hannu a rashin hankalin Saifu, ki fita ido na, yarinyar da bakwa so ai ta samu kamilallan miji mai tarbiyya" Baba Anas ya tare ta. Kallon matarsa yake zuciyar sa na kimtsa masa abubuwa da zai yi amfani wajen yin maganinta da ɗanta.
"Baba ka ji wai kamilalle, ina kamala a jikin bamaguje, ni dai Baba ka yi min rai kar ka aura ma ɗana sauran maguzawa ka san zina ce kalar ta su soyayyar"
tace tana ƙara sakin kuka mai tsuma rai, gaba ɗaya ta birkita tunaninsu, kallon ta su ke yi don babu wanda yayi tunanin abin da za ta ce kenan. Ganin an tsaya kallonta ne ta sake faɗin
"Rantse mata fa yake in sun yi aure za ta cigaba da musuluncinta..."

TAZARAR DA KE TSAKANINMUWhere stories live. Discover now