BABI NA TALATIN DA ƊAYA

4.2K 420 189
                                    

TAZARAR DA KE TSAKANINMU 🤦🏼‍♂🤦🏿‍♀
✍🏾KHADIJA SIDI & SAFIYYAH UMMU-ABDOUL

    BABI NA  TALATIN DA ƊAYA

Gaba ɗayansu bin sa su ka yi da kallo har ya fice, nan ne Baba zubairu ya ɗan muskuta ya ce

"Nifa ban ga laifin yaron nan ba, na tabbata da ace shi mu ka gani a wannan hali ba zamu taɓa waiwayensa ba balle mu taimaka masa, bayan mu ne addininmu ya koyar da mu kyautatawa" yace yana mai kallon ƙanensa zuciyarsa cike da Nadama.

"Gaskiya ne, don wallahi ba ruwan bambancin addini a kyautata mu'amala ko sauke hakkin makotaka. Yanda ya wajaba a kan musulmi haka ya wajaba akan wanda ba musulmi ba,  sannan a ko ina cin fuska haramun ne" Baba Anas ya ce yana mai goyon bayan Baba Zubairu.

"Amma kuma aka ce kada mu riƙe su aminai" Baba hamza ya ce a ɗan hasale..

"Eh an ce kada ka rike su aminai don za su cutar da kai amma ba a ce kada ka rike su da amana ba, kun manta zamanin Annabi SAW sau da yawa kafirai na zuwa da niyyar kashe shugaban halitta amma su ɓige da musulunta ba su kaɗai ba har mutan garin su, duk saboda kyakkyawan mu'amala da musulunci ya koyar da ayi ga kowa ciki har da wanda ba musulmi ba." Baba Anas ya ce kai tsaye.

" Ni dai babu wani kame kame da za ku min, kun ci amanar Babanmu, kun sani sarai yanda yake ƙyamarsu don su ɗin najasa ne, da kuke maganar na siya ba a sanin ko nawaye me yasa kullu. Muke addu'a muke faɗin RABBANA LAA TU'AKHIZNA INNA SINA AU AKHƊA'ANA toh shi Ubangiji ai mai Rahma ne, ba zai kama mu da laifi ba amma kuma yanzu fa? Haba! Haba!! " faɗin Baba Hamza ransa a ɓace.

" Kunga matsalar Bahaushe kenan, shi a duniya gani yake babu wanda ya kai shi zama kusa da Allah, haka kuka dinga tada jijiyar wuya lokacin da ɗan wajen madina ya auro Gara, a bakin bahaushe za ka ji yana kaskantar da wani jinsi in dai ba yarensa ɗaya ba da kiransa ƙabila.
Shi bahaushe shi dai wanda bai cikata farillansa ba amma a duniya ba wanda yake nuna wa Yatsa sai wanda ba musulmi ba, shi ne zai kalli malamin addini ya kira shi da tubabbe matukar daga baya ya musulunta.
Da haka manzo SAW yayi da ya tara manyan sahabbai da yake da su? don dukkansu tubabbu ne a fassaran bahaushe." Baba Salihu ya faɗi kai tsaye.

" Shine ai nagani, gashi kiri kiri wanda kuka zaɓa akan arnen yana shirin kashe muku mahaifi. Na gwammace a ce Arnen can ne ɗa na in dai zai tuba ya musulunta akan wancan sakaran" Baba Anas ya sake fadi cikin takaici.

"Ko me zaku ce muna dai jin ku ne kawai don ba zai wanke cewa baku kyauta ma babanmu ba kunci amanarsa ba ko kaɗan ba, Jinin Arne fa ke gudana a jikin Baba, mutumin da yayi rayuwar sa kaf cikin musulunci" Baba Mahmuda da tun farko bai maganta ba ya ce yana mai tsananin jin takaici.

Tun da suka fara magana Baban Sasa ya dawo hayyacin sa, idanunsa a rufe sai yake jin zantuttukan su kaf a kunnensa inda yake ji kamar mafarki yake yi, so yake ya fahimci me su ke faɗi amma ya gagara, idanun sa sun masa nauyi dan haka ya kasa bude so, bubu abin da ke motsi jikin sa face yan yatsun hannun sa. Baba Idris wanda tun da aka fara magana bai tamka mu su ba, shi ne ya lura da halin da ya ke ciki. Cikin hanzari ya tashi ya na fad'in

"Ina ga fa Baba ya motsa, yi maza kira likita! Baba Muhammadu ne ya fita cikin sauri sauri gudu gudu, in da gaba ɗayan su suka zagaye shi  suna masu faɗin

"Sannu Baba! Allah ya tashi kafadar ka"

***

Faɗin Damuwar da Amatullah ta shiga ba zai misaltu ba, don gaba ɗaya kanta ta ba laifi don gani take damuwar rashin komenta ne ya kwantar da Baban Sasa.
Addu'a kam ta yi sosai akan ya samu lafiya.

Zaune take tana tunanin zuwa shika Amma wa zai kai ta? Lokaci take kallo tare da tsimayen kiran sallan la'asar domin ta ba da farali. Ɗumi ta ji ya fito mata wanda ta dan razana tare da gyara zama yayin da taji fitowarsa a karo na biyu.

TAZARAR DA KE TSAKANINMUWhere stories live. Discover now