[1/3, 7:24 AM] Obama: 💔💔💔❣❣❣💔💔💔❣❣❣
*SANADIN HOTO*
*TARE DA ALK'ALAMIN HASSANA D'AN LARABAWA*✍✍✍
*page 111 to 115*
*DEDICATED TO ALL MY FAN'S*
*INAJIN DAD'IN YADDA KUKE SON LITTAFINNAN DA YABAMIN NAGODE INA SONKU ADUK INDA KUKE DA WAD'ANDA NASANI DA WAD'ANDA BANSANIBA*,,,,,,,,,,,,,,,Washe gari da safe kafin safah ta tashi kamal ne yaimata gyaran d'aki da falon ,duk da kasancewar komai tsaf yake amma saida yakuma gyarawa ,baitasheta da asuba ba tunda ba sallah zatayiba ,shidai ya tashi yaje masallaci yayi sallah ,duk da shed'an yaso makarar dashi amma haka ya daure ya tashi .
"Kafin ya fita saida yaje ya tashi jamila ,wadda taci baccinta ta more ,tasan cewa mijinta ba zai angwanceba shiyasa bata damu kanta da tunani ba ,yayita tashinta tana jinsa tayi banza dashi saida yayi mata cakulkuli abinda bataso ,aikuwa da sauri ta mik'e tana k'unk'uni waiya dameta tashige toilet ta barshi da kallon bayanta yana murmushi ,saida yaji zubar ruwa a toilet d'in sannan yafita ya nufi masallaci anata kiran Assalatu.....!!
"Ana idar da sallah yadawo gida ,gudun kar safah ta tashi bata ganshiba ,saida ya kuma lek'a d'akin jamila saiya tarar ta idar da sallah takoma gado harta koma bacci ,ya jamata k'ofar yafito ya nufi sashen safah .
Har lokacin baccinta takeyi rungume da filon da yasa mata ,fuskarta duk busasshen hawaye,ya zauna gefenta ya tsura mata idanu yana wani irin kallonta fuskarta tayi fayau duk ta rame dalilin tashin hankali ,yasa hannu yashafi fuskarta ,sannan ya kwanta gefenta fuskarsa na kallon tata ,numfashinsu ya gauraya ya lumshe idanu ,ya kai kusan Rabin awa a haka ,sannan ya mik'e yafara gyaran sashen ya kunna turaren wuta a bonner ,k'amshi yacika d'akin ,da kansa yashiga kitchen ya d'ora tea ya tafasa ya d'auko flask ya wanke ya juye ,sannan ya soya k'wai ya had'a duk ya kai dinning ya d'ebi madara da Milo da bota da suger duk ya kai da cups da spoon da kuma breed ,ya gyara kitchen d'in ,hatta wanke wanke da bai iyaba ranar saida ya gwada ,aikuwa suka wanku tas yamaida komai ko'ina yadda yake ......!!
"Ya koma toilet d'in d'akin ya wanke pant d'inta data cire jiya da dare ,sannan ya had'a ruwan wanka yayi wankansa me kyau ,yafito d'aure da towel sai k'amshin sabulun wanka yake ,bayan ya goge jikinsa ya shafa mayuka masu k'amshi da roll on da body spray yanayi yana kallonta tanata baccinta ,yaje ya bud'e wata kwaba da akayi daga gefe ta glass ce ,turaruka ne iri iri na mata da humra ,ya bud'e humrar ya tuttula ya shafa a jikinsa ,k'amshinta yasashi lumshe idanu ,irin wannan k'amshin yakeji a jikin safah tunda akafara hidimar bikin ,baitab'a jin k'amshi me sanyin dad'i irin wannan ba ,shiyasa ako yaushe yakeson rab'ar jikinta ,duk da ba burinsa kenan ba.
Yagama shiryawa ,ya d'auko wani yadi light blue me shara shara yasaka ,yasaka hula da ta dace da kayan ,ya d'aura agogonsa ,ya fito ras dashi , duk Wanda ya ganshi yaga ango kyakkyawa me nutsuwa da hankali da aji .......!!
"Toilet ya shiga ya had'awa safah ruwan wanka ,sannan yadawo d'akin ,rasa yadda zaiyi ya tasheta yayi saboda yasan tana farkawa kuka zata mishi ,shikuma bayaso ,wallahi da tasan yadda yakeji a zuciyarsa sanadin kukan nan da ta tausaya mishi ta dena.
"""Ya daure ya k'arasa gadon ,yasa hannu ya yaye bargon ,ya d'agota cak ya d'orata a cinyarsa yana cewa "baccin ya isa haka matata " kitashi kiyi wanka ki karya rana tayi ,kar bak'i su fara zuwa amarya na bacci yafad'a yana murmushi......!
Nafara bud'e ido a hankali ,idona yayi tangararan ,jina a jikin kamal saina dawo hayyacina gabad'aya ,nafara k'ok'arin yin abinda nasaba wato kuka ,yana fuskantar haka saiya marairaice fuska ya kwantar da kansa a kafad'ata ya k'ara rungumeni ,cikin tattausar murya yafara magana....!!
YOU ARE READING
SANADIN HOTO
Historical Fictionlabari ne da aka ginashi akan tsabtatacciyar soyayya ,wadda tafara tun daga yarinta ,dab da burin masoyan zai cika k'addara ta afka musu dalilin sanadin hoto ,kubiyoni Dan sanin shin k'addarar tana kaisu ga auren juna ko kuwa ........!?