page 9&10

657 25 1
                                    

[11/13, 6:10 PM] Hassana D'an Larabawa🥰: 💔💔💔❣❣❣💔💔💔❣❣❣


*SANADIN HOTO*

*TAREDA ALKALAMIN HASSANA DANLARABAWA*✍✍✍

*page 10*

*rabin raina 🥰rabin jikina 😘kinsan kanki 😎in akace HASSANA 👈dole ace hussaina 👈dake nake 👉inajin dadin kwarin gwiwar dakike bani a kullum 😍Allah yabar zumuncin mu*

Har mutane suka dawo daga gun dinner bansaniba, inata baccina, aunty kuwa har inda nake tazo tadan duddubani tashafa kwantaccen gashin kaina, tayimin addu 'a.

Da asuba mun idar da sallah kenan, nakoma zan kwanta dan har yanzu banji dadin jikina sosaiba banda wani qarfin jiki, saiga Maman mu tashigo da waya a hannu tace min "ungo safah Abbas ya isheni da kira tun ina bacci yake kira, ina sallah ma yaqara kira, nasan dai keyake nema ungo yanxu nasan zaikuma kira".

Kan tarufe bakinta ma waya tafara ringing, na karba ina murmushi, itakuma tajuya tafita,

Kwanciya nayi gefen katifa najawo filo na matse a qirjina waini zanyi hira da masoyi 🤪😂,nadaga wayar nakara a kunnena cikin taushin murya nace ""

"assalamu alaikum warahmatullah ""

Daga can ya Abbas ya sauke wata nannauyar ajiyar zuciya yana sauke numfashi a hankali sannan yace ""

"my soul kintashi lfy "?ya jikinna mu "?

"jikin mu kuma ya Abbas "?jikina dai ko"?

"no jikinmu dai!!!!!, ai jikin ki nawane, kema jikina nakine ""koba hakaba,

Murmushi nai me sauti nace "hakane habibi na "

"yace yauwa my soul haka nake son ji ""

"kin san me kuwa "?.........

Ah ah saika fada ""

Duk fa maganar da mukeyi muna yine cikin salon so Yadda ko na kusa dani bazai iya jiba.

""jiya dake na kwana a raina wallahi da qyar nasamu nai bacci, acikin barcin kuma nayi wani kyakkyawan mafarki cikin yanayin da bazan iya fadamiki ba yanxu har sai munyi aure, domin maganar nada nauyin fade ""yafada cikn wata irin murya da bansan shi da itaba saboda tsananin qasa da tayi ga laushi da taushi har wata irin sheshsheqa yake yayin maganar.

"wooo!!! Gaba daya jikina yaiwani irin sanyi, hannuna ma da kyar nake iya dagawa saboda tsabar shiga shauqi, idona har wani ciccikowa suke, tsigar jikina na tashi qirjina na bugawa, shauqi, doki, fata, da marmarin inzama matar ya Abbas suka qume ni, tabbas nasan nazama matarsa zan more, zaikula dani sosai, zai tarairayeni zai shagwabani sannan zai sani cikin bargon soyayyar sa me dadin kwanciya, inama inama, inama a yanxu mata da miji muke nida ya Abbas.

Kafin indawo daga shauqin da ya afkani yakuma cillani wani, dan cemin yayi ""

Inataya Abbas murna safar sa ta girma ta isa aure ""

Nayi shiru ba mgn, sbd bansan inda maganar tasamo asaliba,

"kince bamu isa aure ba, nikuma nasan mun isa, banqara tabbatar da haka ba sai jiya da ciwo ya kamamin ke....... Yanxu Kin tabbatar kin isa kokuwa kinada ja har yanxu ""?.

Ya rasulallahi!!!!!!!!! Ya Abbas zaikasheni da kunya yau........ 

Dankuwa wata kunya ce tataso ta rufeni, narasa abin cewa, banda nishi da numfarfashi ba abinda nakeyi, nayi dif dani.

"yadai? Kema kin qagu ko? Ainafiki qaguwa wannan tym yayi, wayyo dadi ranar zakisan kin auri me sonki, ranar zakisan abinda baki saniba, ranar zakiji dadin da baki taba jiba, ranar zan kaiki duniyar da baki taba zuwaba, Allah yanuna mana wannan lokaci da wurwuri kice ameen my soul ""

SANADIN HOTOWhere stories live. Discover now