[1/3, 7:24 AM] Obama: 💔💔💔❣❣❣💔💔💔❣❣❣
*SANADIN HOTO*
*TARE DA ALK'ALAMIN HASSANA D'AN LARABAWA*✍✍✍
*page 141 to 145*
*MASU GANIN KAMAR NA ZAB'I B'ANGARE GUDA D'AYA ,TO BAHAKA BANE ,BANA TEAM KAMAL ,KUMA BANA TEAM ABBAS ,NI ATSAKIYA NAKE BAN FIFITA B'ANGARE D'AYABA ,DA MASOYAN KAMAL DA MASOYAN ABBAS KUMA DUK D'AYA KUKE AGURINA ,DOMIN DUKANKU KUNA NUNA SOYAYYARKU NE AKAN RUBUTUNA ,HAR KUKE TUNANIN NAYI K'OK'ARIN DA YA KAMATA A JINJINAMIN TAMKAR BA LITTAFINA NA FARKO BA ,TO NIMA INA JINJINA MUKU DA KUKE FAHIMTAR SAK'ONA ,COMMENT D'INKU KAD'AI YASA NA FAHIMCI KUN GANE INDA NA DOSA KUMA KUN FAHIMTA ,NAGODE MUKU SOSAI ,WALLAHI INAJIN DAD'IN KASANCEWA TARE DA KU MASOYANA,HASSANA D'AN LARABAWA NA TARE DAKU A KODA YAUSHE*🥰🥰🥰😍😍😍😘😘😘💃💃💃
*DEDICATED TO ALL ONLINE WRITERS ,KUNA K'OK'ARI MATUK'A ,ALLAH YAK'ARA HAD'A KANMU YABAMU LAFIYA DA ZAMA LAFIYA*🤝🤝🤝🤝
"""""""""""""" Gabana yayi wata muguwar fad'uwa ganin yadda aunty hameeda ta zazzaromin ido tana tambayata .
"Lallai nayi b'arin zance Ashe bansaniba, nikuwa wane tsautsayin ne ya kaini ?nai wuri wuri da ido ina Sosa kai nakasa magana".
"Aunty ta d'aure fuska tana hararata tace "
"Yanzu ke safah da bakinki kike fad'amin wannan maganar saboda rashin kunya da rashin mutumci ?jahila ce ke kome ?da iliminki na addini da hankalinki da tarbiyyarki ,amma Dan toshewar basira kidinga wahalarda mijinki ??
" kiji tsoran Allah !ki tabbatar kika mutu a wannan halin wuta zaki tafi wallahi !kinsan matsayin miji kuwa ?yanzufa kamal gaba yake da Abba da mama agunki !aljannarki tana k'ark'ashin k'afarsa wallahi saiya d'aga zaki shigeta ".
"Allah da kansa yace "
"da zan umarci wani yayiwa wani sujjada ,to Dana umarci mace tayiwa mijinta sujjada".
"Saboda tsananin girman miji agun matarsa" .
"Wallahi ,wallahi ,wallahi ,idanma kamal ne bakyaso shi Allah ba ruwansa ,zai tuhumeki akan rashin biyayya da tauye masa hak'k'i da kikeyi ,bantab'a ganin yarinya me taurin kai irinkiba safah ,akanki aka fara rashin masoyi ne ?anyi soyayya wadda tafi taku kuma anrabu ancigaba da rayuwa kuma !to kisani inma tunanin Abbas kikeyi zunubi kike kwasarwa kanki ,Dan yanzu ke matar aurece" .
"Ba kowace macece tayi sa'ar miji tamkar kiba, mazan yanzun da basuda tabbas ,suna wulak'anta mata ,suna dukan mata ,kullum kikaje hizba zancen kenan case tsakanin mata da miji ,amma ke Allah yadubeki yabaki miji nagari Wanda yahad'a komai da komai babu aibu ,kamal ga kyau ga kyawun zuciya ,ga kyauta ,ga hak'uri da kyautatawa ,ga sanyin hali da iya soyayya !bayan wad'annan abubuwa me kikeso kuma ??
"Nasan zakice rashin so da kuma kasancewarsa me mata !to wannan ba hujja bace !wallahi idan zanyi rantsuwa babu kaffara nasan ko bakyason kamal to kuma bakya k'insa ,nasan yadda kike girmama kamal abaya da irin yabonsa da kikeyi da bakinki kan cewa mutum ne nagari me kyautatawa mutane ,ko bakya sonsa a yanzu nangaba zaki soshi ,domin aure yafice wasa safah ,karki jefa kanki halaka a kan mummunar ak'idarki da ba zata amfana miki komaiba duniya da lahira ".
"Allah ya jarrabi kamal da mata Mara kirki me sab'amasa akoda yaushe ,kamata yayi ace yadda Allah yayi masa tukuici dake kekuma ki kyautata masa ,ki riritashi ,ki nunawa jamila kurenta na wahalardashi da takeyi ,ki rungumi mijinki ko kyasamu tsira agurin mabuwayi sarki Allah ,musamman da ya kasance tauraruwarki na k'yalk'yali a zuciyar kamal d'in.
YOU ARE READING
SANADIN HOTO
Historical Fictionlabari ne da aka ginashi akan tsabtatacciyar soyayya ,wadda tafara tun daga yarinta ,dab da burin masoyan zai cika k'addara ta afka musu dalilin sanadin hoto ,kubiyoni Dan sanin shin k'addarar tana kaisu ga auren juna ko kuwa ........!?