[1/3, 7:24 AM] Obama: 💔💔💔❣❣❣💔💔💔❣❣❣
*SANADIN HOTO*
*TARE DA ALK'ALAMIN HASSANA D'AN LARABAWA*✍✍✍
*page 151 to 155*
*GAREKU FAN'S*
*masu ganin laifin safah akan tafara tunanin wayafi sonta tsakanin kamal da ya Abbas ,shin kun manta da cewa akwai bambamci tsakanin soyayyar waje da soyayyar aure ?shin kun manta da cewa zuciya tanason me kyautata mata ?shin bakusan ko mace batason mutum kyautatawar da yake mata da soyayyar da yake nuna mata da hak'urin da yake da ita yana jawo taji farat d'aya ta kamu da sonsa ba ?musamman zuciyar mace da ta kasance me rauni ?idan har kukace safah ta cigaba da ji a zuciyarta cewa ya Abbas yafi kamal sonta to kuna kai safah hanyar wuta ne !tabbas ya Abbas yaso safah fiye da tunanin me karatu , soyayya me girma wadda shak'uwar da sukayi tak'ara hab'akata ,sab'anin kamal da basuyi shak'uwa irin wadda tayi da ya Abbas ba ,amma inaso kusani ayanzu soyayya ya Abbas da safah tak'are ,tunda Allah baisa sun mallaki junaba ,bance dole masoyan ya Abbas suso kamal ba ,haka bance dole masoyan kamal suso ya Abbas ba ,abinda zance kawai yakamata mu fifita dokar Allah da bin tafarki madaidaici ,bawai mudinga bin soye soyen zuciyarmu ba ,har yanzu sanadin hoto bai k'areba ,fad'akarwarsa bata k'areba ,dad'insa bai k'areba ,soyayyar cikinsa bata k'areba ,ilimin cikinsa bai k'areba ,haka k'addarar sa bata k'areba ,da abubuwa da dama a gaba ,Dan haka kucigaba da bina a sannu cikin ikon Allah har mukai k'arshe ,nagode da k'aunarku gareni masoyana ,Allah yabamu lafiya da zama lafiya da mazajenmu wad'anda muka auresu don soyayya ko wad'anda muka auresu Dan biyayya ,ubangiji yabamu ladan zaman auren da mukeyi ,Allah ka shirya mana zur'ia ,ina yinku fan's d'ina iya wuya muna tare*👍👍🥰🥰😍😍😘😘🤝🤝💃💃
*NAGODE DA ADDU'ARKU GARENI ,HANNUNA YA WARKE ZAMU D'ORA*
,,,,,,,,,,, Ranar alhamis da misalin k'arfe sha biyu da rabi na rana su teema sukazo su uku ,nayita tsalle ina rungumesu saboda farinciki .
"Saida nagama karad'ina sannan na kula da su ikhram da saleem Ashe hardasu hafsat tabiya ta tawo dasu, aikuwa na k'ank'ame y'an uwana harda k'wallar farinciki ,suma sunata murnar ganina .
"Saina manta dasu teema naja k'annena inata tambayarsu Abba da mama "sukace suna gaidani ,Abba ma yace zasuzo shida mama" .
"Nashare hawayena saboda kewar gida da naji "nace " ikhram ina sameer ?ko nemana bayayi ko ?.
"Tace "wallahi saida mama tace yabiyomu mutawo tare ,yace zaizo wataran ,amma sai kin dena kuka, shi bayason yaga kina kuka shima kukan zaiyi ,"amma yacemin ince miki yana gaisheki gaisuwa d'ari ba d'aya ,ta cikon d'arin sai kun had'u "ta k'arasa da dariya .
"Na Shafa kan saleem da ke cinyata a zaune yayi lakwas a jikina ,nayi murmushi tare da zubowar wasu hawayen ,nayi maza na share kar ikram tagani nace " Allah sarki d'an uwana Rabin jikina sameer ,ina amsawa sosai kullum inata tunaninku ikram ,idan kun koma kice dashi inason in ganshi, kuma idan baizoba bazan daina kuka ba "
"Ikhram tace " to aunty zan gaya masa ,sannan ta zaro wani Abu acikin mayafinta ta mik'omin aleda tacemin "gashi inji ya sameer yace inbaki ".
" na karb'a da sauri na na bud'e ledar ,sainaga game me kyau Y'ar k'arama ,sai kuma Y'ar takarda k'arama yayi rubutun da bashida yawa ajiki ".
*Assalamu alaikum*
*Y'ar uwata ykk ,ina kewarki sosai ,ga game kidinga bugawa ko zaki dunga tunawa dani ,amma banda kukafa ,inanan zuwa gareki domin inganki ,agaida uncle kamal nagode*
YOU ARE READING
SANADIN HOTO
Historical Fictionlabari ne da aka ginashi akan tsabtatacciyar soyayya ,wadda tafara tun daga yarinta ,dab da burin masoyan zai cika k'addara ta afka musu dalilin sanadin hoto ,kubiyoni Dan sanin shin k'addarar tana kaisu ga auren juna ko kuwa ........!?