[11/13, 6:10 PM] Hassana D'an Larabawa🥰: 💔💔💔❣❣❣💔💔💔❣❣❣
*SANADIN HOTO*
*TAREDA ALKALAMIN HASSANA DANLARABAWA*✍✍✍
*page 7*
Isarmu qasa me tsarki keda wuya, muka fara abinda yakaimu wato ibada, a madina munshiga rauda, nayi farinciki mara misali da kukan farin ciki ganin gani ga maaiki *S A W* nayi addu'a meyawa, munyi ziyaza iri iri irinsu (masjid quba) da masjid qiblataini da kuma dutsennan me tarihi wato (uhudu) da dai sauransu.
Kwananmu takwas a madinatul munawwara, sannan muka shirya dan tafiya makka, mukaje masallaci mukai bankwana mukai adduar Allah yasa munada rabon sake dawowa munsha kukan rabuwa da madina, saboda gari ne me dadi da sanya nutsuwa a zukata, gaskiya madina tayi ".
Bayan mundawo masaukinmu duk 'yan tawagarmu mukayi wanka kowa yasa haraminsa, mota takwashe mu muka nufi makka, a hanyar madina zuwa makka aka tsaya a miqatin mu wato (zul hulaifa) duk muka fito muka shiga daganan kowa yayi alwala yayi sallah rakaa biyu, sannan muka dauki niyyar yin umrar mu.
Mundawo mota bayan kowa ya kammala, sannnan akajamu muka karasa birnin makka, akakaimu masaukin mu, muka ajiye kayanmu sannan muka nufi harami dan mu sauke umara , tunda muka shiga masallaci gabana ke faduwa, musamman yadda naga dakin Allah wato (*ka'aba) da idanuna muraran baa hoton 📺 TV ba, kwarjininta da girmanta, daukakarta da kyawunta yawuce misali, hawaye masu sanyin dadi suka kwararomin, naqara rike hannun aunt hameeda gamm dake kusa dani, har sai da tajuyo ta kalleni taimun murmushi.
Haka mukayi dawafin mu da sa 'ayin mu wato (safah da marwa) mu kayi sallah rakaa biyu bayan kammala dawafin mu, abayan (muqamu ibraheem) mukasha zam zam, bayan mun kammala sa 'ayi na yankewa aunty hameeda gashi itama ta yankemin gwargwadon yadda ake bukata, shikenan mun sauke umrar mu kenan, zamu koma masauki mu cire haramin mu saikuma randa zamu fita (muna) zamu sake sawa, danyin aikin hajji, dayake mu aikin hajji (tamattu 'i) zamuyi.
A kullum yinin masallaci mukeyi, wani lokacin ma kwana mukeyi, da gasken gaske addu 'a mukeyi bada wasaba, dankuwa kasamu kaje gurinnan ba batun wasa dole kadage ka fafata da addu 'a, nayiwa ya abbas addu 'a me tarin yawa, da iyayena, da 'yan uwana, da musulmin duniya baki daya,".
*(multazam*) wani gurine tsakanin hajarul aswad da kofar ka'aba, guri ne da Ba'a juyar da addu 'a, naqudiri niyyar insha Allah sainaje gurin, aikuwa Allah yabani sa 'a saida naje gurin nai addua me yawa, da hawaye a idona nake adduar Allah yabani miji nagari, ina nufin ya abbas, domin araina inajin shine zabina kuma zabin Allah, wannan waje bakowa kesamun damar isa inda yakeba, saboda cikowar mutane da turmutsutsu, amma nidai Allah yabani sa 'a naje, kuma nayi gdy ga rabbil izzati sarki mabuwayi.
Addu 'a dai iya yi munyi, sai fatan Allah yakarbi ibadunmu,.
Ran bakwai ga wata aka debemu aka kaimu (muna) muka kwana takwas gawata aka kwashemu sai filin arfa da daddare muka kwana muka wayi gari a filin arfa, wayyo ranar arfa rana me dunbun daraja da falala, mundage munyi adduo 'i sosai, munroki Allah bukatunmu dana musulmai, nan ma bangaji da rokarwa kaina miji nagari ba, wanda aurensa zai zamarmin alkairi.
Saida rana ta fFadi,magriba tayi sannan mukabar filin arfa muka wuce (muzdalifa) anan mukayi sallah magriba da isha, sannan mukadan yi addua muka kwanta, bamuyi wani bacci meyawa ba, akayi assalatu muka tashi mukai sallah sannan muka tsinci tsakuyoyin yin jifan shaidan, muka nufi gun jifa, bayan munyi jifanmu a ranar muka koma makka mukayi dawafil ifada, wato dawafin aikin hajji kenan, mukai saayi muka yi aski, sai yanka, shikenn mun sauke aikin hajjinmu, saikuma muka koma muna a ranar kan rana tafadi domin karasa kwanakin yin jifa.
YOU ARE READING
SANADIN HOTO
Historical Fictionlabari ne da aka ginashi akan tsabtatacciyar soyayya ,wadda tafara tun daga yarinta ,dab da burin masoyan zai cika k'addara ta afka musu dalilin sanadin hoto ,kubiyoni Dan sanin shin k'addarar tana kaisu ga auren juna ko kuwa ........!?