[1/3, 7:24 AM] Obama: 💔💔💔❣❣❣💔💔💔❣❣❣
*SANADIN HOTO*
*TARE DA ALK'ALAMIN HASSANA D'AN LARABAWA*✍✍✍
*page 101 to 105*
*INA KUKE Y'AN AMANA ,MUTANE MASU DARAJA ,MUYI HAK'URI MUK'ARA HAK'URI ,ALLAH YANA SANE DAMU,ALLAH ZAI SAKAMANA ZALUNCIN DA AKAYI MANA*😭
*ALHAMDULILLAH INA TAYAKU MURNAR SAMUN K'ARUWA DA KUKAYI ,ALLAH YARAYA BABY'S ,ALLAH YABAKU LAFIYAR JIKI DA TA SHAYARWA*
*SA'ADATU TIJJANI D'AHEER*
*DA*
*SAFIYYA AHMAD SANI*
K'arfe takwas dai dai zaune nake agaban Abba na inata kuka saboda nasihar da yakemin akan inyi biyayya ga mijina ,mijina shine aljannata ,idan har banyi biyayya ba bashi bani ,sannan Abba na ya godemin abisa biyayyar da nayi masa da hak'uri da nayi akan zab'insa ,Abba na yace" ba kowace y'ace kamar niba ,yana alfahari dani ,nasiha iya nasiha a wannan dare Abba yayi min ,kukana yasa Abba zubarda hawaye shima ,na rungume Abba inata kuka me tsuma zuciya ,dama ba jin dad'in jikin nawa nakeba ,ciwon Mara ya warke sai zazzab'i ,Dan mama taso abarni zuwa gobe sai akaini ,amma Abba yace a a ,akaini zan k'arasa murmurewa a gidan mijina ,,,,,!
Na dad'e jikin Abba na ina kuka yanata rarrashina da k'arfafamin gwiwa ,har mama tashigo d'akin ,ina ganin tashigo nazame jikin Abba nakoma gunta na rungumeta kamar zankoma cikinta na kuma fashewa da kuka ,na karyawa mama zuciya itama ta kama kukan ,kunsan uwa !mama tausayina takeji Y'ar k'arama dani zan shiga cakwakiya ,ga rashin son miji ga zama da kishiya ,mun dad'e muna kuka nida mama har muryata ta dashe jikina zafi rau sai rawa yake, kan Abba sunkuye yana sauraren kukanmu ,sai daga can yazo inda muke ya b'anb'areni jikin mama ,Yakama hannuna d'aya da hannunsa ,sannan Yakama hannun mama da d'aya hannun ya kalli mama da hawaye ya b'ata fuskarta yayi mata murmushi yace "haba matata uwar y'ay'ana ,nasan amatsayinki na uwa kina tausayin d'iyarkine !amma baidace kisata gaba kina kuka ba zaki k'ara karyamata gwiwa ,kibita da addu'a kawai ,zata isketa har inda take ,sannan kimata nasiha akan zaman aure ,tabi mijinta ,ta girmama kishiyarta ,tayiwa mahaifiyarsa biyayya ,ta kyautatawa danginsa ,intayi haka zata dace ,Allah zai jib'anci al'amuranta ,zakuma tasamu rabo duniya da lahira ,mafi yawa mata y'an wuta ne ,bakuma wani dalili ke kaisu wuta ba face rashin biyayya ga miji ,da tozarta miji ,da gudun miji ,shi aure hak'uri ake dashi ,hak'urinsa yafi dad'insa yawa ,kuma muddin zakayi hak'uri to zakaji dad'in zaman kuma zakasamu riba,,,,,,!
Mama ta share hawayenta ,sannan tadubeni tayimun nasiha dai dai gwargwado tabani shawarwari akan yadda zanyi zaman aure ,ta k'arfafamin gwiwa ,sannan tace "inrik'e sirrin mijina ,duk abinda yadameni inyi hak'uri inyi addu'a ,idan kuma yayi tsanani abune na Neman shawara to in sanarda ita ,idan inajin kunya ga Y'ar uwata nan hameeda ingayamata zataji dani da lalurorina ,a k'arshe mama tayimin addu'a me tsawo da fatan alkairi ,da addu'ar Allah yasa inshiga da k'afar dama gidan mijina .
,,,,,Abba na ya kalleta ya matsa hannunta yace "ko kefa !yanzu kikayi abinda ya dace Maman su !ina alfaharin kasancewar ki matata ,,ya juyo ya dubeni inata hawaye yace dani " kibar kuka !yau Allah yabaki daraja me girma !kinzama babbar mace ,kinkusa ki fara tarbiyyar wasu kamar yadda mukayi miki ,ina jaddada miki !ki rik'e aurenki da kyau !kibi mijinki !kuma inason in tambayeki shin kin Isar da sak'on da nabaki ???.
"Na d'aga kaina ,cikin dasasshiyar murya nace "na Isar da sak'onka Abba na kuma ya amince da maganata ,na k'arasa da wani kukan .
"Abba yace " alhamdulillah ala kulli halin "nagode miki y'ata ,insha Allah cikin satinnan itama zata Sani ,mahaifiyarsa ma zata Sani ,Allah yasa abin yazomana da sauk'i ,alfarmar Shugaba S A W .
YOU ARE READING
SANADIN HOTO
Historical Fictionlabari ne da aka ginashi akan tsabtatacciyar soyayya ,wadda tafara tun daga yarinta ,dab da burin masoyan zai cika k'addara ta afka musu dalilin sanadin hoto ,kubiyoni Dan sanin shin k'addarar tana kaisu ga auren juna ko kuwa ........!?