BABI NA ASHIRIN

4K 382 132
                                    

TAZARAR DA KE TSAKANINMU 🤦🏼‍♂🤦🏿‍♀

✍🏾KHADIJA SIDI & SAFIYYAH UMMU-ABDOUL 

    BABI NA  ASHIRIN

Sannu sannu har mun yi sati goma a cikin wannan tafiya tamu, godiya ta Musamman ga duk wanda idonsa ke kan saƙon nan, mun gode, Saifullah da Amatullah na gaida ku cikin kwando. Dee Yusuf da mimi na muku fatan Alkhairi.. 

Baban Sasa na jiran ku kai masa farfesun Hanta. 

Muna ƙaunar ku Fisabilillah. 

Umdija😍😘🌹

***

Jan jiki ta yi zuwa ɗaki bayan ta nemi abin da za ta riƙe hanjinta da shi. Allah ya isa kuwa ta masa ya fi sau a ƙirga don ba ta ga dalilin da zai sa ya haramta mata sa hijab ba, haka kawai ta dinga tallan jikinta gareshi kamar wacce ba ta da kishin kanta. Da ire-iren tunanin nan ta kammala cin abincin, miƙe kafafu tayi ta jingina nan ma wani sabon bacci yayi awon gaba da ita. 

Hayaniya ya tayar da ita sa'ilin da yan gidansu su ka iso wainda mafi akasarinsu innoninta ne, bayan ta gaida su, wasu na mata tsiya ne su ka sanya ta je ta yi wanka saboda masu shigowa ganin amarya. 

Atamfarta ta sanya ɗinkin riga da skirt, sosai ɗinkin ya zauna a jikinta, golden color din da ke jikin atamfar wanda ya sakaya cofee da peach ya fito da kalarta tare da bayyana madarar kyawun da ta mallaka. 

Hijab golden ta ɗinka ma kayan har ta ɗauko za ta sanya 

"A matsayina na mijinki, na haramta miki sanya hijabi a cikin gida" take wasu hawaye su ka zubo mata,  jujjuya hijabin ta ke a hannun ta hawayen ba su daina zubar mata ba, takaicin ta yanda cousins ɗinta maza ke kaikomo a cikin gidan suna taimakawa wajen ƙara kimtsa gidan. 

"Ga wannan ki yafa" cewar innarta Aisha, kallon gyalen ta yi, kamar ta ce A'a amma shakkar Innar tata da take yi yasa ta amsa. Ana faɗin matar soja sojace bata yarda ba sai akan innarta Aisha, don in ta rikide musamman akan abubuwa da ya jiɓinci ado da kwalliya sai ka rantse wani hafsin soja ne a fagen yaƙi. 

Gyaran da aka ma fuskarta da yanda ta yane jikinta da gyalen ya fito da ita ainun. 

"MaashaAllah! MaashaAllah!!"

 kawai ake faɗi, nan sai ta hau Saman gado fuskarta lulluɓe da gyalen amma tana iya hango su. 

"Ai ni jiya hankali na ya ɗauke wajen hidimar yaya mairo, a ce amarya da hijabi, kai ke kuwa izalarki ta yi yawa wallahi" inna Aisha ta faɗi tana mai yaba kyawun yar tata. 

Zamanta a legas ya sanya duk wani darun da aka yi ba ta da labari, itace ke bi ma Goggo Mairo, sun yi aure da mijinta tun tana shekaru goma sha huɗu shi kuma an yaye su a depot din zaria. Allah cikin ikonsa ya haɗa mijin nata da oga nagari ya masa hanya ya tura sa makarantar horar da sojaji ta NDA yayi shekaru  biyar ya fita da anini. Yanzu har ya kai ga Jan wuya a aikin soja. 

"Ai yaya indo ni na rasa kamun jiki irin na Amatullah, su ne yan fatawar ko hoda mace ba ta sawa, amma wainda su ka san darajar mata sun san su ake kira first class ladies" faɗin Inna Hafsatu kanwar su goggo mairo ce, hakan ya sanya yan uwan hajiya da su ka shigo fita cikin sanyin jiki, da sun shigo suna musu yatsina ne. Suna fita kannen Goggo Mairo su ka sanya shewa.

Haka su ka yini suna gyara da taya Amatullah zama sai da aka kira magariba sannan duk su ka watse a gidan, suna mai masu fatan Alkhairi. 

Kamar juya Amatullah ba ta jira shigowar Saifullah ba ta kulle ɗakinta, sai dai ta iya canza kaya zuwa na bacci kafin ta bi lafiyar gado.

TAZARAR DA KE TSAKANINMUWhere stories live. Discover now