BABI NA GOMA SHA DAYA

3.2K 350 160
                                    

FIKRA WRITERS ASSOCIATION

TAZARAR DA KE TSAKANINMU 🤦🏼‍♂🤦🏿‍♀

✍🏾KHADIJA SIDI & SAFIYYAH UMMU-ABDOUL

    BABI NA  GOMA SHA DAYA

Shigowa ya yi don amsar abincin dare duk da hakan ba al'adarsa bace amma yanayin da yake ciki ya isa ya hana masa cin abin da yafi soyuwa a gare shi da dare. Har yayi hanyar ɗakin gwaggo Mairo kamar yadda ya saba sai ya canza don baya fatan abin da zai haɗa shi da bagidajiyar yarinyar nan, ya ayyana a ransa.

"Amma dai an yi sakarai wahalalle ya rasa wacce zai ci burin sakawa a motar nan sai bagidajiyar yarinyar nan" ya fadi ya na mai dafa bango jin wani abu ya tokare shi a ƙirji.

"2008 Suzuki SX4 ce fa" ya faɗi tunawa da cewa a ƙarshen shekarar da ta gabata a ka fitar da motar, yayi maitan mallakar ta amma shi a karan kanshi ya san motar ta girmi duk wani ahlin gidan Jamoh a wannan lokacin, sai gashi wacce ya fi gani a kaskantaciya da bai yi tunanin mamallakin keke zai kalle ta da soyayya ba mamallakin dream car dinsa ya zo afujajajan idanunsa dauke da tsantsan soyayya gareta.

Sai da ya kwashe kusan mintuna goma sha biyar yana maida numfarfashi da tattaro natsuwa kafin ya karasa  cikin ɗakin mahaifiyar sa
.
"Ku tashi ku bamu wuri" hajiya ta faɗi ma kannensa ganin suna zaune ba mai shirin fita duk da ba wai don sun saba fita bane in ya shigo ɗakin.
"Saki Ranka yayansu, ashe yaron nan da Amatullah ke so arne ne, in faɗa  maka ina ji na yi wuf na iske baban Sasa na faɗa masa" tace cikin raɗa, fuskar ta cike da annuri, rasa me zai ce mata yayi, ya rasa yanayin da ya tsinci kansa haka yake kallonta sheƙeƙe bai ga ta in da tayi gwaninta ba balle ta birge shi.

"Kin ga matsalar shegiyar al'adar nan taku ta banza wai kunyar ɗan fari ko, ni na ce miki ina son Amatullah da har za ki taya ni kishi" ya ce yana kokarin saita fushi da ya ji yana taso masa da ga kasan zuciya.

'watau ba ma musulmi bane balle a ce shima ustaz ne yana son ustaziyya' zuciyar sa ta dinga nanata masa.

"Na ga dai duk gidan nan babu wacce ta kamo kafafunta ne a haɗuwa boko da islamiyya, in ka aureta zan tabbata na zarce duk wata mace a gidan nan" ta katse masa tunani, magana take ƙasa-ƙasa gudun fitar da wani gun, duk da ta san ana faɗin bango na da kunnuwa.

"A tunanin ki hajja zan auri wacce ta taso a cikin manyan biranen ƙasar nan ne balle kuma wacce ta taso a cikin zaria, matan da ba su san komi ba sai lulluɓe jiki kamar sauran kuturta. Hajja ki min jagora kar a aura min bagidajiyar can, zan auro miki wacce ta haɗu, wacce duk ta wuce sai an saki baki an bi ta da idanu, ki amince min Hajja" ya ƙarasa rauni cike da muryarsa, shiru ta yi ta lula mafarkin ido biyu, babu abin da ta ke hangowa sai surukar da sanadin ta za ta dinga zuwa haji duk shekara.

"Amma kuma mahaifin ka fa? Ɗazu fa kiris ya kwaɗe ni gaban su Baban Sasa" tace sa'ilin da ta tuna babu wanda zai kawo masu cikas sama da shi.

"Hajja matarsa fa kike, kiyi amfani da damar nan" yace mata kai tsaye. Tunawa da tayi da Madina, kanwar mijinta kuma aminiyarta wacce ba ta san wa yafi tsanar Goggo Mairo ba cikin su biyun.
"Zan nemi madina gobe inshaAllah, duk abin da ake ciki za ka ji" da haka su ka yi sallama, ya wuce ɗakin sa ya rufe, baya ko fatan abin da zai sa ya haɗu da mahaifinsu hakan ya sa ya kuduri niyyar ba zai fita sallan asuba ba.

***

Kwance ya ke bisa gadon sa, duk yadda ya so ya cire tunanin Amatullah da maganganun da su ka yi abin ya gagara. Hamza yayi kokarin jan shi su fita amma hakan ya ci tura, rokan sa yayi da dan Allah ya rabu da shi sam ba ya jin dadi dan haka ba ya san damuwa.
Sanye ya ke cikin farin singileti da gajeran wando. Tun yana juye-juye har ya tashi yana mai lalubar wayar shi da tun dawowar shi daga wajan Amatullah ta ke kashe. Kunna wayar yayi, idanun sa kan fuskar wayar in da agogon kan wayar ya nuna karfe goma sha daya da rabi na dare, lalle ya daɗe kwance domin kuwa Allah kaɗai ya san awanni nawa ya ɗauka nan kwance. Ba tare da ta san abin da ya ke ba ya tsinci kan sa ya na mai danna number Amatullah, ta yi ringing har ta katse ba ta ɗaga ba. Ajiyar zuciya ya saki, yayin da ya furta

TAZARAR DA KE TSAKANINMUWhere stories live. Discover now